{"id":8731,"date":"2026-03-02T09:08:43","date_gmt":"2026-03-02T09:08:43","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8731"},"modified":"2026-03-02T09:08:43","modified_gmt":"2026-03-02T09:08:43","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-fa%c9%97a%c9%97a-rijistar-tallafin-jamaa-domin-tantance-masu-bu%c6%99ata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-fa%c9%97a%c9%97a-rijistar-tallafin-jamaa-domin-tantance-masu-bu%c6%99ata\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Fa\u0257a\u0257a Rijistar Tallafin Jama\u2019a Domin Tantance Masu Bu\u0199ata"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya na fa\u0257a\u0257a tare da \u0199arfafa Rijistar Tallafin Jama\u2019a ta \u0198asa National Social Register domin tabbatar da cewa an tantance gidaje marasa \u0199arfi a fa\u0257in \u0199asar nan yadda ya kamata, an yi musu rajista, tare da ha\u0257a su cikin tsare-tsaren kariya da tallafin zamantakewa.<\/p>\n<p>Ministan Ma\u2019aikatar Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, ya bayyana haka a wajen \u0199addamar da rabon kayan tallafin abinci da na gina jiki \u0199ar\u0199ashin Shirin Shugaban \u0198asa na Tallafin Abinci da Gina Jiki, wanda aka gudanar a Minna, Jihar Niger.<\/p>\n<p>Dakta Bernard Doro ya ce ma\u2019aikatar za ta yi aiki kafada da kafada da Gwamnatin Jihar Niger domin tabbatar da cewa an yi rajistar dukkan masu cin gajiyar shirin da mutanen da lamarin ya shafa a fa\u0257in jihar, ta yadda za su cancanci shiga shirye-shiryen kariya da rage talauci na Gwamnatin Tarayya.<\/p>\n<p>A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta himmatu wajen tabbatar da cewa samar da wadataccen abinci, rage talauci da kuma kare al\u2019umma masu rauni sun kasance ginshi\u0199ai a tsarin mulkinta, domin kada a bar kowane \u0257an Najeriya mai bu\u0199ata a baya.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Niger, Mohammed Umar Bago, ya gode wa Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ci gaba da bai wa jihar goyon baya. Ya kuma yaba wa hukumomin tallafi da sauran masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudunmawa.<\/p>\n<p>Mohammed Umar Bago ya bayyana cewa Jihar Niger na da kusan kashi goma cikin \u0257ari na fa\u0257in \u0199asar Najeriya, lamarin da ke sa kula da tsaro a dukkan sassan jihar ya zama \u0199alubale ba tare da cikakken goyon bayan Gwamnatin Tarayya ba. Ya kuma jaddada \u2018yancin yara na zuwa makaranta, tare da kira ga ha\u0257in gwiwar dukkan masu ruwa da tsaki domin mayar da yara makarantu, don kauce wa fa\u0257awa cikin ayyukan ta\u2019addanci.<\/p>\n<p>Sakataren dindindin na Ma\u2019aikatar Harkokin Jin-\u0199ai da Kula da Bala\u2019o\u2019i, Mista Olu Bunmi Olusanya, ya bayyana cewa tallafin ya yi daidai da gyare-gyaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa, wa\u0257anda suka mayar da hankali kan gaskiya da adalci wajen za\u0253en masu amfana, da ingantaccen isar da tallafi kai tsaye ga wa\u0257anda suka fi bu\u0199ata cikin mutunci da kan lokaci.<\/p>\n<p>Shi ma Kwamishinan Harkokin Jin-\u0199ai da Kula da Bala\u2019o\u2019i na Jihar Niger, Ibrahim Inga, ya ce duk da nasarorin da ma\u2019aikatar ta samu tun bayan kafuwarta kimanin shekaru uku da suka gabata, tana fuskantar \u0199alubale da dama sakamakon \u0199arancin ku\u0257a\u0257e da yawaitar bala\u2019o\u2019i. Don haka ya bu\u0199aci \u0199arin tallafi daga Gwamnatin Tarayya, tare da yin kira ga masu amfana da kada su sayar da kayan tallafin a kasuwa.<\/p>\n<p>Aliyu Lawal<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya na fa\u0257a\u0257a tare da \u0199arfafa Rijistar Tallafin Jama\u2019a ta \u0198asa National Social Register domin tabbatar da cewa an tantance gidaje marasa \u0199arfi a fa\u0257in \u0199asar nan yadda ya kamata, an yi musu rajista, tare da ha\u0257a su cikin tsare-tsaren kariya da tallafin zamantakewa. Ministan Ma\u2019aikatar Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8732,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[469],"class_list":["post-8731","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-fg"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/3478e444-4e3f-4441-8f87-47d02cf37434.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8731","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8731"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8731\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8733,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8731\/revisions\/8733"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8732"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8731"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8731"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8731"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}