{"id":9077,"date":"2026-03-27T22:01:03","date_gmt":"2026-03-27T22:01:03","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9077"},"modified":"2026-03-27T22:01:03","modified_gmt":"2026-03-27T22:01:03","slug":"hajjin2026-jigawa-ta-kara-kaimi-wajen-horar-da-maniyyata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hajjin2026-jigawa-ta-kara-kaimi-wajen-horar-da-maniyyata\/","title":{"rendered":"Hajjin2026: Jigawa ta Kara Kaimi Wajen Horar Da Maniyyata"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa tace ta dawo da ci gaba da bitar maniyyatan aikin hajjin bana a dukkan kananan hukumomin jihar bayan kammala azumin watan Ramadan.<\/p>\n<p>Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala ganawa da manyan jami&#8217;an hukumar a Dutse babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Yana mai cewar, hukumar da dakatar da bitar ne saboda azumin watan ramadan.<\/p>\n<p>A don haka, a zancen da ake yi yanzu, an dawo da bitar maniyyatan gadan-gadan domin kara fadakar da su gami da ilmantar da su yadda za su gudanar da aikin hajji a kasa mai tsarki.<\/p>\n<p>Alhaji Ahmed Umar Labbo ya kuma bukaci maniyyata da su tashi tsaye wajen ganin sun samu ilimin aikin hajji domin samun damar yin aikin hajji karbabbe.<\/p>\n<p>Yayi nuni da cewar, hukumar ta kammala shirye-shiryen tantance lafiyar maniyyata, wanda hakan ya sanya hukumar aikin hajji ta kasa ta jinjina wa tsarin jihar Jigawan, kuma ta farko wajen yin hakan.<\/p>\n<p>Labbo, ya kara da cewar hukumar za ta yi zama na musamman da shugabannin shiyoyinta na jihar da kuma jami&#8217;anta na kananan hukumomi wato center officers domin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsarin fara jigilar maniyatan daga nan gida zuwa \u0199asa mai tsarki.<\/p>\n<p>Ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake ba su domin ganin jihar ta ci gaba da zama ta \u0257aya a gudanar da aikin hajji.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa tace ta dawo da ci gaba da bitar maniyyatan aikin hajjin bana a dukkan kananan hukumomin jihar bayan kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala ganawa da manyan jami&#8217;an hukumar a Dutse [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9078,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1906,380,59],"class_list":["post-9077","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-2026hajj","tag-bita","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260226-WA0045.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9077","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9077"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9077\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9079,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9077\/revisions\/9079"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9078"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9077"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9077"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9077"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}