{"id":8706,"date":"2026-02-28T21:28:21","date_gmt":"2026-02-28T21:28:21","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8706"},"modified":"2026-02-28T21:28:21","modified_gmt":"2026-02-28T21:28:21","slug":"gwamnatin-jigawa-ta-gargadi-yan-kwangila-kan-ingancin-abincin-ramadan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-ta-gargadi-yan-kwangila-kan-ingancin-abincin-ramadan\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa ta Gargadi \u2018Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara yin kira ga &#8216;yan kwangilar da aka baiwa sayen kayan abincin shan ruwa da su sanya tsoron Allah wajen sayen kayayyakin abinci masu inganci.<\/p>\n<p>Shugaban kwamitin ciyarwar\u00a0 na watan Ramadan kuma Kwamishinan ma&#8217;aikatar ilimi matakin farko na jihar Dr Lawan Yunusa Danzomo ya yi wannan kiran a lokacin da ya ziyarci wasu cibiyoyin dafa abincin a yankin karamar hukumar Birnin kudu.<\/p>\n<p>Ya bukace su da su sanya tsoron Allah wajen sayen kayayyakin abinci masu inganci da kuma tsafta kamar yadda aka cimma yarjejeniya da su da gwamnatin jihar.<\/p>\n<p>Ya nuna gamsuwar sa dangane da yadda ake dafawa da raba abincin buda baki a cibiyoyin da aka tanadar a garuruwan Birnin Kudu da Kantoga da Kafin gana da Kangire dake karamar hukumar Birnin Kudu.<\/p>\n<p>Dr Lawan Yunusa Danzomo wanda ya ziyarci cibiyoyin don ganewa idon sa yanda yawan abincin da tsaftarsa ya ke, ya nuna gamsuwarsa dangane da yadda wadanda aka baiwa alhakin aikin suke gudanar da rabon.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8708\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0017-200x300.jpg\" alt=\"\" width=\"200\" height=\"300\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0017-200x300.jpg 200w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0017-682x1024.jpg 682w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0017-768x1152.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0017.jpg 853w\" sizes=\"auto, (max-width: 200px) 100vw, 200px\" \/><\/p>\n<p>Yace Gwamnatin jihar Jigawa karkashin jagorancin Malam Umar Namadi ta bullo da shirin ciyarwar ne da nufin tallafawa dukkanin al&#8217;ummar jihar Jigawa musamman masu karamin karfi don su sami abin da za su yi buda baki da shi a lokacin shan ruwa.<\/p>\n<p>A don haka, Dan Zomo ya yi kira ga yan kwangilar da su tabbatar suna sayen kayan abincin a yankunan da za a dafa\u00a0 don a karfafi tattalin arzikin al&#8217;ummar yankunan.<\/p>\n<p>Yayi nuni da cewar, a kowacce cibiya ana dafa shinkafa da kunun tsamiya da kosai don rabawa mabukata har na tsawon watan Ramadan.<\/p>\n<p>Kazalika, ya yi kira ga al&#8217;umma da su ci gaba da yi wa Gwamnati addu&#8217;oi ra musamman a wannan watan na Ramadan domin samun nasarar gudanar da aiyukan alherin da kuma zaman lafiya mai dorewa a fadin jihar Jigawa.<\/p>\n<p>A jawaban su daban-daban, al&#8217;ummar garuruwan da kwamishinan ya ziyarta sun godewa gwamnatin jihar bisa bullo da shirin ciyarwar.<\/p>\n<p>Sun kuma yi addu&#8217;ar fatan alkhairi ga Gwamna Umar Namadi da gwamnatin sa da ma jihar jigawa baki daya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara yin kira ga &#8216;yan kwangilar da aka baiwa sayen kayan abincin shan ruwa da su sanya tsoron Allah wajen sayen kayayyakin abinci masu inganci. Shugaban kwamitin ciyarwar\u00a0 na watan Ramadan kuma Kwamishinan ma&#8217;aikatar ilimi matakin farko na jihar Dr Lawan Yunusa Danzomo ya yi wannan kiran [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8709,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[943,59,218],"class_list":["post-8706","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ciyarwa","tag-jigawa","tag-ramadan"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260228-WA0016.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8706","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8706"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8706\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8710,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8706\/revisions\/8710"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8709"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8706"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8706"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8706"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}