{"id":9193,"date":"2026-04-06T11:48:14","date_gmt":"2026-04-06T11:48:14","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9193"},"modified":"2026-04-06T11:48:14","modified_gmt":"2026-04-06T11:48:14","slug":"yan-kasuwar-albasa-a-najeriya-sun-dakatar-da-fitar-da-kaya-zuwa-ghana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-kasuwar-albasa-a-najeriya-sun-dakatar-da-fitar-da-kaya-zuwa-ghana\/","title":{"rendered":"&#8216;Yan Kasuwar Albasa a Najeriya Sun Dakatar da Fitar da Kaya Zuwa Ghana"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Nasir Malali\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>\u2019Yan Kasuwar Albasa a Najeriya sun dakatar da fitar da albasa zuwa Jamhuriyar Ghana sakamakon wani sabani da aka samu.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da shugabannin kungiyoyin \u2019yan kasuwar albasa suka fitar a Sakkwato,\u00a0 wadda aka rabawa manema labarai, sun ce wannan mataki ya biyo bayan yawaitar hare-hare da ake kai wa \u2019yan kasuwarsu, musamman a kasuwar Kotoku, wacce take muhimmiyar cibiyar kasuwanci ce a babban birnin Ghana.<\/p>\n<p>A cewar \u2019yan kasuwar, lamarin ya kara kamari ne bayan wata takaddama tsakanin \u2019yan kasuwar Najeriya da na Ghana wadda ake zargin ta kai ga kwace manyan motoci dauke da albasa mallakar \u2019yan kasuwar Najeriya.<\/p>\n<p>Wannan lamari, wanda ke barazana ga wani muhimmin bangare na kasuwancin noma a yankin kasashen Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ECOWAS, ya janyo damuwa kan tsaron \u2019yan kasuwar Najeriya da kuma dorewar harkokin kasuwancin kan iyaka tsakanin kasashen biyu.<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba da kasancewa har sai an warware dukkan matsalolin da ke akwai tare da dawo da yanayi na kasuwanci mai aminci, adalci da bin doka.<\/p>\n<p>Ta kuma yi kira ga hukumomin da abin ya shafa a Najeriya da Ghana, tare da kungiyoyin yankin, da su gaggauta binciken abubuwan da aka ruwaito, ciki har da kwace motocin albasa na \u2019yan Najeriya, domin hana sake faruwar irin wannan rikici a nan gaba.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Nasir Malali\u00a0 \u2019Yan Kasuwar Albasa a Najeriya sun dakatar da fitar da albasa zuwa Jamhuriyar Ghana sakamakon wani sabani da aka samu. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da shugabannin kungiyoyin \u2019yan kasuwar albasa suka fitar a Sakkwato,\u00a0 wadda aka rabawa manema labarai, sun ce wannan mataki ya biyo bayan yawaitar hare-hare da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9194,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[2030,86,295,63],"class_list":["post-9193","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-albasa","tag-ghana","tag-sokoto","tag-yan-kasuwa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/01000000-c0a8-0242-7fe5-08dbc04f44b0_w408_r1_s.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9193","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9193"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9193\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9195,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9193\/revisions\/9195"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9194"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9193"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9193"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9193"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}