{"id":8725,"date":"2026-03-02T08:58:11","date_gmt":"2026-03-02T08:58:11","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8725"},"modified":"2026-03-02T08:58:11","modified_gmt":"2026-03-02T08:58:11","slug":"taraba-ta-kaddamar-da-rarraba-kayan-aikin-a-kananan-hukumomi-16","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/taraba-ta-kaddamar-da-rarraba-kayan-aikin-a-kananan-hukumomi-16\/","title":{"rendered":"Taraba Ta Kaddamar da Rarraba Kayan Aikin A Kananan Hukumomi 16"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba \u0199ar\u0199ashin Shirin IMPACT, ta \u0199addamar da rarraba kayan aikin lafiya da babura ga jami\u2019an sa ido da tantance ayyuka (M&amp;E) a kananan hukumomi 16 na jihar.<\/p>\n<p>An gudanar da bikin \u0199addamarwar ne a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, a Jalingo, da nufin \u0199arfafa tsarin sa ido da inganta bayar da ayyukan kiwon lafiya a matakin \u0199asa.<\/p>\n<p>An samar da kayan ne ta hannun Ma\u2019aikatar Lafiya ta Jihar Taraba tare da tallafin World Bank Nigeria, \u0199ar\u0199ashin Shirin IMPACT.<\/p>\n<p>Baburan an ware su ne domin jami\u2019an sa ido da tantance ayyuka na kananan hukumomi, yayin da kayan aikin lafiyar kuma za su taimaka wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a matakin farko a yankunan karkara.<\/p>\n<p>Da yake \u0199addamar da shirin, Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Bordiya Buma, ya ce wannan tallafi zai \u0199ara tabbatar da gaskiya da ri\u0199on amana, da \u0199arfafa sa ido, tare da inganta sakamakon ayyukan kiwon lafiya, musamman a yankunan karkara da wuraren da ke da wahalar isa.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Manajan Shirin IMPACT a jihar, Dakta Ubanus Ezekiel, ya bayyana cewa tun bayan fara cikakken aiwatar da shirin a watan Janairun bara, an samu gagarumin ci gaba.<\/p>\n<p>Shi ma Babban Kwararren Lafiya kuma Jagoran Tawagar Shirin IMPACT na Bankin Duniya a ofishin Abuja, Dakta Onoriode Ezire, ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa bai wa kiwon lafiyar matakin farko muhimmanci, yana mai cewa \u0199arfafa kananan hukumomi na da matu\u0199ar tasiri wajen inganta ayyukan kiwon lafiya.<\/p>\n<p>Da yake magana a madadin shugabannin kananan hukumomi, Shugaban ALGON na Jihar Taraba, Mista Moses Maihankali, ya ce Shirin IMPACT ya inganta kayan aikin asibitoci a kananan hukumomi 16 na jihar.<\/p>\n<p>A wata hira da aka yi da ita, Mai Kula da Shirin IMPACT a matakin \u0199asa na Bankin Duniya a Najeriya, Dakta Amina Abdula-One, ta yi al\u0199awarin ci gaba da tallafa wa Gwamnatin Jihar Taraba domin cimma burinta na samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al\u2019umma a matakin \u0199asa.<\/p>\n<p>Rediyon Najeriya ya lura cewa wasu daga cikin shugabannin kananan hukumomi, ciki har da Shugaban Karamar Hukumar Jalingo, Mista Nuru Dantsoho, sun riga sun kar\u0253i kayayyakinsu domin rabawa.<\/p>\n<p>Haka kuma, a yayin bikin, \u0257aya daga cikin jami\u2019an sa ido da ya ci gajiyar shirin ya gwada \u0257aya daga cikin sabbin baburan da aka raba.<\/p>\n<h2>Sani Sulaiman<\/h2>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Kula da Ci gaban Kiwon Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Taraba \u0199ar\u0199ashin Shirin IMPACT, ta \u0199addamar da rarraba kayan aikin lafiya da babura ga jami\u2019an sa ido da tantance ayyuka (M&amp;E) a kananan hukumomi 16 na jihar. An gudanar da bikin \u0199addamarwar ne a ranar Alhamis, 26 ga Fabrairu, 2026, a Jalingo, da nufin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8726,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[325],"class_list":["post-8725","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-taraba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/03\/b27c7b87-df0f-4a55-ac79-f9360d224c59.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8725","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8725"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8725\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8727,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8725\/revisions\/8727"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8726"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8725"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8725"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8725"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}