{"id":9089,"date":"2026-03-30T08:33:15","date_gmt":"2026-03-30T08:33:15","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9089"},"modified":"2026-03-30T08:33:15","modified_gmt":"2026-03-30T08:33:15","slug":"kiristoci-a-kwara-sun-fito-kan-titi-domin-bikin-palm-sunday","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kiristoci-a-kwara-sun-fito-kan-titi-domin-bikin-palm-sunday\/","title":{"rendered":"Kiristoci a Kwara sun fito kan titi domin bikin Palm Sunday"},"content":{"rendered":"<p>Dubban mabiya addinin Kirista a jihar Kwara sun fito kan tituna domin bikin Palm Sunday, ranar tunawa da shigowar Yesu Almasihu cikin birnin Urushalima cikin nasara, kamar yadda littattafan addini suka bayyana.<\/p>\n<p>Bikin na kuma nuni da \u0199arshen azumin kwanaki 40 na Lenten Fast da kuma fara makon ibada na Easter (Holy Week).<\/p>\n<p>Mabiya addinai daga dariku daban-daban sun taru a Cocin Saint Barnabas Cathedral, Sabo-Oke, inda daga nan suka gudanar da jerin gwanon tafiya na sa\u2019o\u2019i da dama ta wasu muhimman titunan birnin Ilorin, ciki har da Murtala Way, Maraba, Amilegbe, Ipata, Opo-Malu, Emir\u2019s Road, Taiwo Isale, Unity da kuma yankin Ofishin Wasi\u0199a, kafin daga bisani su koma cocin inda aka kammala da addu\u2019ar rufewa (benediction).<\/p>\n<p>Da yake jawabi bayan kammala jerin gwanon, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Kwara, Right Reverend Sunday Adewole, ya bukaci Kiristoci da su ci gaba da kasancewa cikin tsayuwar imani da hidima ga Allah.<\/p>\n<p>Ya kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su \u0199ara \u0199o\u0199ari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama\u2019a, yana mai cewa tsaron jama\u2019a ya kamata ya kasance abu na farko a fifiko.<\/p>\n<p>Adewole ya kuma jaddada tasirin hauhawar farashin man fetur da \u0199arancin wutar lantarki a gidaje da kasuwanci, yana mai cewa akwai bukatar gaggawar magance wa\u0257annan matsaloli na tattalin arziki.<\/p>\n<p>A nasa \u0253angaren, Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda wakilinsa, Reverend Timothy Akangbe, ya halarta, ya bukaci jama\u2019a da su ci gaba da yin addu\u2019a domin ci gaban jihar da Najeriya baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada muhimmancin tawali\u2019u da soyayya a rayuwar yau da kullum.<\/p>\n<p>Tsohon Sakatare na CAN, Pa Olusola Ajolore, ya yi kira da a \u0257auki matakan gaggawa wajen magance matsalar tsaro, tare da shawartar gwamnatoci su yi amfani da ku\u0257a\u0257en tsaro yadda ya kamata domin kare rayuka da dukiya.<\/p>\n<p>Ya kuma bukaci samar da ayyukan yi da kuma sake duba kundin tsarin mulki domin dacewa da halin da ake ciki a yau.<\/p>\n<p>Haka kuma, Babban Annabi Segun Korode na Cocin Cherubim and Seraphim Movement Church, Hedikwatar Ilorin, ya tunatar da mabiya cewa su ri\u0199a gode wa Allah a kowane lokaci tare da koyi da tawali\u2019un Yesu Almasihu wanda ya zo da ceton \u0257an adam.<\/p>\n<p>Bikin Palm Sunday a Ilorin ya nuna ha\u0257in kai na ibada tare da \u0199ara jaddada kira ga al\u2019umma kan zaman lafiya, tsaro da ci gaban tattalin arziki.<\/p>\n<p>Ali Muhammad Rabiu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Dubban mabiya addinin Kirista a jihar Kwara sun fito kan tituna domin bikin Palm Sunday, ranar tunawa da shigowar Yesu Almasihu cikin birnin Urushalima cikin nasara, kamar yadda littattafan addini suka bayyana. Bikin na kuma nuni da \u0199arshen azumin kwanaki 40 na Lenten Fast da kuma fara makon ibada na Easter (Holy Week). Mabiya addinai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9090,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[175],"class_list":["post-9089","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kwara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/dff4a766-7a00-4609-b4aa-9905cca0dcf9.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9089","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9089"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9089\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9091,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9089\/revisions\/9091"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9090"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9089"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9089"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9089"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}