{"id":8958,"date":"2026-03-16T11:54:48","date_gmt":"2026-03-16T11:54:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8958"},"modified":"2026-03-16T11:54:48","modified_gmt":"2026-03-16T11:54:48","slug":"gwamnatin-zamfara-ta-amince-da-biyan-albashin-watan-maris-gabanin-bukukuwan-karamar-sallah","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-zamfara-ta-amince-da-biyan-albashin-watan-maris-gabanin-bukukuwan-karamar-sallah\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Zamfara Ta Amince da Biyan Albashin Watan Maris Gabanin Bukukuwan Karamar Sallah"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu<\/em> <\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma\u2019aikatan gwamnati da masu kar\u0253ar fansho a fa\u0257in jihar, gabanin bikin Sallar Eid-el-Fitr.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al\u2019adu, Mahmud Muhammad Dantawasa ya fitar, ya ce an \u0257auki wannan mataki ne domin saukaka wa ma\u2019aikata da wadanda suka yi ritaya, tare da ba su damar yin shirye-shiryen Sallah yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Dantawasa ya bayyana cewa, bisa ga bayanin da aka samu daga Ofishin Akanta Janar na Jihar, an kammala dukkan shirye-shirye da suka dace domin tabbatar da an biya albashi da fansho cikin gaggawa ga dukkan wa\u0257anda suka cancanta a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada \u0199udirin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na ci gaba da kula da jin da\u0257in ma\u2019aikatan gwamnati da &#8216;yan fansho, tare da yaba musu bisa sadaukarwa da gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>Mahmud Dantawasa ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da ba da fifiko ga manufofin da za su inganta rayuwar ma\u2019aikata da wadanda suka yi ritaya.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bu\u0199aci ma\u2019aikatan gwamnati da &#8216;yan fansho da su ci gaba da mara wa manufofin gwamnati baya, tare da yin addu\u2019ar zaman lafiya, ha\u0257in kai da ci gaba mai \u0257orewa a Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta kuma yi wa dukkan ma\u2019aikatan gwamnati, da wadanda suka yi ritaya, da kuma al\u2019ummar jihar fatan yin Sallar Eid-el-Fitr cikin kwanciyar hankali da farin ciki.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da biyan albashin watan Maris da wuri ga dukkan ma\u2019aikatan gwamnati da masu kar\u0253ar fansho a fa\u0257in jihar, gabanin bikin Sallar Eid-el-Fitr. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Al\u2019adu, Mahmud Muhammad Dantawasa ya fitar, ya ce an \u0257auki wannan mataki ne domin saukaka wa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8959,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[448,2002,115],"class_list":["post-8958","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-albashi","tag-karamar-sallah","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/Untitled-1-1177.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8958","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8958"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8958\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8960,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8958\/revisions\/8960"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8959"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8958"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8958"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8958"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}