{"id":8924,"date":"2026-03-11T21:42:56","date_gmt":"2026-03-11T21:42:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8924"},"modified":"2026-03-11T21:42:56","modified_gmt":"2026-03-11T21:42:56","slug":"taiwo-oyedele-zai-maye-gurbin-minista-a-maaikatar-kudi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/taiwo-oyedele-zai-maye-gurbin-minista-a-maaikatar-kudi\/","title":{"rendered":"Taiwo Oyedele Zai Maye Gurbin Minista a Ma&#8217;aikatar Kudi"},"content":{"rendered":"<p><em><strong>Daga Bashir Meyere<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Majalisar Dattawa ta tabbatar da na\u0257in Mista Taiwo Oyedele a matsayin Ministan kasa,.<\/p>\n<p>Kafin nadin nasa, Mista Taiwo ya kasance Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban \u0198asa kan dokokin gyaran haraji, inda ya taka rawar gani wajen jagorantar dokokin gyaran haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, sannan Shugaban \u0198asa Bola Ahmad Tinubu ya rattaba hannu a kansu.<\/p>\n<p>Tabbatar da na\u0257in nasa ya biyo bayan sa\u2019o\u2019i na tambayoyi masu zurfi daga sanatoci daga jam\u2019iyyun siyasa daban-daban, kan batutuwan tsaro, tattalin arziki da harkokin ku\u0257i da suka shafi ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin \u2018yan Najeriya.<\/p>\n<p>Yayin da yake amsa wasu daga cikin tambayoyin, Taiwo Oyedele ya bayyana cewa sayar da \u0257anyen mai na iya taimakawa wajen \u0199arfafa tattalin arziki, daidaita kudaden shiga na gwamnati, tare da samar da daidaitaccen farashin man fetur a \u0199asar.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa idan aka kayyade farashi na wani kaso na \u0257anyen man Najeriya na wani lokaci, gwamnati za ta iya tabbatar da samun kasafin ku\u0257i tare da rage tasirin sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.<\/p>\n<p>Dangane da matsalar rashin biyan ku\u0257in \u2018yan kwangila saboda \u0199arancin ku\u0257a\u0257en shiga, Oyedele ya ba da shawarar cewa a rika ba da kwangiloli ne gwargwadon ku\u0257in da ake da su domin kauce wa taruwar matsalolin biyan ku\u0257in da sauransu.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa irin wannan yanayi na iya sa kwangilar da aka fara da farashin naira biliyan \u0257aya ta tashi zuwa naira biliyan biyu, domin rufe asarar da \u2018yan kwangila ke yi sakamakon jinkirin biyan su daga gwamnati.<\/p>\n<p>Game da hanyoyin samun ku\u0257a\u0257en shiga na \u0199asar, Oyedele ya ce an fi mayar da hankali kan harajin man fetur da iskar gas, yayin da sauran fannoni kamar ma\u2019adinai ke da babbar dama ta samar da ku\u0257a\u0257en shiga, amma ba a ba su kulawa yadda ya kamata ba.<\/p>\n<p>Oyedele ya jaddada bu\u0199atar yin sahihin kasafin ku\u0257i\u00a0 tare da aiwatar da ayyukan da aka amince da su yadda ya kamata. Ya ce idan aka yi kasafin ku\u0257i, dole ne a tabbatar da cewa akwai ku\u0257in da za a aiwatar da shi, tare da sakin ku\u0257a\u0257e domin a kammala ayyukan musamman na ababen more rayuwa.<\/p>\n<p>A jawabin sa bayan tabbatar da na\u0257i, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan na\u0257in Oyedele, yana mai cewa mutum ne mai \u0199warewa kuma ya dace da wannan mu\u0199ami.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Bashir Meyere Majalisar Dattawa ta tabbatar da na\u0257in Mista Taiwo Oyedele a matsayin Ministan kasa,. Kafin nadin nasa, Mista Taiwo ya kasance Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban \u0198asa kan dokokin gyaran haraji, inda ya taka rawar gani wajen jagorantar dokokin gyaran haraji da Majalisar Tarayya ta amince da su, sannan Shugaban \u0198asa Bola [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8925,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[11,12],"tags":[211,488],"class_list":["post-8924","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labaran-gida","category-labaran-ketare","tag-majalisa","tag-minista"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/Taiwo-Oyedele.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8924","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8924"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8924\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8926,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8924\/revisions\/8926"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8925"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8924"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8924"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8924"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}