{"id":8612,"date":"2026-02-23T13:06:39","date_gmt":"2026-02-23T13:06:39","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8612"},"modified":"2026-02-23T13:06:39","modified_gmt":"2026-02-23T13:06:39","slug":"jamiyyar-apc-ta-zabi-sabbin-shugabanninta-a-jihar-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamiyyar-apc-ta-zabi-sabbin-shugabanninta-a-jihar-zamfara\/","title":{"rendered":"Jam\u2019iyyar APC ta Zabi Sabbin Shugabanninta a Jihar Zamfara"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Jam\u2019iyyar APC ta gudanar da tarukan za\u0253en shugabanni na mazabu da na \u0199ananan hukumomi cikin nasara a dukkan mazabu 147 da \u0199ananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, inda aka fitar da shugabannin jam\u2019iyyar ta hanyar sulhu.<\/p>\n<p>An gudanar da tarukan cikin kwanciyar hankali, kuma an bayyana su a matsayin masu tsari da nagarta, tare da halartar masu ruwa da tsaki da mambobin jam\u2019iyyar daga sassa daban-daban na jihar.<\/p>\n<p>Da yake zantawa da manema labarai a Gusau, shugaban kwamitin gudanar da tarukan, Babande Babakura Imam, ya ce an gudanar da aikin cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.<\/p>\n<p>Imam ya bayyana cewa tarukan na mazabu da \u0199ananan hukumomi sun samu halartar jama\u2019a da yawa, inda aka sami dukkan shugabanni\u00a0 ta hanyar\u00a0 sulhu da amincewar mambobin jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>Ya ce, \u201cJami\u2019an HukumarZabe mai Zaman Kanta ta kasa(INEC), da jami\u2019an tsaro, da wakilan jam\u2019iyyar APC daga sakatariyar \u0199asa da ke Abuja, da kuma wakilan APC na jiha ne suka sanya ido kan yadda aka gudanar da tarukan.\u201d<\/p>\n<p>A cewarsa, tarukan \u0199ananan hukumomi sun fitar da shugabannin APC a dukkan \u0199ananan hukumomi 14, ciki har da shugabanni, sakatarori da sauran jami\u2019ai.<\/p>\n<p>Shi ma da yake jawabi, shugaban APC na Jihar Zamfara, Alhaji Tukur Danfulani, ya bayyana nasarar gudanar da tarukan a matsayin abin farin ciki ga jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>Danfulani ya yabawa kwamitin tarukan bisa bin \u0199a\u2019idojin jam\u2019iyyar yadda ya kamata, wajen gudanar da aikin a duk fa\u0257in jihar, yana mai jaddada cewa APC na da \u0199udurin tabbatar da gaskiya da ha\u0257in kai.<\/p>\n<p>Shugaban jam\u2019iyyar ya kuma nuna kwarin gwiwa cewa APC na da ha\u0257in kai gabanin za\u0253uka masu zuwa a jihar, yana mai cewa fitowar sabbin shugabanni zai \u0199ara \u0199arfafa tsarin jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>\u201c<em>Wannan ci gaba alama ce cewa APC ta shirya tsaf domin \u0199wato jihar Zamfara tare da yin aiki domin sake za\u0253en Bola Ahmed Tinubu da dukkan \u2018yan takarar APC a za\u0253en shekarar 2027<\/em>,\u201d in ji Danfulani.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda mambobin jam\u2019iyyar suka halarci tarukan da kuma yadda aka gudanar da su cikin tsari da lumana a fa\u0257in jihar.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Aminu Dalhatu\u00a0 Jam\u2019iyyar APC ta gudanar da tarukan za\u0253en shugabanni na mazabu da na \u0199ananan hukumomi cikin nasara a dukkan mazabu 147 da \u0199ananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara, inda aka fitar da shugabannin jam\u2019iyyar ta hanyar sulhu. An gudanar da tarukan cikin kwanciyar hankali, kuma an bayyana su a matsayin masu tsari da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8613,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[1205,115],"class_list":["post-8612","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-apc","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260223-WA0013.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8612","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8612"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8612\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8614,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8612\/revisions\/8614"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8613"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8612"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8612"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8612"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}