{"id":8948,"date":"2026-03-16T08:51:28","date_gmt":"2026-03-16T08:51:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8948"},"modified":"2026-03-16T08:51:28","modified_gmt":"2026-03-16T08:51:28","slug":"yan-sanda-sun-bankado-maboyar-masu-garkuwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-sanda-sun-bankado-maboyar-masu-garkuwa\/","title":{"rendered":"\u2018Yan Sanda Sun Bankado Maboyar Masu Garkuwa"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da jami\u2019in hulda da jama\u2019a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, ya ce jami\u2019an Sashen Leken Asiri na Jihar (SID) sun samu sahihan bayanai da suka kai su ga bankado maboyar wani fitaccen mai garkuwa da mutane a Gidan Akuya da ke karamar hukumar Keana ta jihar.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce da zarar masu laifin suka hango jami\u2019an tsaro, sai suka yi kokarin tserewa daga wurin, amma \u2018yan sanda suka bi su da sawu inda a yayin samamen aka samu nasarar kama wani da ake zargi mai suna Jibril Yunusa.<\/p>\n<p>Binciken da aka gudanar a maboyar ya kai ga kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, mujallar harsashi daya mara komai, da kuma bindiga kirar gida guda daya.<\/p>\n<p>A cewar sanarwar, yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya shiga cikin hare-haren garkuwa da mutane da dama a yankunan Keana da Awe na jihar, tare da bayar da wasu muhimman bayanai da za su taimaka wajen ci gaba da bincike.<\/p>\n<p>Kwamishinan \u2018yan sandan jihar, CP Shetima Jauro Mohammed, ya umarci jami\u2019an rundunar da su kara zage damtse domin kamo sauran \u2018yan kungiyar da suka tsere.<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar wa mazauna jihar kudurin rundunar na ci gaba da yaki da laifuka tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al\u2019umma a ko\u2019ina cikin jihar.<\/p>\n<p>Aliyu Muraki\/Lafia<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018yan sandan jihar Nasarawa ta ce ta samu wani gagarumin nasara a kokarinta na yaki da masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a jihar. A wata sanarwa da jami\u2019in hulda da jama\u2019a na rundunar, SP Ramhan Nansel, ya fitar, ya ce jami\u2019an Sashen Leken Asiri na Jihar (SID) sun samu sahihan bayanai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8949,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[181],"class_list":["post-8948","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-police"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/c60c2d21-de5c-4414-b5c4-e7e742c9e103.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8948","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8948"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8948\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8950,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8948\/revisions\/8950"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8949"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8948"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8948"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8948"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}