{"id":8933,"date":"2026-03-13T09:08:00","date_gmt":"2026-03-13T09:08:00","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8933"},"modified":"2026-03-13T09:08:00","modified_gmt":"2026-03-13T09:08:00","slug":"jamiar-bayero-kano-ta-yi-martani-kan-zargin-damfarar-dalibi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamiar-bayero-kano-ta-yi-martani-kan-zargin-damfarar-dalibi\/","title":{"rendered":"Jami\u2019ar Bayero Kano Ta Yi Martani Kan Zargin Damfarar Dalibi"},"content":{"rendered":"<p>Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK) ta yi martani kan zarge-zargen da ke yawo cewa wani mutum da ake zargin yana ikirarin kasancewa dalibin jami\u2019ar yana aikata damfara ta yanar gizo tare da yin amfani da sunan wani.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Hul\u0257a da Jama\u2019a na jami\u2019ar, Lamara Garba, ya fitar, jami\u2019ar ta jaddada cewa tana da tsauraran \u0199a\u2019idoji kan halayya, ladabi da kuma \u0257abi\u2019ar da ake bukata daga dukkan dalibanta.<\/p>\n<p>Jami\u2019ar ta kuma bayyana cewa duk wani abu da wani dalibi ya aikata ba lallai ba ne ya wakilci dabi\u2019u da martabar jami\u2019ar gaba \u0257aya.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce bayan bullar zargin, jami\u2019ar ta fara bincike na farko domin gano gaskiyar lamarin, inda hukumomin jami\u2019ar ke duba batun bisa \u0199a\u2019idojin gudanarwa da hanyoyin ladabtarwa da aka tanada.<\/p>\n<p>Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya bayyana ne bayan Farfesa Farooq Kperogi, malamin sadarwa ta zamani a wata jami\u2019a da ke Amurka, ya bayyana a fili cewa wani da ake zargi da damfara yana ikirarin dalibi ne na BUK yana neman taimakon ku\u0257i tsawon shekaru domin biyan ku\u0257in makaranta.<\/p>\n<p>Malamin ya gano cewa mutumin yana amfani da sunan \u0199arya ne, har ma yana kwaikwayon mace domin samun ku\u0257i. Bayan wallafar bayanin Farfesa Kperogi, wasu mutane ma sun fito suna cewa su ma sun fuskanci irin wannan damfara.<\/p>\n<p>Jami\u2019ar ta yaba da \u0199o\u0199arin Farfesa Kperogi da sauran mutane masu taimaka wa dalibai mabukata ta hanyar tallafa musu da ku\u0257in rajista da sauran bukatun karatu, tana mai cewa irin wannan taimako na taimakawa wajen fa\u0257a\u0257a damar samun ilimi.<\/p>\n<p>Jami\u2019ar ta kuma tabbatar wa jama\u2019a cewa idan bincike ya tabbatar da zargin, za a \u0257auki matakin ladabtarwa da ya dace bisa dokokin jami\u2019ar da kuma dokokin \u0199asa.<\/p>\n<p>Har ila yau, jami\u2019ar ta bukaci jama\u2019a da su bar binciken ya kammala cikin natsuwa tare da kauce wa ya\u0257a bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.<\/p>\n<p>Rel \/ Khadijah Aliyu<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jami\u2019ar Bayero Kano (BUK) ta yi martani kan zarge-zargen da ke yawo cewa wani mutum da ake zargin yana ikirarin kasancewa dalibin jami\u2019ar yana aikata damfara ta yanar gizo tare da yin amfani da sunan wani. A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Hul\u0257a da Jama\u2019a na jami\u2019ar, Lamara Garba, ya fitar, jami\u2019ar ta jaddada cewa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8934,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[736],"class_list":["post-8933","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-buk"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/4346E770-A248-4CE0-8CCE-55CA1D22B476.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8933","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8933"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8933\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8935,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8933\/revisions\/8935"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8934"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8933"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8933"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8933"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}