{"id":8868,"date":"2026-03-06T22:21:27","date_gmt":"2026-03-06T22:21:27","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8868"},"modified":"2026-03-06T22:21:27","modified_gmt":"2026-03-06T22:21:27","slug":"ramadan-tinubu-ya-kara-jaddada-kudirinsa-na-inganta-rayuwar-jamian-soji","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ramadan-tinubu-ya-kara-jaddada-kudirinsa-na-inganta-rayuwar-jamian-soji\/","title":{"rendered":"Ramadan: Tinubu Ya Kara Jaddada Kudirinsa na Inganta Rayuwar Jami\u2019an Soji"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Bello Wakili\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Shugaban \u0199asa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana godiya ga jami&#8217;an Rundunar Sojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare \u0199asar, tare da tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da inganta jin da\u0257insu da kuma tallafa wa ayyukansu.<\/p>\n<p>Shugaban ya bayar da wannan tabbaci ne yayin wani taron bu\u0257a-baki na mabiya addinin Musulunci da na Kirista da ya yi tare da jami&#8217;an Rundunar Sojin \u0199asa da sauran hukumomin tsaro a Fadar Shugaban \u0198asa da ke Abuja.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya ce taron ya nuna ha\u0257in kan al\u2019ummar Najeriya, yana mai cewa watan Ramadan lokaci ne na yin tunani a kan rayuwa, tsarkake\u00a0 zuciya da kuma \u0199arfafa zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai.<\/p>\n<p>Ya yaba wa sojoji kan jajircewarsu wajen kare \u0199asa duk da \u0199alubalen da suke fuskanta, ciki har da nisantar iyalansu da kuma fuskantar barazanar \u2018yan ta\u2019adda da \u2018yan Bindiga.<\/p>\n<p>Shugaban \u0199asar ya tabbatar musu cewa sadaukarwar da suke yi ba za ta fadi a banza ba, yana mai \u0199ara cewa jin da\u0257in sojoji da iyalansu zai ci gaba da kasancewa muhimmin abin da gwamnatinsa za ta bai wa fifiko.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya kuma amince da cewa akwai matsalolin \u0199arancin gidaje ga sojoji, yana mai cewa gwamnati na aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar.<\/p>\n<p>Dangane da halin tattalin arzikin \u0199asar, shugaban ya bayyana cewa duk da cewa Najeriya ta fuskanci \u0199alubale masu tsanani a farkon mulkinsa, matakan da gwamnati ta \u0257auka sun fara haifar da Da mai ido.<\/p>\n<p>Ya bayyana kwarin gwiwa cewa \u0199asar ta fara fita daga mawuyacin hali na tattalin arziki, tare da bada tabbacin cewa nan gaba kadan za a kara ganin canji mai ma&#8217;ana a Najeriya.<\/p>\n<p>Shugaban \u0199asar ya kuma mi\u0199a ta\u2019aziyya ga gwamnati da al\u2019ummar Jihar Borno kan wani sabon lamari na rashin tsaro da ya faru a jihar, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tallafa wa \u0199o\u0199arin da ake yi domin kawo \u0199arshen ta\u2019addanci da \u2018yan bindiga a fa\u0257in \u0199asar.<\/p>\n<p>Tun da farko, Babban Hafsan Sojin \u0198asa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya gode wa shugaban \u0199asa bisa shirya taron bu\u0257a-bakin na ha\u0257in gwiwar addinai, tare da yaba masa kan amincewa da matakan da nufinsu shi ne inganta jin da\u0257in jami\u2019an rundunar soji.<\/p>\n<p>Ya kuma yaba wa shugaban \u0199asan kan amincewa da \u0199arin albashi ga sojoji, \u0199arin alawus ga rundunar Brigade of Guards, da kuma amincewa da sayen sabbin kayan aiki da inganta matsugunan sojoji.<\/p>\n<p>Laftanar Janar Shaibu ya ce wa\u0257annan matakai za su taimaka matu\u0199a wajen \u0199ara inganta aikin rundunar da kuma \u0199arfafa gwiwar jami\u2019anta.<\/p>\n<p>Haka kuma ya sake jaddada biyayyar rundunar sojin \u0199asa ga shugaban \u0199asa, tare da tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen kare dimokura\u0257iyyar Najeriya da kuma martabar \u0199asar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Bello Wakili\u00a0 Shugaban \u0199asa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana godiya ga jami&#8217;an Rundunar Sojin Najeriya bisa sadaukarwar da suke yi wajen kare \u0199asar, tare da tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da inganta jin da\u0257insu da kuma tallafa wa ayyukansu. Shugaban ya bayar da wannan tabbaci ne yayin wani taron bu\u0257a-baki [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8869,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[215,218,1985,89],"class_list":["post-8868","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-buda-baki","tag-ramadan","tag-soji","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/8a951b10-ddf8-46d1-849f-e7ebfa40cb6f.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8868","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8868"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8868\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8870,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8868\/revisions\/8870"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8869"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8868"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8868"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8868"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}