{"id":9022,"date":"2026-03-22T15:56:14","date_gmt":"2026-03-22T15:56:14","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9022"},"modified":"2026-03-22T15:56:14","modified_gmt":"2026-03-22T15:56:14","slug":"yan-sandan-bauchi-sun-kama-wani-kan-satar-yaro-da-kisan-kai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-sandan-bauchi-sun-kama-wani-kan-satar-yaro-da-kisan-kai\/","title":{"rendered":"Yan Sandan Bauchi Sun Kama Wani Kan Satar Yaro Da Kisan Kai"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da aikata garkuwa da yaro da kuma kisan kai, a wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a cikin birnin Bauchi. Lamarin ya fito fili ne bayan da wani mazaunin unguwar Nasarawa Madina, Salisu Yunusa, ya kai rahoto ga \u2018yan sanda cewa dansa mai shekaru hudu, Yunusa Salisu, ya bace tun ranar 18 ga watan Maris da safe.<\/p>\n<p>Mai magana da yawon rundunar SP Nafiu Habibu ya bayyana cewar mahaifin yaron, bayan bacewar dansa sai ya samu kira daga wata lambar waya da ba a sani ba a ranar 19 ga watan Maris, inda aka bukaci ya biya kudin fansa na naira dubu dari biyar domin a sako yaron. Duk da cewa ya biya naira dubu dari guda domin ceto dansa, amma bai sake ganin yaron ba, lamarin da ya kara tayar masa da hankali tare da sanya shi garzayawa ga jami\u2019an tsaro.<\/p>\n<p>Bayan samun rahoton, jami\u2019an bincike na ofishin \u2018yan sanda na \u2018C\u2019 Division karkashin jagorancin DPO suka fara gudanar da bincike cikin gaggawa, wanda ya kai ga cafke wani matashi mai suna Rabiu Safiyanu mai shekaru 20, wanda yake zaune a unguwar daya da iyalan yaron. Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin yana da kusanci da iyalan yaron, kasancewarsa abokin kanin mahaifin yaron kuma yana da damar shiga gidan ba tare da wata shakka ba.<\/p>\n<p>A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifin cewa shi ne ya dauki yaron, inda daga bisani ya shake shi har ya mutu, sannan ya kai gawarsa wani wuri da ake kira Warinje Hills ya jefar. Har ila yau, ya amsa cewa shi ne ya kira mahaifin yaron domin neman karin kudin fansa duk da cewa ya riga ya kashe yaron.<\/p>\n<p>Jami\u2019an \u2018yan sanda sun samu nasarar gano gawar yaron a wurin da aka jefar da ita, inda aka tarar da alamun shakewa a jikinsa, tare da igiya da ake zargin an yi amfani da ita wajen aikata laifin. Likitan \u2018yan sanda ya tabbatar da mutuwar yaron, sannan aka dauki hotunan gawar kafin a mika ta ga iyalansa domin yi masa jana\u2019iza a wurin bisa dalilan lafiyar jama\u2019a.<\/p>\n<p>Kwamishinan \u2018yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin mika shari\u2019ar ga sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) domin zurfafa bincike tare da tabbatar da an gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu cikin gaggawa. Haka kuma ya yi kira ga al\u2019ummar jihar da su kasance masu lura da mutanen da ke kewaye da su tare da kai rahoton duk wani abu da ya zama abin zargi ga jami\u2019an tsaro.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cafke wani matashi da ake zargi da aikata garkuwa da yaro da kuma kisan kai, a wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a cikin birnin Bauchi. Lamarin ya fito fili ne bayan da wani mazaunin unguwar Nasarawa Madina, Salisu Yunusa, ya kai rahoto ga [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":9023,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2011],"class_list":["post-9022","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-bauci"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0082.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9022","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9022"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9022\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9024,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9022\/revisions\/9024"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9023"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9022"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9022"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9022"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}