{"id":9092,"date":"2026-03-30T08:34:48","date_gmt":"2026-03-30T08:34:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9092"},"modified":"2026-03-30T08:34:48","modified_gmt":"2026-03-30T08:34:48","slug":"niphid-ta-gudanar-da-gangamin-wayar-da-kai-kan-tarin-fuka-a-zaria-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/niphid-ta-gudanar-da-gangamin-wayar-da-kai-kan-tarin-fuka-a-zaria-kaduna\/","title":{"rendered":"NIPHID ta gudanar da gangamin wayar da kai kan tarin fuka a Zaria, Kaduna"},"content":{"rendered":"<p>Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a masallatan Juma\u2019a da coci-coci, tare da gudanar da shirin jinya kyauta a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) ta Chikaji, a \u0199aramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna.<\/p>\n<p>Gangamin na daga cikin shirin wayar da kai domin \u0199ara fahimtar jama\u2019a kan hanyoyin kariya, gano cutar da wuri, da kuma maganinta, tare da \u0199arfafa shigar al\u2019umma cikin yaki da cutar.<\/p>\n<p>Da yake jawabi yayin aikin, Darakta-Janar na Cibiyar, Dakta Abdullahi Dalhatu Aminu, ya bayyana kwarin gwiwa cewa za a iya kawar da tarin fuka idan dukkan masu ruwa da tsaki suka tashi tsaye wajen yakar ta.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa kawar da cutar na bukatar ha\u0257in kai tsakanin gwamnati, al\u2019umma da kuma daidaikun mutane, yana mai cewa nasara za ta samu ne idan kowa ya taka rawarsa.<\/p>\n<p>Dakta Abdullahi ya bayyana cewa gwamnati na bayar da magungunan tarin fuka kyauta, tare da gwaje-gwaje da sauran hanyoyin gano cutar a sassa daban-daban na \u0199asar.<\/p>\n<p>Sai dai ya ce har yanzu wasu marasa lafiya na fuskantar \u0199alubale wajen samun cibiyoyin lafiya sakamakon matsalar sufuri da sauran bu\u0199atun yau da kullum.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa Najeriya ce ta hu\u0257u a duniya wajen yawan masu dauke da tarin fuka, kuma ta farko a nahiyar Afirka, lamarin da ya bayyana a matsayin babban \u0199alubale na lafiya da ke bukatar gaggawar magancewa.<\/p>\n<p>Ya kuma yi kira ga kafafen ya\u0257a labarai da su \u0199ara \u0199aimi wajen wayar da kai, tare da neman goyon bayan jama\u2019a da hukumomi ta hanyar tallafi da shawarwari domin kawo \u0199arshen cutar a Najeriya.<\/p>\n<p>Haka kuma, wata kwararriyar likita, Dakta Umma Aliyu, wacce ke kula da sashen kula da marasa lafiya, ta ce tarin fuka cuta ce mai warkewa kuma mai hana ya\u0257uwa idan aka bi matakan kariya da suka dace.<\/p>\n<p>Ta bayyana cewa kariya daga cutar na bukatar guje wa cunkoson jama\u2019a da kuma tabbatar da samun iska mai kyau a gidaje da wuraren taruwar jama\u2019a.<\/p>\n<p>Dakta Aliyu ta kuma shawarci mutane da su guji shan taba sigari da yawan shan giya, tana mai cewa wa\u0257annan halaye na \u0199ara ha\u0257arin kamuwa da tarin fuka.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin marasa lafiyar tarin fuka da suka halarci shirin sun nuna godiya ga National Institute of Public Health and Infectious Diseases bisa shirya wannan gangamin wayar da kai.<\/p>\n<p>Rahoton Radio Nigeria ya ce yayin gangamin, \u0199wararru sun shafe wani \u0253angare na rana a PHC Chikaji inda aka gudanar da gwaje-gwaje da shawarwari kyauta ga mutane da dama, ciki har da yara da manya.<\/p>\n<p><strong>Ibrahim Suleiman\/Zaria<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cibiyar kula da lafiya dake Saye Zaria, ta gudanar da gangamin wayar da kai kan cutar tarin fuka (TB) a masallatan Juma\u2019a da coci-coci, tare da gudanar da shirin jinya kyauta a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) ta Chikaji, a \u0199aramar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna. Gangamin na daga cikin shirin wayar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9093,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[562],"class_list":["post-9092","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zaria"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/7f39dd54-c025-40e8-81d9-6cf61ce9d7b7.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9092","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9092"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9092\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9094,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9092\/revisions\/9094"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9093"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9092"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9092"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9092"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}