{"id":8668,"date":"2026-02-27T09:13:20","date_gmt":"2026-02-27T09:13:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8668"},"modified":"2026-02-27T09:13:20","modified_gmt":"2026-02-27T09:13:20","slug":"kano-tana-karfafa-shirin-rigakafi-ga-yaran-da-ba-su-karbi-allura-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kano-tana-karfafa-shirin-rigakafi-ga-yaran-da-ba-su-karbi-allura-ba\/","title":{"rendered":"Kano Tana Karfafa Shirin Rigakafi Ga Yaran da Ba Su Karbi Allura Ba"},"content":{"rendered":"<p>A wani yunkuri na \u0199arfafa shirin rigakafin yau da kullum, Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano ta gudanar da wata ganawa ta musamman da manyan masu kula da cibiyoyin lafiya da Jami\u2019an Rigakafi na yau da kullum daga kananan hukumomi 15 da aka gano suna da yawan yaran da ba su taba kar\u0253ar ko wace allurar rigakafi ba.<\/p>\n<p>Taron wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Na\u2019ibawa, ya samu jagorancin Darakta Janar, Farfesa Salisu Ahmed, wanda ya sake jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da an kai wa kowane yaro da aka bari a baya rigakafi.<\/p>\n<p>Tattaunawar ta mayar da hankali ne kan sabon tsarin na rigakafin yau da kullum, wanda aka tsara domin ganowa, bibiyar su da kuma yi wa yaran da ba su taba kar\u0253ar allura ba ko kuma wadanda ba su kammala jadawalin rigakafinsu ba allurar da ta dace, musamman a al\u2019ummomin da matsalar ta fi kamari.<\/p>\n<p>Farfesa Ahmed ya bayyana cewa kawar da yankunan da ke da yawan yaran da ba a musu alluran ba na daga cikin manyan manufofin lafiyar al\u2019umma, inda ya bukaci shugabannin cibiyoyin lafiya su tabbatar da ingancin bayanai, tsauraran sa ido a filin aiki, da kuma \u0199arfafa wayar da kan al\u2019umma domin \u0199ara yawan masu kar\u0253ar rigakafi.<\/p>\n<p>Daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a taron shi ne fayyace rawar da kowane mamba na tawagar kananan hukumomi zai taka, domin tabbatar da hadin kai, \u0257aukar alhaki, da kuma sa ido kan yadda ake aiwatar da shirin yadda ya kamata.<\/p>\n<p>Darakta Janar ya kuma bukaci mahalarta taron su nuna jajircewa da kishin aiki, su \u0199arfafa tsarin kulawa da sa ido, tare da samar da sakamakon da zai nuna irin jagorancin da Jihar Kano ke da shi a fannin gyaran tsarin kula da lafiyar matakin farko.<\/p>\n<p>Shirin na samun tallafi daga gidauniyar Bill &amp; Melinda Gates ta hannun abokan hul\u0257a masu aiwatarwa, domin rage gibin rigakafi da kuma kare lafiyar kowane yaro a Jihar Kano.<\/p>\n<p>Hukumar ta kuma jaddada cewa ci gaba da irin wannan hadin gwiwa a matakin kananan hukumomi na da matukar muhimmanci wajen cimma burin kasa na rigakafi tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da za a bari a baya.<\/p>\n<h2>Khadijah Aliyu\/Kano<\/h2>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A wani yunkuri na \u0199arfafa shirin rigakafin yau da kullum, Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano ta gudanar da wata ganawa ta musamman da manyan masu kula da cibiyoyin lafiya da Jami\u2019an Rigakafi na yau da kullum daga kananan hukumomi 15 da aka gano suna da yawan yaran da ba su taba [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8669,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1967],"class_list":["post-8668","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-rigakafin"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/ea49d62b-2611-4ca0-b7eb-d4d57cc9bdbf.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8668","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8668"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8668\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8670,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8668\/revisions\/8670"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8669"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8668"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8668"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8668"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}