{"id":8651,"date":"2026-02-26T22:30:34","date_gmt":"2026-02-26T22:30:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8651"},"modified":"2026-02-26T22:30:34","modified_gmt":"2026-02-26T22:30:34","slug":"hukumar-alhazai-ta-jigawa-ta-hori-tawagar-manema-labarai-da-aiki-bisa-gaskiya-da-amana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-alhazai-ta-jigawa-ta-hori-tawagar-manema-labarai-da-aiki-bisa-gaskiya-da-amana\/","title":{"rendered":"Hukumar Alhazai ta Jigawa ta Hori Tawagar Manema Labarai da Aiki Bisa Gaskiya da Amana"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Jigawa ta bu\u0199aci tawagar kafafen ya\u0257a labarai ta shekarar 2026 da ta yi bisa gaskiya, ha\u0199uri da jajircewa wajen hidimtawa Alhazan jihar a \u0199asar Saudiyya<strong>.<\/strong><\/p>\n<p>Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan kiran yayin wani taron da tawagar kafafen ya\u0257a labarai gabanin gudanar da aikin Hajjin bana, wanda aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Dutse, babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa wannan aiki amana ce babba wadda ya kamata su jajirce domin sauke nauyin da aka dora musu.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa aikin ya ha\u0257a da ya\u0257a bayanai kafin tafiya Hajji, wayar da kai da ilmantarwa,\u00a0 \u0257aukar rahotanni, da kuma isar da sahihan bayanai cikin lokaci ga al\u2019ummar Jihar Jigawa da ma \u0199asa baki \u0257aya kan harkokin Hajji a Najeriya da kuma a Masarautar Saudiyya.<\/p>\n<p>A cewarsa, za a raba tawagar kafafen ya\u0257a labarai zuwa kwamitoci daban-daban domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin 2026.<\/p>\n<p>Ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa amincewa da kafa tawagar, tare da kira ga mambobin da su gudanar da aikinsu bisa \u0199wazo, rikon amana da kuma tsoron Allah.<\/p>\n<p>Da yake \u0199arin haske kan gyaran rabon guraben Hajjin 2026 ga jihohi kamar yadda Hukumar Alhazai ta \u0198asa (NAHCON)) ta umarta, Daraktan ya bayyana cewa Jihar Jigawa ta samu gagarumar nasara wajen shigar da bayanan dukkan maniyyata a shafin yanar gizo kafin wa\u2019adin \u0199arshe.<\/p>\n<p>Ya kuma ce hukumar ta kammala gwajin lafiya ga dukkan maniyyatan jihar a babban asibitin gwamnati da ke Dutse, daidai da \u0199a\u2019idojin hukumomin Saudiyya.<\/p>\n<p>Labbo ya \u0199ara da cewa gwajin lafiyar yana da ala\u0199a kai tsaye da sharu\u0257\u0257an bayar da biza ga maniyyatan shekarar 2026.<\/p>\n<p>A nasa jawabin na godiya a madadin mambobin tawagar, Babban Manajan gidan Talbijin na kasa reshen Jigawa(NTA), Malam Muhammad Ibrahim, tare da Malam Lawan Iliya Dutse na Talabijin na Jihar Jigawa, sun yaba wa gwamnatin jihar da hukumar bisa amincewa da guraben tawagar kafafen ya\u0257a labarai.<\/p>\n<p>Sun kuma yi al\u0199awarin cewa za su tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar gudanar da ayyukansu cikin \u0199warewa, sadaukarwa da kuma tsoron Allah.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Da\u0257in Alhazai ta Jihar Jigawa ta bu\u0199aci tawagar kafafen ya\u0257a labarai ta shekarar 2026 da ta yi bisa gaskiya, ha\u0199uri da jajircewa wajen hidimtawa Alhazan jihar a \u0199asar Saudiyya. Babban Daraktan hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya yi wannan kiran yayin wani taron da tawagar kafafen ya\u0257a labarai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8652,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1906,59],"class_list":["post-8651","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-2026hajj","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260226-WA0045.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8651","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8651"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8651\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8653,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8651\/revisions\/8653"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8652"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8651"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8651"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8651"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}