{"id":8908,"date":"2026-03-10T22:06:19","date_gmt":"2026-03-10T22:06:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8908"},"modified":"2026-03-10T22:06:19","modified_gmt":"2026-03-10T22:06:19","slug":"nema-da-masu-ruwa-da-tsaki-sun-kara-ha%c9%97a-gwiwa-don-hana-aukuwar-ambaliya-da-hadarin-tankar-mai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nema-da-masu-ruwa-da-tsaki-sun-kara-ha%c9%97a-gwiwa-don-hana-aukuwar-ambaliya-da-hadarin-tankar-mai\/","title":{"rendered":"NEMA Da Masu Ruwa Da Tsaki Sun Kara Ha\u0257a Gwiwa Don Hana Aukuwar Ambaliya Da Hadarin Tankar Mai"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>By Adamu Yusuf<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta \u0198asa (NEMA), tare da ha\u0257in gwiwar masu ruwa da tsaki da ke kula da harkokin bala\u2019o\u2019i a Jihar Kaduna, sun sake ha\u0257a karfi da karfe domin rage aukuwar bala\u2019o\u2019i a wannan shekarar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake magana a wajen taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a ofishin NEMA da ke Kaduna domin duba abubuwan da suka faru na bala\u2019o\u2019i a shekarar da ta gabata, Shugaban Ayyuka na hukumar NEMA mai kula da jihohin Katsina da Kaduna, Suleiman Mohammed, ya ce hukumar ta sauya tsarin aikin ta daga bayar da taimako gaggawa bayan bala\u2019i ya faru zuwa \u0257aukar matakan kare faruwar bala\u2019i baki daya.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8912\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0084-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0084-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0084-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0084.jpg 1016w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa bayan hukumomin da suka dace kamar Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya sun fitar da hasashen yanayi na kakar daminan bana, hukumar NEMA ta shirya irin wannan taron masu ruwa da tsaki tun farkon shekarar domin nazarin yiwuwar illolin da ka iya tasowa tare da tsara hanyoyin da za a bi wajen shawo kan bala\u2019o\u2019i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, taron ya ha\u0257a manyan masu ruwa da tsaki da suka tattauna hanyoyin da za su yi aiki tare wajen tunkarar bala\u2019o\u2019i tun kafin su faru da lokacin da suke faruwa, da kuma bayan sun faru.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Suleiman Mohammed ya kuma bayyana cewa ha\u0257in gwiwar hukumomi kamar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA), Kungiyar Red Cross, Hukumar Kashe Gobara, Civil Defence da sauran hukumomi ya taimaka wajen magance wasu bala\u2019o\u2019i da suka faru a jihar a shekarar da ta gabata, ciki har da ambaliya, gobara da kuma hatsarin tankokin mai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya tuna cewa an gudanar da wani atisayen kwaikwayo kan yadda za a magance hatsarin tankokin mai a Maraban Jos, domin nuna yanda hukumar take gudanar da ayyukan ceto da agajin gaggawa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cAtisayen wanda ya ha\u0257a da direbobin tankokin mai da sauran masu ruwa da tsaki, an shirya shi ne domin \u0199arfafa shirin ko-ta-kwana da kuma tabbatar da ha\u0257in gwiwar da ya dace idan irin wa\u0257annan bala\u2019o\u2019i suka faru.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa duk da cewa an samu wasu ambaliyar ruwa a yankuna kamar Kaduna North, Kaduna South, Zaria da kuma \u0199aramar hukumar Sanga, saurin \u0257aukar mataki da hukumomin agaji suka yi ya taimaka wajen rage illolin da bala\u2019in ya jawo ga al\u2019ummomin da abin ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Sashen Kula da Bala\u2019o\u2019i na Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Najeriya (NSCDC) a Jihar Kaduna, Mataimakin Kwamandan Hukumar Akaine King Michael, ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci kuma da ya zo a kan lokaci domin nazarin ayyukan kula da bala\u2019o\u2019i na shekarar da ta gabata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce taron ya ba masu ruwa da tsaki damar tantance abubuwan da suka faru a shekarar 2025, musamman hatsarin tankokin mai da ke \u0257auke da man fetur, wanda sau da dama kan haddasa zubar mai a kan hanyoyi tare da jefa rayuka da dukiyoyi cikin ha\u0257ari.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8910\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0086-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0086-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0086-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0086.jpg 1016w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Michael ya kuma bayyana cewa hukumar NSCDC na ci gaba da aiki tare da NEMA wajen gudanar da ayyukan ceto yayin bala\u2019o\u2019i, inda ya ce babban aikin su shi ne fitar da mutanen da abin ya shafa daga wuraren ha\u0257ari, kulle wuraren da lamarin ya faru da kuma hana jama\u2019a \u0257iban mai idan tankar mai ta yi hatsari..<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nata jawabin, Shugabar Sashen Muhalli da Sauyin Yanayi da Makamashi na Hukumar Wayar da Kai ta \u0198asa (NOA) a Jihar Kaduna, Rahmatu Suleiman, ta bayyana muhimmiyar rawar da hukumar ke takawa wajen wayar da kan jama\u2019a da kuma ha\u0257a kai da al\u2019umma domin hana aukuwar bala\u2019o\u2019i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce NOA na aiki kafada da kafada da NEMA wajen isar da sa\u0199onnin wayar da kai ga al\u2019ummomi a fa\u0257in jihar, inda ta bayyana cewa hukumar na da ma\u2019aikata a dukkan \u0199ananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna da ke gudanar da wayar da kan jama\u2019a kan ha\u0257arin bala\u2019o\u2019i kamar ambaliya.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8911\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0085-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0085-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0085-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0085.jpg 1016w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Rahmatu Suleiman ta \u0199ara da cewa hukumar na kuma aiki tare da kafafen ya\u0257a labarai domin \u0199ara wayar da kan jama\u2019a, inda ta bayyana cewa Daraktan NOA na Jihar Kaduna, Danjuma Makama, kan bayyana a kafafen ya\u0257a labarai sau da dama domin ilmantar da jama\u2019a kan matakan kariya da kuma hanyoyin rage illolin ambaliya da sauran bala\u2019o\u2019i.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mahalartar taron sun jaddada muhimmancin ci gaba da ha\u0257in gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati, shugabannin al\u2019umma da kuma jama\u2019a domin hana aukuwar bala\u2019o\u2019i da kuma tabbatar da saurin kai dauki idan suka faru.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sun kuma yi kira a ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama\u2019a domin gujewa halayen da kan jawo hatsari ko \u0199ara tsananta matsaloli, musamman a lokutan hatsarin tankokin mai da kuma ambaliya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; By Adamu Yusuf &nbsp; Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta \u0198asa (NEMA), tare da ha\u0257in gwiwar masu ruwa da tsaki da ke kula da harkokin bala\u2019o\u2019i a Jihar Kaduna, sun sake ha\u0257a karfi da karfe domin rage aukuwar bala\u2019o\u2019i a wannan shekarar. &nbsp; Da yake magana a wajen taron masu ruwa da tsaki da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":8909,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[320,1998,1999,1997,1847,1996,810],"class_list":["post-8908","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-ambaliya","tag-aukuwar","tag-hadarin-tankar-mai","tag-haa-gwiwa","tag-hana","tag-masu-ruwa-da-tsaki","tag-nema"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260310-WA0082.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8908","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8908"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8908\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8913,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8908\/revisions\/8913"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8909"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8908"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8908"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8908"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}