{"id":8643,"date":"2026-02-25T21:47:48","date_gmt":"2026-02-25T21:47:48","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8643"},"modified":"2026-02-25T21:47:48","modified_gmt":"2026-02-25T21:47:48","slug":"gwamnatin-kano-ta-yi-karin-girma-ga-maaikata-130","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kano-ta-yi-karin-girma-ga-maaikata-130\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kano Ta yi Karin Girma ga Ma\u2019aikata 130"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Kula da\u00a0 Ma\u2019aikatan Gwamnatin Jihar Kano ta amince da karin girma ga ma\u2019aikata 130 a fannoni daban-daban na aikin gwamnati a jihar.<\/p>\n<p>An amince da karin girman ne a yayin taron Hukumar na wata-wata, inda mambobi suka duba tare da tantance ma\u2019aikatan da suka cancanci karin matsayi, da nazarin wasu batutuwan gudanarwa da suka hada da bukatun canjin aiki da kuma shari\u2019o\u2019in ladabtarwa.<\/p>\n<p>Shugabar Hukumar, Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, ta ce karin girman na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulki ya dora wa hukumar, na tabbatar da bin ka\u2019idoji da dokokin aikin gwamnati.<\/p>\n<p>Ta kuma bukaci ma\u2019aikatan gwamnati da su ci gaba da jajircewa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, tana mai jaddada cewa gwamnatin jihar na goyon bayan ma\u2019aikata masu \u0199wazo da jajircewa, amma ba za ta lamunci sakaci ko rashin da\u2019a a wurin aiki ba.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma\u2019aikatan Gwamnati ta Kano, Alhaji Abdullahi Mahmud Umar, ya jaddada muhimmancin sadaukarwa da \u0199warewa a aiki, yana mai cewa hukumar na ci gaba da kyautata wa ma\u2019aikatan da suka cancanta tare da tabbatar da inganci a aikin gwamnati.<\/p>\n<p>Shi ma a nasa bangaren, babban sakataren hukumar, Alhaji Sani Shehu Minjibir, ya nuna gamsuwa da yadda taron ya gudana, yana mai tabbatar da cewa an yanke dukkan hukuncin ne bisa ga dokoki da \u0199a\u2019idojin aikin gwamnati da aka tanada.<\/p>\n<p>Karin girman na daga cikin \u0199o\u0199arin da gwamnatin jihar ke yi na \u0199arfafa gwiwar ma\u2019aikata da kuma inganta ayyukan\u00a0 a ma\u2019aikatu, da hukumomin gwamnati.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Khadijah Aliyu Hukumar Kula da\u00a0 Ma\u2019aikatan Gwamnatin Jihar Kano ta amince da karin girma ga ma\u2019aikata 130 a fannoni daban-daban na aikin gwamnati a jihar. An amince da karin girman ne a yayin taron Hukumar na wata-wata, inda mambobi suka duba tare da tantance ma\u2019aikatan da suka cancanci karin matsayi, da nazarin wasu batutuwan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1856,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[39,636,1094],"class_list":["post-8643","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kano","tag-karin-girma","tag-maaikata"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/Abba-Kabir-Yusuf-Kano-Governor.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8643","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8643"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8643\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8644,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8643\/revisions\/8644"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1856"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8643"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8643"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8643"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}