{"id":9095,"date":"2026-03-30T08:36:52","date_gmt":"2026-03-30T08:36:52","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9095"},"modified":"2026-03-30T08:36:52","modified_gmt":"2026-03-30T08:36:52","slug":"fmc-gusau-ta-kar%c9%93i-tallafin-littattafan-lafiya-daga-gidauniyar-sir-emeka-offor","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/fmc-gusau-ta-kar%c9%93i-tallafin-littattafan-lafiya-daga-gidauniyar-sir-emeka-offor\/","title":{"rendered":"FMC Gusau ta kar\u0253i tallafin littattafan lafiya daga gidauniyar Sir Emeka Offor"},"content":{"rendered":"<p>Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya kar\u0253i tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka Offor Foundation, a wani \u0253angare na shirin \u0199asa baki \u0257aya na \u0199arfafa horaswa da bincike a cibiyoyin lafiya na tarayya.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na cibiyar, Dakta Naziru A. Tukur ya fitar, ya ce tallafin na daga cikin wani babban shirin rabon littattafai da ya shafi cibiyoyin lafiya 58 da aka za\u0253a a fa\u0257in yankuna shida na \u0199asar.<\/p>\n<p>Dakta Tukur ya bayyana cewa an tanadi littattafan ne domin tallafa wa koyarwa, horas da \u0199wararru da kuma bincike a cibiyoyin da suka amfana.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa gidauniyar ta \u0257auki nauyin sayo da jigilar kwantena goma na littattafai da mujallu na zamani masu tsawon kafa 40 zuwa Najeriya domin aiwatar da shirin.<\/p>\n<p>Wannan rabon littattafai shi ne karo na 13 na shirin da aka fara tun a shekarar 2013. Ba kamar lokutan baya ba, na shekarar 2026 ya mayar da hankali ne kacokan kan fannin kiwon lafiya.<\/p>\n<p>A cikin wasi\u0199ar da aka aika wa Daraktan Lafiya na cibiyar, Dakta Bello A. Mohammed, gidauniyar ta ce wannan tallafi ya biyo bayan bu\u0199atar da Ministan Lafiya da Walwalar Jama\u2019a mai kula da harkokin daidaitawa, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya gabatar a madadin cibiyoyin lafiya na tarayya.<\/p>\n<p>Wasi\u0199ar wadda mukaddashin Babban Jami\u2019in Ma\u2019aikata na gidauniyar, Barista Chijioke James ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an amince da sayo da jigilar littattafan daga Amurka domin \u0199ara \u0199arfafa horaswa a cibiyoyin lafiya na \u0199asar.<\/p>\n<p>Ta kuma nuna cewa Cibiyar ta Gusau na daga cikin cibiyoyin da aka za\u0253a su ci gajiyar shirin.<\/p>\n<p>Da yake mayar da martani, Daraktan Lafiya na cibiyar, Dakta Bello A. Mohammed, ya gode wa gidauniyar da kuma ministan bisa wannan tallafi na kan lokaci.<\/p>\n<p>Ya ce gudunmawar za ta taimaka matu\u0199a wajen bun\u0199asa harkokin ilimi da \u0199warewa a cibiyar, musamman a daidai lokacin da ake \u0199o\u0199arin mayar da ita asibitin koyarwa.<\/p>\n<p>Dakta Mohammed ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni, \u2019yan kasuwa, \u2019yan siyasa, shugabannin addini da na gargajiya da sauran jama\u2019a da su yi koyi da wannan kyakkyawan aiki na taimako.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa ci gaba da tallafi daga masu ruwa da tsaki yana da muhimmanci wajen ha\u0253aka cibiyar da kuma inganta ayyukan kula da lafiya.<\/p>\n<p>\u201cBabu wanda ya kai talauci da ba zai iya bayarwa ba, kamar yadda babu wanda ya kai arziki da ba zai iya kar\u0253a ba,\u201d in ji shi, yana mai tabbatar da cewa za a yi amfani da littattafan yadda ya kamata domin inganta koyarwa da kuma ingancin ayyukan kiwon lafiya.<\/p>\n<p>A gefe guda kuma, cibiyar ta kafa wani kwamiti domin tantance littattafan da kuma gano bukatun sassa daban-daban, domin tabbatar da an raba su yadda ya dace.<\/p>\n<p>Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Shugaban Sashen Ayyukan Asibiti (Bincike da Horaswa), Dakta Usman Sulaiman, ya ce sun fara aikin tantance littattafan gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa za a rarraba littattafan bisa fannoni da muhimmanci, sannan a duba gibin da ke akwai a sassa da \u0257akunan karatu daban-daban.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa kwamitin na shirin kafa tsarin bibiyar amfani da littattafan da kula da su, domin tabbatar da an kiyaye su yadda ya kamata kuma ma\u2019aikata suna samun sau\u0199in amfani da su.<\/p>\n<p>Aminu Dalhatu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asibitin Kula da Lafiya na Tarayya da ke Gusau, ya kar\u0253i tarin littattafan kiwon lafiya da mujallu daga Sir Emeka Offor Foundation, a wani \u0253angare na shirin \u0199asa baki \u0257aya na \u0199arfafa horaswa da bincike a cibiyoyin lafiya na tarayya. A cikin wata sanarwa da jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na cibiyar, Dakta Naziru A. Tukur [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9096,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[669],"class_list":["post-9095","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-dalhatu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/1d59da99-252c-4973-a87b-ea5d3b914b5b.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9095","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9095"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9095\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9097,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9095\/revisions\/9097"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9096"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9095"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9095"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9095"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}