{"id":883,"date":"2024-04-04T08:15:04","date_gmt":"2024-04-04T08:15:04","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=883"},"modified":"2024-04-04T08:15:04","modified_gmt":"2024-04-04T08:15:04","slug":"gwamnatin-kaduna-ta-raba-tallafi-ga-wadanda-yan-fashin-daji-suka-raba-da-gidajen-su","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kaduna-ta-raba-tallafi-ga-wadanda-yan-fashin-daji-suka-raba-da-gidajen-su\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kaduna Ta Raba Tallafi Ga Wadanda &#8216;Yan Fashin Daji Suka Raba Da Gidajen su"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-884\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e-300x225.jpeg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e-300x225.jpeg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e-1024x768.jpeg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e-768x576.jpeg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e.jpeg 1040w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rabon kayan abinci ga \u2018yan gudun hijira sama da dubu daya da \u2018yan fashi daji suka raba da gidajensu a karamar hukumar Kajuru.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe da ta kaddamar da rabon kayayyakin a karamar hukumar Kajuru ta ce gwamnati ta kudiri aniyar samar da yanayi mai aminci da wadata ga kowa da kowa kuma ba za ta huta ba har sai an kawar da barazanar \u2018yan fashin daji.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dokta Balarabe wanda mataimakin shugaban ma\u2019aikata a ofishinta, Mista James Kanyip ya wakilta, ya bayyana cewa, a matsayinsu na gwamnati, ya zama wajibi su tabbatar da tabbatar da walwala da jin dadin al\u2019ummarta, musamman a wannan lokaci da suke cikin mawuyacin hali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ta ce Gwamna Uba Sani ya fahimci radadin da suke ciki sakamakon rashin tausayi da Imani da aka nuna musu don haka ba a za ayi kasa a gwiwa ba wajen basu taimako da tallafi ga wadanda abin ya shafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewar Dokta Balarabe, kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da manyan motoci guda biyu da garin masara da kuma shinkafa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake jawabi ga \u2018yan gudun hijirar, Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna KADSEMA, Dokta Usman Mazadun ya ce kimanin \u2018yan gudun hijira dubu dari biyu da casa\u2019in ne aka samu a kananan hukumomi 12 na jihar Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mista Mazadun ya bayyana cewa a karamar hukumar Chikun, matsalar rashin tsaro ta shafi al\u2019ummomi 134 da kuma mutane 26,345 da suka rasa matsugunansu yayin da a Birnin Gwari, al\u2019ummomi 84 da abin ya shafa kuma 70,893 suka rasa matsugunansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dakta Usman Mazadun ya kuma bayyana cewa nan da \u2018yan makonni masu zuwa gwamnati za ta mika rabon tallafin ga daukacin al\u2019ummomin da abin ya shafa a kananan hukumomi 12 da aka tantance.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake magana da manema labarai, shugaban karamar hukumar Kajuru, Mista Ibrahim Gajere, ya bayyana fatansa cewa, \u2018yan gudun hijira na karamar hukumar Kajuru ne suka fara cin gajiyar tallafin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Basaraken Kufana Gwan Kufana, Mista Titus Dauda, \u200b\u200bya nuna matukar godiya ga Gwamnan, da kuma tawagarsa bisa namijin kokarin da suke yi na ganin an kai agaji ga wadanda suka fi bukata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa aikin alheri ba wai kawai samar da ababen more rayuwa ba ne, har ma ya kara dankon zumunci tsakanin gwamnati da jama\u2019a.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wadanda suka ci gajiyar tallafin, sun nuna jin dadinsu ga jihar Kaduna bisa samar da tallafin da suka hada da Shinkafa da garin tuwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aminu Dalhatu\/Wababe<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kaduna ta fara rabon kayan abinci ga \u2018yan gudun hijira sama da dubu daya da \u2018yan fashi daji suka raba da gidajensu a karamar hukumar Kajuru. &nbsp; Mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Balarabe da ta kaddamar da rabon kayayyakin a karamar hukumar Kajuru ta ce gwamnati ta kudiri aniyar samar da yanayi mai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":884,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10,2,9],"tags":[27],"class_list":["post-883","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","category-siyasa","category-tattalin-arziki","tag-abinci"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/ef617a7a-4f3c-40c3-be63-70eee14b969e.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/883","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=883"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/883\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":885,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/883\/revisions\/885"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/884"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=883"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=883"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=883"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}