{"id":9064,"date":"2026-03-25T14:16:25","date_gmt":"2026-03-25T14:16:25","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9064"},"modified":"2026-03-25T15:02:11","modified_gmt":"2026-03-25T15:02:11","slug":"trump-ya-aike-da-daftarin-shirin-zaman-lafiya-ga-iran","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/trump-ya-aike-da-daftarin-shirin-zaman-lafiya-ga-iran\/","title":{"rendered":"Trump Ya Aike da Daftarin Shirin Zaman Lafiya ga Iran"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya aike wa Iran wani\u00a0 daftarin shirin zaman lafiya, inda ya bayyana \u0199warin gwiwar kawo \u0199arshen ya\u0199in da aka shafe kusan wata guda ana gwabzawa, a yayin da Iran ta sanar da cewa za ta bai wa jiragen wa\u0257anda ba sa gaba da ita damar wucewa ta mashigar ruwan Hormuz.<\/p>\n<p>Wannan alama ta kawo \u0199arshen ya\u0199in da ake gwabzawa ta hanyar diflomasiyya na zuwa ne duk kuwa da sabbin hare-hare da \u0253angarorin da ke kai ruwa rana ke kwarara wa juna, lamarin da ke cigaba da haddasa ta\u2019adi ga dukkaninsu.<\/p>\n<p>Trump, wanda kalamansa a cikin \u01b4an kwanakin nan suka tashi daga shan alwashin munanan hare-hare akan Iran, zuwa ayyana cewa ya\u0199in na daf da kawo \u0199arshe, ya ce Amurka na cikin tattaunawa a halin da ake ciki, sai dai Iran ba ta tabbatar da hakan ba.<\/p>\n<p>Shugaban Amurkan ya shaida wa manema labarai a Washington cewa Iran ta \u0257auki wani mataki da ya burge su, lamarin da ke nuni da cewa su na tattaunawa da wa\u0257anda suka kamata, sai dai bai yi wani \u0199arin bayani akan wannan furuci ba.<\/p>\n<p>Jim ka\u0257an bayan kalaman Trump ne Iran ta cikin wani sa\u0199o da hukumar kula da sufurin ruwa na \u0199asa da \u0199asa ta ya\u0257a, ta ce ta bai wa jiragen \u0199asashen da ba sa rigima da su damar wucewa mashigar ruwan Hormuz lafiya.<\/p>\n<p>Tun da farko a cikin &#8216;\u01b4an kwanakin da suka wuce, Iran ta ce ba ta rikici da \u0199asashen da ke kyautata mata, sai dai duk da haka jiragen ruwa da dama sun dakatar da bin hanyar, duba da yadda kamfanonin inshora suka kauce wa \u0257aukar kasada.<\/p>\n<p><em>rfi<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya aike wa Iran wani\u00a0 daftarin shirin zaman lafiya, inda ya bayyana \u0199warin gwiwar kawo \u0199arshen ya\u0199in da aka shafe kusan wata guda ana gwabzawa, a yayin da Iran ta sanar da cewa za ta bai wa jiragen wa\u0257anda ba sa gaba da ita damar wucewa ta mashigar ruwan Hormuz. Wannan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":7403,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[454,75],"class_list":["post-9064","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-iran","tag-trump"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/11\/FB_IMG_1763297822674.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9064","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9064"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9064\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9065,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9064\/revisions\/9065"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/7403"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9064"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9064"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9064"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}