{"id":9015,"date":"2026-03-22T06:28:49","date_gmt":"2026-03-22T06:28:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=9015"},"modified":"2026-03-22T06:28:49","modified_gmt":"2026-03-22T06:28:49","slug":"eid-el-fitr-sarkin-kauru-ya-jaddada-muhimmancin-hadin-kai-da-zaman-lafiya-a-tsakanin-alumma","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/eid-el-fitr-sarkin-kauru-ya-jaddada-muhimmancin-hadin-kai-da-zaman-lafiya-a-tsakanin-alumma\/","title":{"rendered":"Eid El-Fitr: Sarkin Kauru Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai da Zaman Lafiya a Tsakanin Al\u2019umma"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Yusuf Zubairu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Sarkin Kauru, Zakari Ya\u2019u Usman na biyu, ya yi kira ga al\u2019ummar masarautar da ke Jihar Kaduna, da su ci gaba da tabbatar da ha\u0257in kai, da zaman lafiya yayin gudanar da bukukuwan Sallah .<\/p>\n<p>Sarkin ya yi wannan kira ne a sakon sa na Sallah da ya gabatar a ranar Juma\u2019a, 20 ga watan Maris na shekarar 2026, bayan kammala\u00a0 azumin watan Ramadan.<\/p>\n<p>Ya gode wa Allah bisa bai wa Musulmi damar ganin wannan lokaci cikin \u0199oshin lafiya da walwala.<\/p>\n<p>Dangane da tsaro, Sarkin ya tabbatar da cewa an samu ci gaba a yankin, amma ya yi gargadin har yanzu akwai barazanar satar mutane da sauran laifuka makamantansu.<\/p>\n<p>Ya bukaci al\u2019umma da su kasance masu lura don kare yankunansu, tare da kai rahoton duk wani motsin bako a yankin.<\/p>\n<div id=\"attachment_9019\" style=\"width: 144px\" class=\"wp-caption alignnone\"><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" aria-describedby=\"caption-attachment-9019\" class=\"wp-image-9019 size-medium\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0002-134x300.jpg\" alt=\"\" width=\"134\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0002-134x300.jpg 134w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0002-457x1024.jpg 457w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0002.jpg 482w\" sizes=\"auto, (max-width: 134px) 100vw, 134px\" \/><p id=\"caption-attachment-9019\" class=\"wp-caption-text\"><em>Muhammad Sani Suleiman (Danburan) <\/em><\/p><\/div>\n<p>Zakari Ya\u2019u II ya jaddada muhimmancin ha\u0257in kai tsakanin dukkan al\u2019umma, ba tare da la\u2019akari da addini ko kabilanci ba, yana mai cewa ha\u0257in kai ne ke tabbatar da zaman lafiya da tsaro a masarautar.<\/p>\n<p>Sarkin yakuma bayyana zaman lafiya a matsayin ginshi\u0199in ci gaba, inda ya yi gargadi kan yada jita-jita da ka iya haifar da tashe tashen hankula.<\/p>\n<p>Ya kuma bukaci al\u2019summar masarautar da su ci gaba da zama tare cikin mutunta juna da fahimtar juna.<\/p>\n<p>Har ila yau, Sarkin ya\u00a0 jaddada muhimmancin kula da lafiyar jama\u2019a, inda ya bukaci su kula da tsafta, tsaftace muhalli, da kuma neman kulawar lafiya cikin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.<\/p>\n<p>Haka zalika ya yi nuni da muhimmancin rigakafin cututtuka, ciki har da allurar rigakafi na yau da kullum, musamman ga yara da mata masu juna biyu, bisa shirye-shiryen lafiyar jama\u2019a da ake gudanarwa.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-9018\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0001-300x146.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"146\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0001-300x146.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0001.jpg 482w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>A bangaren ilimi, Sarkin Kauru ya bukaci a kara himma a fannin ilimin zamani da na addini, yana mai kira ga iyaye da matasa su fifita neman ilimi a matsayin ginshi\u0199in ci gaban\u00a0 al\u2019umma.<\/p>\n<p>Ya kuma ba da shawarar dogaro da kai, musamman ga matasa, inda ya bukace su da su koyi sana\u2019o\u2019i maimakon jiran aikin gwamnati kawai, yana mai cewa yakamata arika amfani da shirye-shiryen gwamnati kamar na \u0199ungiyoyin manoma yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Sarkin ya yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, bisa kokarinsa na kawo ci gaba a yankin, ciki har da gina hanyoyi, shirin inganta wutar lantarki, da matakan \u0199arfafa tsaro. Haka kuma ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Honarabul Bashir Tanko Dawaki, bisa jajircewarsa wajen ci gaban karkara.<\/p>\n<p>Ya bukaci gwamnati ta kara himma wajen ciki gina muhimman hanyoyi da za su ha\u0257a Kauru da sauran yankuna makwabta, da \u0199arin tallafin noma ga manoma, da kuma kafa makarantar sakandare a garin Kauru.<\/p>\n<p>Zakari Ya\u2019u II ya kuma yi kira da a ci gaba da aikin gyaran Fadar Masarautar Kauru, musamman mataki na biyu.<\/p>\n<p>A \u0199arshe, Sarkin ya yi addu\u2019ar samun zaman lafiya yayin bukukuwan Sallah, da ci gaba da lafiya, tare da ro\u0199on Allah ya kar\u0253i ibadun da aka yi a watan Ramadan.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Yusuf Zubairu\u00a0 Sarkin Kauru, Zakari Ya\u2019u Usman na biyu, ya yi kira ga al\u2019ummar masarautar da ke Jihar Kaduna, da su ci gaba da tabbatar da ha\u0257in kai, da zaman lafiya yayin gudanar da bukukuwan Sallah . Sarkin ya yi wannan kira ne a sakon sa na Sallah da ya gabatar a ranar Juma\u2019a, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":9020,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[33,1424,260],"class_list":["post-9015","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kaduna","tag-kauru","tag-sallah"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260322-WA0000.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9015","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=9015"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9015\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":9021,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/9015\/revisions\/9021"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/9020"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=9015"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=9015"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=9015"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}