{"id":8905,"date":"2026-03-09T22:11:24","date_gmt":"2026-03-09T22:11:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8905"},"modified":"2026-03-09T22:11:24","modified_gmt":"2026-03-09T22:11:24","slug":"kaduna-ta-kaddamarda-shirin-rabon-maganin-kariya-daga-cutar-dundumi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kaduna-ta-kaddamarda-shirin-rabon-maganin-kariya-daga-cutar-dundumi\/","title":{"rendered":"Kaduna Ta Kaddamarda Shirin Rabon Maganin Kariya Daga Cutar Dundumi"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga Khadija Kubau<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ma\u2019aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda ha\u0257in gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba magunguna domin kare al\u2019umma daga kamuwa daga cutar dundumi River Blindness a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a Cibiyar Kula da Lafiya ta Matakin Farko (PHC) da ke Kinkinau a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, inda jami\u2019an lafiya da shugabannin al\u2019umma da kuma abokan hul\u0257a suka halarta domin tallafawa yaki da cututtukan da aka yi watsi da su wato Neglected Tropical Diseases<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Umma K. Ahmed, wadda ta kaddamar da shirin rabon magungunan, ta bayyana cewa za a gudanar da shirin ne a kananan hukumomi shida daga cikin kananan hukumomi 23 na jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamishinar, wadda Daraktan Kiwon Lafiyar Jama\u2019a, Dakta Abubakar Sadiq Idris ya wakilta, ta ce an zabi Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu ne domin fara shirin saboda bincike ya nuna cewa akwai mutane da dama da cutar ta fi shafa a yankin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta kara da cewa za a raba magungunan ga mutane masu shekaru biyar zuwa sama domin dakile yaduwar cutar tare da rage illolinta a cikin al\u2019umma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da take jawabi a wajen taron, Madam Gong, wadda ta wakilci Daraktar kungiyar Sightsavers Nigeria, Farfesa Joy Shuaibu, ta roki al\u2019umma da su rika shan magungunan kamar yadda jami\u2019an lafiya suka umarta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta jaddada cewa hadin kan al\u2019umma yana da matukar muhimmanci wajen cimma burin kawar da cutar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko, jami&#8217;ar kulada Cututtukan da aka yi watsi da su, (NTD), Zainab Haruna, ta bayyana manufofin shirin, inda ta ce an kirkiro shi ne domin rage yawaitar cutar ta hanyar raba magungunan kariya kyauta ga al\u2019umma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta kuma bukaci mazauna yankin da su baiwa jami\u2019an lafiya hadin kai tare da halartar shirin domin cin gajiyar magungunan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Daraktan Kiwon Lafiyar Jama\u2019a, Dakta Abubakar Sadiq Idris, ya jaddada kudurin gwamnatin jihar na ci gaba da yakar cututtukan da aka yi watsi da su ta hanyar shirye-shiryen kiwon lafiya da kuma hadin gwiwa da kungiyoyin tallafi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A jawabin maraba, wakilin Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Dakta Maidubu, ya gode wa Ma\u2019aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna da kuma kungiyar Sightsavers bisa tallafinsu ga wannan shiri.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa za a raba magungunan yadda ya kamata domin tabbatar da cewa duk wadanda suka cancanta sun amfana da shirin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Hakimin Tudun Wada, Alhaji Tahir Mahmud, wanda shi ne Uban Taron, ya yi alkawarin cikakken goyon bayan masarautar gargajiya domin ganin shirin ya yi nasara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa za su wayar da kan al\u2019umma tare da karfafa musu gwiwa su fito domin karbar magungunan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daya daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin mahalarta taron shi ne wasan kwaikwayo da aka gabatar domin wayar da kan al\u2019umma kan haddasuwar cutar, hanyoyin kariya, da kuma muhimmancin halartar shirin rabon magungunan.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Daga Khadija Kubau &nbsp; Ma\u2019aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna tareda ha\u0257in gwiwar kungiyar Sightsavers sun kaddamar da shirin raba magunguna domin kare al\u2019umma daga kamuwa daga cutar dundumi River Blindness a jihar. &nbsp; An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a Cibiyar Kula da Lafiya ta Matakin Farko (PHC) da ke Kinkinau a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":8906,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[1995,743,33,1005,1199,1994,744],"class_list":["post-8905","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-cutar-dundumi","tag-kaddamarda","tag-kaduna","tag-kariya","tag-maganin","tag-rabon","tag-shirin"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG_20260309_113757_044-scaled.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8905","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8905"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8905\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8907,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8905\/revisions\/8907"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8906"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8905"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8905"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8905"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}