{"id":9215,"date":"2026-04-08T20:48:32","date_gmt":"2026-04-08T20:48:32","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9215"},"modified":"2026-04-08T20:48:32","modified_gmt":"2026-04-08T20:48:32","slug":"nelfund-ya-raba-sama-da-naira-biliyan-3-ga-daliban-buk","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nelfund-ya-raba-sama-da-naira-biliyan-3-ga-daliban-buk\/","title":{"rendered":"NELFUND Ya Raba Sama da Naira Biliyan 3 ga Daliban BUK"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em> <\/strong><\/p>\n<p>Asusun Bada Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya raba jimillar Naira Biliyan 3 da Miliyan 39 a matsayin kudaden karatu ga daliban Jami\u2019ar Bayero da ke Kano su\u00a0 27,640,\u00a0 a wani\u00a0 mataki na fadada damar samun ilimi cikin sauki.<\/p>\n<p>Shugaban Jami\u2019ar, Haruna Musa ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da Darakta Janar na NELFUND, Akintunde Sawyerr, tare da tawagarsa suka kai jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Ziyarar, na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da kuma tattauna batutuwan da suka shafi kudaden da ke bai wa dalibai.<\/p>\n<p>A jawabinsa, Farfesa Haruna Musa ya yaba wa NELFUND kan irin tasirinsa ga dalibai, yana mai cewa shirin ya taimaka matuka wajen kara damar shiga makarantu ga dimbin \u2018yan Najeriya da ba za su iya yin rajista ba a baya.<\/p>\n<p>Ya ce a zangon karatu na shekarar 2023\/2024, daliba BUK 113 ne suka ci gajiyar shirin, inda aka biya Naira Biliyan 1 da Miliyan 494 a matsayin kudaden karatu.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa adadin ya karu sosai a zangon 2024\/2025 zuwa dalibai 14,539, wanda kudaden suka kai jimillar Naira Biliyan 1 da Miliyan 545.<\/p>\n<p>\u201c<em>Gaba daya, jimillar dalibai 27,640 daga Jami\u2019ar Bayero sun amfana da shirin NELFUND, inda kudaden makaranta suka kai Naira Biliyan 3 da Miliyan 39, baya ga kudaden amfanin yau da kullum da ake biya kai tsaye ga daliban<\/em>,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Sai dai Shugaban Jami\u2019ar ya bayyana cewa wasu dalibai sun fuskanci matsaloli yayin neman lamunin da kuma karbar kudade ta shafin NELFUND. Inda ya bayyana fatan tawagar za ta zage damtse wajen tabbatar da magance wadannan matsaloli.<\/p>\n<p>Tun da farko, Mista Sawyerr ya ce ziyarar na da nufin\u00a0 kara zurfafa hadin gwiwa ne da jami\u2019ar, yana mai tabbatar da cewa za a duba korafe-korafen dalibai domin saukaka tsarin neman lamunin da sake nema.<\/p>\n<p>Haka kuma ya shawarci jami\u2019ar da ta rika bude shafinta a kan lokaci domin bai wa dalibai damar yin rajista da wuri, tare da samun kudaden amfanin yau da kullum ba tare da jinkiri ba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu Asusun Bada Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya raba jimillar Naira Biliyan 3 da Miliyan 39 a matsayin kudaden karatu ga daliban Jami\u2019ar Bayero da ke Kano su\u00a0 27,640,\u00a0 a wani\u00a0 mataki na fadada damar samun ilimi cikin sauki. Shugaban Jami\u2019ar, Haruna Musa ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9216,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[736,39,2031],"class_list":["post-9215","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-buk","tag-kano","tag-nelfund"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/IMG-20260408-WA0022.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9215","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9215"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9215\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9217,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9215\/revisions\/9217"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9216"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9215"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9215"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9215"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}