{"id":8939,"date":"2026-03-13T09:11:53","date_gmt":"2026-03-13T09:11:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8939"},"modified":"2026-03-13T09:11:53","modified_gmt":"2026-03-13T09:11:53","slug":"kwastam-ta-kama-kayayyakin-fasa-kwauri-na-naira-miliyan-478-a-kwara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kwastam-ta-kama-kayayyakin-fasa-kwauri-na-naira-miliyan-478-a-kwara\/","title":{"rendered":"Kwastam Ta Kama Kayayyakin Fasa Kwauri Na Naira Miliyan 478 A Kwara"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Jihar Kwara, ta ce ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta da kuma wasu da aka takaita shigowarsu cikin \u0199asa da darajarsu ta haura naira miliyan 478 a bana.<\/p>\n<p>Mukaddashin Kwanturola na Kwastam a jihar, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a Ilorin.<\/p>\n<p>Ya ce rundunar ta kuma samu kudaden shiga da suka haura naira biliyan 2.5 a cikin wannan lokaci da ake nazari, lamarin da ya \u0199ara tabbatar da rawar da take takawa wajen tallafa wa manufofin gwamnati na tattalin arziki.<\/p>\n<p>A cewarsa, rundunar na da \u0199udurin kare tattalin arzikin \u0199asa tare da tabbatar da bin doka da oda.<\/p>\n<p>Ogundeyi ya ce rundunar ba za ta bari jihar ta zama mafakar masu safarar kaya ba bisa \u0199a\u2019ida ba, yana mai \u0199ara da cewa duk wanda ya yi \u0199o\u0199arin tauye tattalin arzikin \u0199asa ta hanyar fasa kwauri zai fuskanci matakin doka.<\/p>\n<p>Mukaddashin Kwanturolan ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da safarar kaya ba bisa \u0199a\u2019ida ba duk da garga\u0257in da ake yi, musamman shigo da shinkafar waje, wadda ke barazana ga manoman cikin gida.<\/p>\n<p>Ogundeyi ya ce haramcin shigo da irin wannan shinkafa daga \u0199asashen waje wani mataki ne na \u0199arfafa masu noma a gida, samar da ayyukan yi da kuma bun\u0199asa samarda abinci.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa nasarar wa\u0257annan ayyuka ta samu ne sakamakon bayanan sirri da kuma ha\u0257in gwiwa da sauran hukumomin tsaro.<\/p>\n<p>Mukaddashin Kwanturolan ya kuma yi kira ga mazauna yankunan kan iyaka, \u2019yan kasuwa da sauran jama\u2019a da su ha\u0257a kai da hukumar domin kare masana\u2019antun cikin gida, bun\u0199asa tattalin arzikin \u0199asa da kuma samar da ci gaba mai \u0257orewa.<\/p>\n<p>Daga cikin kayayyakin da rundunar ta kama akwai motoci biyar da aka yi amfani da su, buhunan shinkafar waje guda 1,107, buhunan sukari da aka shigo da su 44, jarkoki 317 na man fetur (PMS), buhuna 120 na ma\u2019adinin lithium da aka ha\u0199o ba bisa \u0199a\u2019ida ba, da kuma \u0257aruruwan tufafin gwanjo da sassan gyaran motoci.<\/p>\n<p>ALI MUHAMMAD RABIU<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Kwastam ta Najeriya, reshen Jihar Kwara, ta ce ta kama tare da kwace kayayyakin da aka haramta da kuma wasu da aka takaita shigowarsu cikin \u0199asa da darajarsu ta haura naira miliyan 478 a bana. Mukaddashin Kwanturola na Kwastam a jihar, Mataimakin Kwanturola Najeem Ogundeyi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8940,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[531],"class_list":["post-8939","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kamu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/2499709f-9cdd-446e-a7a6-00ff17751ae1.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8939","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8939"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8939\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8941,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8939\/revisions\/8941"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8940"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8939"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8939"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8939"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}