{"id":8674,"date":"2026-02-27T09:18:06","date_gmt":"2026-02-27T09:18:06","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8674"},"modified":"2026-02-27T09:18:06","modified_gmt":"2026-02-27T09:18:06","slug":"majalisar-dattawa-ta-bukaci-gwamnati-ta-tsara-hanya-mai-maana-wajen-tafiyar-kasafin-kudi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-dattawa-ta-bukaci-gwamnati-ta-tsara-hanya-mai-maana-wajen-tafiyar-kasafin-kudi\/","title":{"rendered":"Majalisar Dattawa Ta Bukaci Gwamnati Ta Tsara Hanya Mai Ma\u2019ana Wajen Tafiyar Kasafin Kudi"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar Dattawa ta bukaci tawagar tattalin arzikin gwamnati da ta tsara hanya mai ma\u2019ana domin komawa tsarin kasafin ku\u0257i da ya fi mayar da hankali kan fifikon aiki da sakamako, maimakon tsarin da ake amfani da shi a yanzu na \u201cenvelope system\u201d.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Sani Musa, ne ya yi wannan kira a jawabin sa yayin wata ganawa ta musayar ra\u2019ayi da tawagar tattalin arzikin gwamnati karkashin jagorancin Ministan Kudi, Mista Wale Edun.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sanata Sani Musa ya ce kasafin ku\u0257i tsari ne na hasashe, don haka idan ba a cimma burin kudaden shiga ba, ba zai yiwu aiwatar da shi ya tafi daidai da abin da ake tsammanin samu ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kara da cewa tsarin da ake bi a yanzu ba shi da inganci yadda ya kamata, domin ana sakin kashi 100 cikin 100 na kudaden overhead da na maimaituwa (recurrent), yayin da bangaren ayyukan ci gaba (capital projects) ke samun sifili.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce wannan ba abin yarda ba ne, kuma babbar matsala ce da ya kamata a duba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, \u201cMuna ganin jami\u2019an gwamnati na yin tafiye-tafiye cikin sauki, ana cika biyan kudaden overhead da recurrent, amma kudaden ayyukan ci gaban da aka ware domin \u2018yan Najeriya na nan a sifili. Wannan ba abin kar\u0253a ba ne ga kwamitin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Najeriya ba za ta iya ci gaba da yin kananan gyare-gyare ba yayin da ake bukatar garambawul na tsari baki daya.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai kwamitin ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta koma tsohon tsarin biyan \u2018yan kwangila, maimakon sabon tsarin da aka mayar da shi tsakiya (centralized system), wanda ya jefa gwamnati cikin basussuka ga \u2018yan kwangila da dama, har ma kan ayyukan da aka kammala a shekarar 2024, balle ma na 2025.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasu bangaren, mambobin kwamitin sun goyi bayan shugaban kwamitin tare da shawartar tawagar tattalin arzikin da ta inganta tsare-tsare da aiwatar da kasafin ku\u0257i, tare da gaggauta biyan \u2018yan kwangila.<\/p>\n<p>Haka kuma, a martanin da tawagar tattalin arzikin ta bayar, ta tabbatar wa kwamitin da \u2018yan Najeriya cewa hasashen shekarar 2026 yana da kyau matuka dangane da aiwatar da kasafin ku\u0257i na Naira tiriliyan 58.472 da aka gabatar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan Kudi, Wale Edun, ya bayyana wa kwamitin cewa bashin Naira tiriliyan 152 da kasar ke da shi a halin yanzu ba duka daga rance kai tsaye aka tara shi ba. Ya ce kimanin Naira tiriliyan 30 sun fito ne daga bashin Ways and Means da wannan gwamnati ta gada, yayin da Naira tiriliyan 9 suka taso sakamakon sauyin canjin kudi (exchange rate adjustment).<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce: \u201cA halin yanzu, bashin gwamnati a Naira ya kai tiriliyan 152. Kimanin tiriliyan 30 sun fito daga Ways and Means da muka gada, sannan tiriliyan 9 sun taso daga gyaran canjin kudi. Saboda haka kusan rabin bashin gyare-gyare ne kawai, ba sabon rance ba ne. Sabbin rance tun daga 2023 suna cikin zangon tiriliyan 20.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Tun da farko a farkon zaman ganawar da tawagar tattalin arzikin, kwamitin ya yanke shawarar rubuta wa Shugaba Bola Tinubu domin neman ya sauke Registrar-General na Hukumar Corporate Affairs Commission bisa zargin kin amsa gayyatar kwamitin akai-akai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>An cimma wadannan matsayai ne yayin zaman tattaunawar da tawagar tattalin arzikin Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Ministan Kudi kuma Ministan da ke kula da harkokin tattalin arziki, Mista Wale Edun, tare da Ministan Kasafi da Tsare-tsare na Kasa, Sanata Atiku Bagudu; Akanta Janar na Tarayya, Dakta Shamseldeen Babatunde Ogunjimi; da Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (NRC), Zacch Adedeji.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar Dattawa ta bukaci tawagar tattalin arzikin gwamnati da ta tsara hanya mai ma\u2019ana domin komawa tsarin kasafin ku\u0257i da ya fi mayar da hankali kan fifikon aiki da sakamako, maimakon tsarin da ake amfani da shi a yanzu na \u201cenvelope system\u201d. &nbsp; Shugaban Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa, Sanata Muhammad Sani Musa, ne ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8675,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[538],"class_list":["post-8674","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-majalisar-dattawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/2ce99577-f43d-4b21-8b1a-bcaacaba48c2.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8674","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8674"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8674\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8676,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8674\/revisions\/8676"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8675"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8674"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8674"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8674"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}