{"id":8784,"date":"2026-03-04T11:31:33","date_gmt":"2026-03-04T11:31:33","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8784"},"modified":"2026-03-04T11:31:33","modified_gmt":"2026-03-04T11:31:33","slug":"gwamnatin-jigawa-za-ta-kashe-miliyoyin-naira-don-sayen-gidaje-96-daga-gwamnatin-tarayya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-za-ta-kashe-miliyoyin-naira-don-sayen-gidaje-96-daga-gwamnatin-tarayya\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Miliyoyin Naira Don Sayen Gidaje 96 Daga Gwamnatin Tarayya"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda 96 daga gwamnatin tarayya.<\/p>\n<p>Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al\u2019adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim ka\u0257an bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Dutse.<\/p>\n<p>A cewarsa, majalisar ta amince da sayen gidajen ne daga Ma\u2019aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa sayen gidajen na da nufin magance matsalar matsuguni a cikin jihar, musamman ga ma\u2019aikatan gwamnati da sauran wa\u0257anda suka cancanta.<\/p>\n<p>Ya ce shirin na daga cikin Ajandar Gwamna Umar Namadi 12, wadda ta \u0199unshi babbar dabarar bunkasa gidaje da raya birane, domin samar da matsuguni mai kyau, rage gibin gidaje, da inganta rayuwar al\u2019umma.<\/p>\n<p>Wannan na daga cikin \u0199o\u0199arin gwamnatin na fa\u0257a\u0257a damar samun gidaje masu araha da kuma kyautata jin da\u0257in jama\u2019a.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa majalisar ta amince da kashe sama da Naira miliyan 914 domin \u0199arin ayyuka a kan aikin gina hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje, wadda za ta ha\u0257a da hanyar Yan Dutse zuwa Chori.<\/p>\n<p>Sagir ya ce \u0199arin ayyukan sun zama wajibi bayan \u0199arin binciken fasaha da bitar aikin da aka gudanar, domin \u0199ara inganta \u0199arfinsa da tsarin magudanan ruwa.<\/p>\n<p>Ya ce majalisar ta ce sauyin da aka yi a cikin tsarin aikin zai tabbatar da cewa aikin ya cika \u0199a\u2019idojin da ake bu\u0199ata, tare da biyan bu\u0199atun zirga-zirgar al\u2019ummomin da za su amfana da shi.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya \u0199ara da cewa, da wannan amincewar, jimillar ku\u0257in kwangilar aikin ta kai sama da Naira Biliyan 5.4. Yana mai cewa hanyar Chuwasu zuwa Chakwaikwaiwa zuwa Zango Maje muhimmiyar hanya ce ta karkara wadda aka tsara domin inganta ha\u0257in kai tsakanin al&#8217;umma, sau\u0199a\u0199a jigilar amfanin gona,\u00a0 \u0199ara samun damar isa kasuwanni, makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da bun\u0199asa tattalin arzi\u0199i a yankin da abin ya shafa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 853 domin sayen gidaje guda 96 daga gwamnatin tarayya. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al\u2019adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim ka\u0257an bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Fadar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8785,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[540,59],"class_list":["post-8784","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gidaje","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/IMG-20260304-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8784","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8784"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8784\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8786,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8784\/revisions\/8786"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8785"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8784"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8784"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8784"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}