{"id":9058,"date":"2026-03-25T13:18:34","date_gmt":"2026-03-25T13:18:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9058"},"modified":"2026-03-25T13:20:12","modified_gmt":"2026-03-25T13:20:12","slug":"hukumar-lafiya-a-kano-ta-shirya-taron-masu-ruwa-da-tsaki-kan-cutar-shan-inna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-lafiya-a-kano-ta-shirya-taron-masu-ruwa-da-tsaki-kan-cutar-shan-inna\/","title":{"rendered":"Hukumar Lafiya a Kano ta Shirya Taron Masu Ruwa da Tsaki Kan Cutar Shan Inna"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta gudanar da wani muhimmin taron game da shirye-shiryen tunkarar gamgamin wayar da kai kan allurar rigakafin cutar shan inna na watan Maris, a wani bangare na kokarin ci gaba da tabbatar da jihar ba ta da cutar tare da karfafa harkokin rigakafi na yau da kullum.<\/p>\n<p>Taron, wanda aka gudanar a Cibiyar Ayyukan Gaggawa (EOC), ya hada manyan masu ruwa da tsaki, abokan hulda, da jami\u2019an lafiya domin daidaita tsare-tsare da kuma karfafa hadin kai gabanin gudanar da shirin.<\/p>\n<p>Yayin da yake jagorantar taron, Darakta Janar na KSPHCMB, Farfesa Salisu Ibrahim, ya jaddada muhimmancin hadin kai, da kuma sa hannun al\u2019umma wajen tabbatar da nasarar shirin.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa samun kyakkyawan sakamako na bukatar cikakken hadin gwiwa tsakanin dukkan bangarorin da ke da hannu a ayyukan rigakafi a fadin jihar.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9060\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260325-WA0028-300x226.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"226\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260325-WA0028-300x226.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260325-WA0028-768x578.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260325-WA0028.jpg 1020w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Farfesa Ibrahim ya kuma jaddada bukatar fayyace ayyuka da nauyin da ya rataya a wuyan kowane bangare, ciki har da masu unguwanni, ma\u2019aikatan lafiya, da sauran abokan hulda.<\/p>\n<p>Ya ce hakan zai kara inganta gudanar da ayyuka tare da tabbatar da an kai ga jama\u2019a da dama.<\/p>\n<p>An kuma mai da hankali musamman kan rawar da Jami\u2019an Rigakafi na Kananan Hukumomi (LIOs), Wakilan Unguwanni, Masu Ba da Shawara na Rukunoni, da Masu Sa-kai za su taka, musamman a fannonin wayar da kai, yin allurar rigakafi, da sa ido a matakin kasa.<\/p>\n<p>Hukumar ta sake jaddada kudirinta na gudanar da ingantaccen shirin rigakafi mai tasiri ta hanyar karfafa hadin gwiwa da ci gaba da hada kan al\u2019umma.<\/p>\n<p>An kuma bukaci masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen wayar da kai, tare da yin aiki tare domin tabbatar da cewa kowane yaro da ya cancanta ya samu allurar rigakafi.<\/p>\n<p>Shirin watan Maris na daga cikin ci gaba da kokarin kawar da cutar shan inna da kuma inganta sakamakon rigakafi na yau da kullum a Jihar Kano.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta gudanar da wani muhimmin taron game da shirye-shiryen tunkarar gamgamin wayar da kai kan allurar rigakafin cutar shan inna na watan Maris, a wani bangare na kokarin ci gaba da tabbatar da jihar ba ta da cutar tare da karfafa harkokin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9059,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[2015,39],"class_list":["post-9058","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-cutar-shan-inna","tag-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260325-WA0029.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9058"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9061,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9058\/revisions\/9061"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9059"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9058"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9058"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9058"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}