{"id":8896,"date":"2026-03-09T09:48:28","date_gmt":"2026-03-09T09:48:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8896"},"modified":"2026-03-09T09:48:28","modified_gmt":"2026-03-09T09:48:28","slug":"ncaa-ta-yaba-wa-hukumar-alhazai-ta-jihar-kebbi-bisa-kyakkyawan-tanadin-aikin-hajji","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ncaa-ta-yaba-wa-hukumar-alhazai-ta-jihar-kebbi-bisa-kyakkyawan-tanadin-aikin-hajji\/","title":{"rendered":"NCAA ta Yaba wa Hukumar Alhazai ta Jihar Kebbi Bisa Kyakkyawan Tanadin Aikin Hajji"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Sani Dutsinma<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kebbi bayan duba kayayyakin aiki da shirye-shiryen da aka tanada domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara.<\/p>\n<p>Shugaban tawagar binciken, Injiniya Abba Shu&#8217;aibu Babagana ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya jagoranta zuwa jihar ta Kebbi.<\/p>\n<p>A yayin ziyarar, jami\u2019an NCAA sun duba muhimman wurare da dama a sansanin Alhazai na Kauran Gwandu Hajj Camp domin tantance yadda aka shirya kafin fara jigilar maniyyata zuwa aikin Hajjin bana.<\/p>\n<p>Sun kuma ziyarci Cibiyar ICT, inda ake gudanar da rajista da sarrafa bayanan maniyyata ta hanyar fasahar zamani.<\/p>\n<p>Hakazalika, tawagar ta duba Dakin Taro da ake amfani da shi wajen gudanar da tarurruka, da kuma Dakin Tantancewa\u00a0 inda ake\u00a0 gwajin lafiya, tabbatar da takardu, da sauran matakan tantancewa domin tabbatar da ganin dukkan maniyyata sun cika ka\u2019idojin tafiya kafin a tafi aikin Hajji.<\/p>\n<p>Jami\u2019an NCAA sun kuma zagaya harabar sansanin Alhazan gaba \u0257aya, inda suka nuna gamsuwa da tsafta, tsari, da kuma kayayyakin da aka tanada domin tallafawa maniyyata yayin shirye-shiryen tafiya.<\/p>\n<p>A cewar jami\u2019an, kayayyakin more rayuwa da tsare-tsaren da Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kebbi ta samar, na nuna irin \u0199o\u0199arin gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa an gudanar da aikin Hajji cikin tsari, aminci, da inganci.<\/p>\n<p>Ziyarar na daga cikin binciken da hukumar ke yi akai-akai domin tabbatar da cewa jihohi suna bin \u0199a\u2019idojin sufurin jiragen sama da ka\u2019idojin aiki da ake bu\u0199ata domin nasarar jigilar maniyyata zuwa Saudi Arabia.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Sani Dutsinma Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA), ta yaba da kokarin Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Kebbi bayan duba kayayyakin aiki da shirye-shiryen da aka tanada domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara. Shugaban tawagar binciken, Injiniya Abba Shu&#8217;aibu Babagana ne ya bayyana hakan yayin ziyarar aiki da ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8897,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1906,139,1987,97],"class_list":["post-8896","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-2026hajj","tag-kebbi","tag-ncaa","tag-ziyara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260309-WA0002.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8896","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8896"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8896\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8898,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8896\/revisions\/8898"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8897"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8896"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8896"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8896"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}