{"id":8936,"date":"2026-03-13T09:09:54","date_gmt":"2026-03-13T09:09:54","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8936"},"modified":"2026-03-13T09:09:54","modified_gmt":"2026-03-13T09:09:54","slug":"mataimakin-gwamnan-zamfara-ya-yi-rijista-a-jamiyyar-apc","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/mataimakin-gwamnan-zamfara-ya-yi-rijista-a-jamiyyar-apc\/","title":{"rendered":"Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Yi Rijista a Jam\u2019iyyar APC"},"content":{"rendered":"<p>Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Malam Mummuni, ya yi rijista a hukumance a matsayin cikakken \u0257an jam\u2019iyyar APC.<\/p>\n<p>An gudanar da rajistar ne a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, jim ka\u0257an bayan kaddamar da wani taron horaswa na kwanaki biyu kan rijistar \u2019yan jam\u2019iyya a dukkanin \u0199ananan hukumomi 14 da kuma gundumomi na jihar.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan ya ce muhimmancin wannan horo ba zai misaltu ba.<\/p>\n<p>A cewarsa, an za\u0253i mahalarta taron ne da kulawa domin su zama masu horaswa da kuma masu jagorantar aikin rijistar \u2019yan jam\u2019iyya a \u0199ananan hukumominsu da gundumominsu.<\/p>\n<p>\u201cKamar yadda kowa ya sani, jam\u2019iyyarmu na ci gaba da kar\u0253ar sababbin mambobi da dama a fa\u0257in jihar. Don haka yana da matu\u0199ar muhimmanci tsarin rijistar \u2019yan jam\u2019iyya ya kasance mai tsari, gaskiya da kuma kulawa ta yadda ya dace,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Malam Mani ya yabawa Shugaban Jam\u2019iyyar APC na \u0199asa, Farfesa Nentawe Yilwatda, kan \u0199o\u0199arinsa na ci gaba da bun\u0199asa jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>Ya kuma jaddada cewa yayin da \u0199arin jama\u2019a ke ci gaba da rungumar manufofin jam\u2019iyyar tare da shiga cikinta, ya zama dole a samar da ingantaccen kundin rajistar mambobi wanda zai nuna ainihin \u0199arfin magoya bayan jam\u2019iyyar tun daga matakin \u0199asa.<\/p>\n<p>Mataimakin Gwamnan ya bu\u0199aci mahalarta taron su \u0257auki wannan aiki da muhimmanci, yana mai cewa nasarar shirin zai dogara ne kan jajircewarsu, gaskiya da kuma sadaukarwarsu.<\/p>\n<p>Mani Malam Mummuni ya \u0199ara da cewa wannan shiri ba wai don yin rijistar \u2019yan jam\u2019iyya ka\u0257ai ba ne, har ma don \u0199arfafa tsarin jam\u2019iyyar a matakin \u0199asa da kuma gina hadaddiyar dandali da zai ci gaba da wakiltar muradu da burin al\u2019ummar Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>Haka kuma, a madadin Gwamnan Jihar, Dakta Dauda Lawal, Mataimakin Gwamnan ya yi wa mahalarta taron fatan samun muhawara mai amfani da kuma nasarar gudanar da taron.<\/p>\n<p>Mataimakin Gwamnan ya yi rijistar ne tare da wasu mambobin Majalisar Zartarwa ta Jihar.<\/p>\n<p>COV \/ AMINU DALHATU<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Malam Mummuni, ya yi rijista a hukumance a matsayin cikakken \u0257an jam\u2019iyyar APC. An gudanar da rajistar ne a Fadar Gwamnatin Jihar Zamfara da ke Gusau, jim ka\u0257an bayan kaddamar da wani taron horaswa na kwanaki biyu kan rijistar \u2019yan jam\u2019iyya a dukkanin \u0199ananan hukumomi 14 da kuma gundumomi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8937,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[115],"class_list":["post-8936","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/208a6ad7-5da9-4a22-9943-d88eecb77fd7.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8936","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8936"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8936\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8938,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8936\/revisions\/8938"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8937"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8936"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8936"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8936"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}