{"id":9166,"date":"2026-04-02T09:51:58","date_gmt":"2026-04-02T09:51:58","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9166"},"modified":"2026-04-02T09:51:58","modified_gmt":"2026-04-02T09:51:58","slug":"kungiyar-nuj-reshen-rediyo-najeriya-kaduna-ta-taya-frcn-murnar-cika-shekaru-75-da-kafuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kungiyar-nuj-reshen-rediyo-najeriya-kaduna-ta-taya-frcn-murnar-cika-shekaru-75-da-kafuwa\/","title":{"rendered":"Kungiyar NUJ Reshen Rediyo Najeriya Kaduna ta Taya FRCN Murnar Cika Shekaru 75 da Kafuwa"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Kungiyar \u2018Yan Jaridu ta Kasa NUJ, reshen Rediyo Najeriya Kaduna ta taya mahukunta da ma\u2019aikatan Rediyon Tarayya(FRCN) murnar cika shekaru 75 da kafuwa.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Shugabanta, Umar Adamu Sarkinfada ya fitar, kungiyar ta bayyana wannan gagarumar nasara a matsayin shaida ta jajircewa, \u0199wazo da kuma muhimmiyar gudunmawar da FRCN ke bayarwa wajen ci gaban \u0199asa, ha\u0257in kan al\u2019umma da kuma yada sahihan labarai a Najeriya da ma duniya baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Shugaban ya ce, tsawon sama da shekaru saba\u2019in, Rediyon Tarayya na ci gaba da kasancewa amintacciyar murya wajen wayar da kai, ilmantarwa da kuma nishadantar da al\u2019umma, tare da kiyaye \u0199a\u2019idojin aikin jarida masu inganci.<\/p>\n<p>Ya yaba wa ma\u2019aikatan kafar yada labaran bisa jajircewarsu, aiki tu\u0199uru da sadaukarwa wajen inganta ha\u0257in kan \u0199asa da kuma bai wa al\u2019ummomi daban-daban damar a ji ra&#8217;ayoyinsu a fa\u0257in \u0199asar.<\/p>\n<p>Yayin da yake taya su murna kan wannan nasara, Sarkinfada ya bu\u0199aci mahukunta da su mayar da hankali kan jin da\u0257in ma\u2019aikata, yana mai jaddada cewa \u0199wararrun ma\u2019aikata masu \u0199wazo su ne ginshi\u0199in ci gaba a kowace ma\u2019aikata.<\/p>\n<p>Haka kuma, ya yi kira da a fa\u0257a\u0257a ayyukan gyaran da ake yi a hedikwatar gidan rediyon zuwa dukkan tashoshin yankuna, domin samar da ingantaccen muhalli na aiki.<\/p>\n<p>Umar Adamu Sarkinfada ya kuma \u0199arfafa gwiwar ci gaba da kawo sabbin hanyoyi da kuma bin \u0199a\u2019idoji da manufofin da suka gina Rediyon Tarayya tsawon shekaru.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kungiyar NUJ ta yi wa kafar fatan \u0199arin shekaru masu albarka, ci gaba da nasara a ayyukanta.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu\u00a0 Kungiyar \u2018Yan Jaridu ta Kasa NUJ, reshen Rediyo Najeriya Kaduna ta taya mahukunta da ma\u2019aikatan Rediyon Tarayya(FRCN) murnar cika shekaru 75 da kafuwa. A cikin wata sanarwa da Shugabanta, Umar Adamu Sarkinfada ya fitar, kungiyar ta bayyana wannan gagarumar nasara a matsayin shaida ta jajircewa, \u0199wazo da kuma muhimmiyar gudunmawar da FRCN [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9167,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[33,495,2026],"class_list":["post-9166","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kaduna","tag-nuj","tag-rediyon-tarayya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/04\/IMG-20260402-WA0004.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9166","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9166"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9166\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9168,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9166\/revisions\/9168"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9167"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9166"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9166"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9166"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}