{"id":8930,"date":"2026-03-13T09:04:49","date_gmt":"2026-03-13T09:04:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8930"},"modified":"2026-03-13T09:04:49","modified_gmt":"2026-03-13T09:04:49","slug":"matashi-mai-digiri-na-farko-na-sayar-da-ruwan-leda-a-taraba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/matashi-mai-digiri-na-farko-na-sayar-da-ruwan-leda-a-taraba\/","title":{"rendered":"Matashi Mai Digiri Na Farko Na Sayar Da Ruwan Leda A Taraba"},"content":{"rendered":"<p>Wani matashi mai digirin na 2 a fannin Ilimin (Theology) kuma wanda ya kammala karatun Physics, mai suna Hilekann Eric, na yawo a titunan garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, yana sayar da ruwan leda domin neman abin dogaro.<\/p>\n<p>Ana ganin Eric yana \u0257auke da kwandon ruwan leda a kansa yana kira ga masu wucewa a kan titi yana cewa, <em>\u201cPure water! Ice cold! Uku na naira 100!\u201d<\/em> yayin da rana ke tsananin duka a kansa.<\/p>\n<p>Lamarin ya sha bamban da irin nasarorin ilimi da ya samu a baya.<\/p>\n<p>An gano Eric ne a yankin Roadblock lokacin da wakilinmu ke tattaunawa da jama\u2019a kan aikin sake gina Gadar Namnai da Gwamnatin Tarayya ke yi.<\/p>\n<p>Eric, wanda ya fito daga al\u2019ummar Chanchanji a \u0199aramar hukumar Takum ta Jihar Taraba, ya bayyana takaicinsa kan halin da yake ciki.<\/p>\n<p>\u201cIna da digirin digirgir biyu, amma ga ni a kan titi ina sayar da ruwan leda saboda babu aikin yi. Ina ta aiki tukuru, amma duk da haka kamar ba komai na ke yi ba,\u201d in ji shi cikin damuwa.<\/p>\n<p>Ya ce rashin aikin yi na daga cikin dalilan da ke haifar da tashe-tashen hankula da aikata laifuka a wasu wurare.<\/p>\n<p>\u201cIdan gwamnati za ta duba halin da matasa ke ciki ta tallafa musu, za su iya zama mutane masu amfani ga al\u2019umma. Akwai mutane da za su iya kafa masana\u2019antu \u0257aya ko biyu a wannan yanki domin a \u0257auki matasa aiki,\u201d in ji Eric.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa shi ba shi ka\u0257ai ba ne cikin irin wannan hali, domin akwai \u0257imbin matasa masu digiri da ba su da aikin yi.<\/p>\n<p>\u201cWannan ruwan da kuke gani ina sayarwa shi ne abin da nake rayuwa da shi. Ina gode wa Allah da haka, domin ya fi na shiga sata ko wani abu na haram,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Eric ya kuma bayyana cewa wasu \u2019yan siyasa na amfani da matasa wajen ya\u0199in neman za\u0253e, amma bayan sun samu mulki ba su samar musu da aikin yi ba.<\/p>\n<p>A cewarsa, duk da cewa gwamnati ba za ta iya \u0257aukar dukkan marasa aikin yi aiki ba, kafa masana\u2019antu ka\u0257an zai taimaka wajen rage matsalar.<\/p>\n<p>Sai dai ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan bayar da kwangilar sake gina Gadar Namnai da ta rushe, yana mai cewa wannan wani muhimmin mataki ne.<\/p>\n<p>Sai dai ya nuna damuwa kan hanyar zuwa \u0199aramar hukumar Kurmi a jihar Taraba, wadda ya ce ta da\u0257e tana cikin mummunan hali amma har yanzu ba a gyara ta ba.<\/p>\n<p>\u201cBa wai babu manyan mutane a yankin ba, akwai su. Amma har yanzu ba su gyara hanyar ba, sai dai su ri\u0199a amfani da ita wajen yaudarar jama\u2019a a lokacin ya\u0199in neman za\u0253e,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>A halin yanzu, Hilekann Eric na ci gaba da sayar da ruwan leda tare da fatan wata rana al\u2019amuransa za su canza.<\/p>\n<p>Ya kuma bar lambar wayarsa ga duk wanda zai iya taimaka masa: 08120231338<\/p>\n<p>Sani Sulaiman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wani matashi mai digirin na 2 a fannin Ilimin (Theology) kuma wanda ya kammala karatun Physics, mai suna Hilekann Eric, na yawo a titunan garin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, yana sayar da ruwan leda domin neman abin dogaro. Ana ganin Eric yana \u0257auke da kwandon ruwan leda a kansa yana kira ga masu wucewa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8931,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[2000],"class_list":["post-8930","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ruwan-leda"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/75b65163-87b8-449f-afc7-939928b224d4.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8930","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8930"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8930\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8932,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8930\/revisions\/8932"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8931"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8930"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8930"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8930"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}