{"id":8671,"date":"2026-02-27T09:15:01","date_gmt":"2026-02-27T09:15:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8671"},"modified":"2026-02-27T09:15:01","modified_gmt":"2026-02-27T09:15:01","slug":"an-raba-takin-zamani-da-kayan-noma-ga-manoman-jihar-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-raba-takin-zamani-da-kayan-noma-ga-manoman-jihar-zamfara\/","title":{"rendered":"An Raba Takin Zamani Da Kayan Noma Ga Manoman Jihar Zamfara"},"content":{"rendered":"<h2>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya \u0199addamar da rabon takin zamani da sauran muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a kakar noman rani a fa\u0257in jihar.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>An \u0199addamar da shirin ne a ranar Alhamis a cibiyar Fadama III da ke \u0199ar\u0199ashin Ma\u2019aikatar Noma ta jihar a Gusau.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, kayayyakin da aka raba suna da matu\u0199ar muhimmanci wajen \u0199ara yawan amfanin gona, rage asarar da ake yi bayan girbi, da kuma bun\u0199asa noma mai \u0257orewa.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Kayayyakin da aka raba sun ha\u0257a da buhunan takin NPK 3,920, buhunan takin Urea 1,956, litar maganin kashe ciyawa 3,920, litar maganin kashe \u0199wari 1,956, da kuma fakitin maganin shafa iri 3,920.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>An tsara rabon ne domin kaiwa ga manoma a sassa daban-daban na jihar, musamman \u0199ananan manoma da ke dogaro da noma a matsayin hanyar samun abinci da ku\u0257in shiga.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>A jawabinsa, Gwamna Lawal ya jaddada cewa shirin na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke \u0257auka domin \u0199ara yawan noma, inganta tsaron abinci da kuma bun\u0199asa rayuwar al\u2019umma.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Ya ce noma shi ne ginshi\u0199in tattalin arzikin jihar, don haka wajibi ne gwamnati ta samar wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu su yi noma cikin inganci.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Ya bayyana cewa shirye-shiryen NG-CARES sun samar da tubalin da ya bai wa gwamnatin jihar damar cimma nasarori a bangaren noma, musamman ta hanyar tallafa wa dubban \u0199ananan manoma da iri masu inganci, magungunan gona da shawarwarin dabarun noma.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Gwamnan ya yi kira ga manoman Zamfara da su yi amfani da kayayyakin da aka ba su yadda ya kamata, domin cimma manufar bun\u0199asa noma mai \u0257orewa.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Ya \u0199ara da cewa, gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da irin wa\u0257annan shirye-shirye wajen \u0199ara samar da abinci a cikin gida da rage dogaro da shigo da kayayyakin abinci daga \u0199asashen waje.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Dangane da matsalolin tsaro, Gwamna Lawal ya amince cewa \u0199alubalen tsaro na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar noma a halin yanzu. Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da \u0199arfafa tsarin tsaro a yankunan karkara domin manoma su samu damar komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.<\/h2>\n<h2><\/h2>\n<h2>Haka kuma, ya yaba da goyon bayan da Gwamnatin Tarayya da abokan hul\u0257a na ci gaba ke bayarwa wajen aiwatar da shirin NG-CARES, yana mai cewa ha\u0257in gwiwa tsakanin bangarori ne ka\u0257ai zai tabbatar da nasarar manufofin ci gaban noma da tattalin arziki a jihar.<\/h2>\n<h2>Aminu Dalhatu\/Gusau<\/h2>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya \u0199addamar da rabon takin zamani da sauran muhimman kayan noma domin tallafa wa manoma a kakar noman rani a fa\u0257in jihar. An \u0199addamar da shirin ne a ranar Alhamis a cibiyar Fadama III da ke \u0199ar\u0199ashin Ma\u2019aikatar Noma ta jihar a Gusau. A cewar sanarwar da mai magana da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8672,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[942],"class_list":["post-8671","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-noman-rani"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/284b3445-2c44-4203-a8fa-901a41768c1f.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8671","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8671"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8671\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8673,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8671\/revisions\/8673"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8672"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8671"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8671"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8671"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}