{"id":9190,"date":"2026-04-06T11:31:47","date_gmt":"2026-04-06T11:31:47","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9190"},"modified":"2026-04-06T11:31:47","modified_gmt":"2026-04-06T11:31:47","slug":"gwamnatin-zamfara-ta-jinjinawa-hukumomin-tsaro-bisa-wanzar-da-zaman-lafiya-a-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-zamfara-ta-jinjinawa-hukumomin-tsaro-bisa-wanzar-da-zaman-lafiya-a-jihar\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Zamfara ta Jinjinawa Hukumomin Tsaro Bisa Wanzar da Zaman Lafiya a Jihar"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left\"><strong><em>Daga Aminu Dalhatu<\/em><\/strong><\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana jin da\u0257inta tare da yaba wa hukumomin tsaro da ke aiki a jihar bisa nasarar da suka samu a ya\u0199i da rashin tsaro, musamman a wani sabon samame da ya kai ga hallaka kimanin \u2019yan bindiga 100.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, Mahmud Mohammed Dantawasa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce wannan nasara hujja ce karara ta\u00a0 \u0199wazo da \u0199warewar jami\u2019an tsaro, wa\u0257anda ke ci gaba da sadaukar da rayukansu domin kare al\u2019umma a sassan jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">A cewarsa, gwamnatin jihar na matu\u0199ar yaba wa sadaukarwarsu da jajircewarsu wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Mahmud Dantawasa ya \u0199ara da cewa wannan nasara babbar alama ce ta ci gaba a \u0199o\u0199arin da ake yi na rushe \u0199ungiyomasu&#8217;yan ta&#8217;adda, da kawar da barazanar \u2019yan bindiga da ta addabi yankuna da dama na jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Ya jaddada cewa gwamnatin jihar na \u0199arfafa gwiwar jami\u2019an tsaro da su ci gaba da zama jajirtattu, da ci gaba da aiki tu\u0199uru.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Gwamnatin ta kuma tabbatar musu da cikakken goyon baya da kuma ci gaba da ba su tallafin kayan aiki, tare da yin kira agare su da kada su yi \u0199asa a gwiwa har sai an tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">Haka kuma, gwamnatin jihar ta sake jaddada aniyarta ta \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa da Gwamnatin Tarayya da dukkan masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, tare da al\u0199awarin ci gaba da bayar da duk wani tallafi da ake bu\u0199ata domin nasarar ayyukan tsaro a yanzu da ma nan gaba.<\/p>\n<p style=\"text-align: left\">A \u0199arshe, kwamishinan ya yi kira ga al\u2019ummar Zamfara da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro ha\u0257in kai ta hanyar ba da bayanai a kan lokaci da kuma kula da tsaro a cikin al\u2019umma.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana jin da\u0257inta tare da yaba wa hukumomin tsaro da ke aiki a jihar bisa nasarar da suka samu a ya\u0199i da rashin tsaro, musamman a wani sabon samame da ya kai ga hallaka kimanin \u2019yan bindiga 100. Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, Mahmud Mohammed Dantawasa, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9191,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1968,115],"class_list":["post-9190","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hukumomin-tsaro","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/IMG-20260406-WA0005.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9190","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9190"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9190\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9192,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9190\/revisions\/9192"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9191"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9190"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9190"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9190"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}