{"id":9101,"date":"2026-03-30T08:39:11","date_gmt":"2026-03-30T08:39:11","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9101"},"modified":"2026-03-30T08:39:11","modified_gmt":"2026-03-30T08:39:11","slug":"%c9%97aya-daga-cikin-jariran-nan-biyar-ya-rasu-hu%c9%97u-na-ci-gaba-da-jinya-a-asibitin-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/%c9%97aya-daga-cikin-jariran-nan-biyar-ya-rasu-hu%c9%97u-na-ci-gaba-da-jinya-a-asibitin-kano\/","title":{"rendered":"\u018aaya Daga Cikin Jariran nan Biyar Ya Rasu, Hu\u0257u Na Ci Gaba Da Jinya a Asibitin Kano"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar \u0257aya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin Kwararru ta Murtala Muhammad dake Kano, yayin da sauran hu\u0257un ke ci gaba da samun kulawa ta musamman.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da jami\u2019ar hul\u0257a da jama\u2019a ta hukumar, Samira Suleiman ta fitar, ta ce an haifi jariran ne kafin cikar wa\u2019adin haihuwa, inda aka kwantar da su a sashen kula da jarirai masu bu\u0199atar kulawa ta musamman, domin jinyar matsalolin \u0199arancin nauyi da haihuwa da wuri \u00a0da sauran matsaloli masu ala\u0199a da hakan.<\/p>\n<p>Hukumar ta bayyana cewa nan take aka sanya dukkan jariran biyar a karkashin kulawa ta musamman, ciki har da amfani da na\u2019urar incubator, da kuma magungunan rigakafin cututtuka, wa\u0257anda daga bisani aka \u0199ara inganta su bisa ga yadda yanayin lafiyarsu ke bu\u0199ata.<\/p>\n<p>Da take bayani kan halin da suke ciki, hukumar ta ce jariri na farko, mace mai nauyin kilo 1.3, ta rasu duk da an yi mata \u0199arin jini, sakamakon matsalolin da suka shafi tsayawar numfashi (apnoea).<\/p>\n<p>A cewar hukumar, dukkan jariran sun fuskanci matsalar saukar sukarin jini (hypoglycaemia), amma an shawo kan lamarin cikin gaggawa bisa \u0199a\u2019idojin likitanci.<\/p>\n<p>Haka kuma, ta ce ana yi wa dukkan jariran hasken jinya (phototherapy) domin magance ciwon jaundice na jarirai, wanda galibi ke faruwa ga wa\u0257anda aka haifa da wuri.<\/p>\n<p>\u0198ar\u0199ashin jagorancin shugaban hukumar, Mansur Mudi Nagoda, HMB ta ce an \u0257auki dukkan matakan jinya da suka dace tun daga lokacin haihuwa har zuwa kulawar da ake ci gaba da yi musu.<\/p>\n<p>Duk da haka, hukumar ta jaddada cewa irin wa\u0257annan haihuwar jarirai da yawa a lokaci guda kafin lokaci na da matu\u0199ar ha\u0257ari a fannin likitanci, duk da \u0199o\u0199arin da ake yi na ba su kulawa mafi inganci.<\/p>\n<p>Hukumar ta kuma yaba da \u0199wazon da jajircewar ma\u2019aikatan lafiya na sashen haihuwa da na kula da jarirai, tana mai cewa matakan gaggawa da suka \u0257auka na taka muhimmiyar rawa wajen kula da jariran da suka rage.<\/p>\n<p>Khadijah Aliyu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar \u0257aya daga cikin jarirai biyar da aka haifa a Asibitin Kwararru ta Murtala Muhammad dake Kano, yayin da sauran hu\u0257un ke ci gaba da samun kulawa ta musamman. A cikin wata sanarwa da jami\u2019ar hul\u0257a da jama\u2019a ta hukumar, Samira Suleiman ta fitar, ta ce [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9102,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2020],"class_list":["post-9101","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-haihuwa-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/939cf3c1-5200-4b4f-950e-4ddc7aa25365.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9101","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9101"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9101\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9103,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9101\/revisions\/9103"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9102"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9101"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9101"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9101"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}