{"id":8606,"date":"2026-02-23T09:04:19","date_gmt":"2026-02-23T09:04:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8606"},"modified":"2026-02-23T09:04:19","modified_gmt":"2026-02-23T09:04:19","slug":"wata-kungiya-ta-raba-kayan-abinci-ga-fursunoni-a-wamba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wata-kungiya-ta-raba-kayan-abinci-ga-fursunoni-a-wamba\/","title":{"rendered":"Wata Kungiya Ta Raba Kayan Abinci Ga Fursunoni A Wamba"},"content":{"rendered":"<p>Wata \u0199ungiyar agaji mai suna Islamic Society of Eggon-land (ISE) ta bai wa fursunoni da ke Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba kayan abinci na sahur da bu\u0257a-baki da darajarsu ta kai miliyoyin naira.<\/p>\n<p>Yayin da yake mi\u0199a kayan, Babban Sakataren \u0199ungiyar, Alhaji Umar Abdullahi Galle, ya bayyana cewa wannan tallafi wani \u0253angare ne na al\u2019adar da \u0199ungiyar ke yi a duk watan Ramadan domin tallafa wa \u0199o\u0199arin gwamnati tare da kyautata jin da\u0257in fursunoni da inganta lafiyarsu yayin da suke zaman hukunci.<\/p>\n<p>Ya ce manufar wannan tallafi ba wai rage \u0199imar abin da gwamnati ke yi ba ne, sai dai don \u0199ara musu farin ciki da jin da\u0257i. Ya jaddada cewa kayan abincin ba na Musulmi ka\u0257ai ba ne, an tanade su ne domin dukkanin fursunoni da ke zaman hukunci, kamar yadda kowa ke bu\u0199atar bu\u0257a-baki a wannan wata mai alfarma.<\/p>\n<p>Alhaji Umar Abdullahi Galle ya kuma ro\u0199i shugabannin cibiyar da su yi amfani da kayan yadda ya dace, domin ci gaba da kyakkyawar dangantaka da ake da ita. Ya tunatar da cewa sun ziyarci cibiyar a bara, inda suka samu kyakkyawan rahoto daga fursunoni kan yadda aka sarrafa tallafin da aka bayar a wancan lokaci, tare da kira ga shugabannin da su ci gaba da wannan kyakkyawan tsari.<\/p>\n<p>Da yake kar\u0253ar kayan, Shugaban Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba, John Ali-Bando, ya nuna godiya ga \u0199ungiyar Islamic Society of Eggon-land (ISE) bisa wannan karamci, tare da al\u0199awarin amfani da kayan yadda ya dace domin amfanin fursunonin.<\/p>\n<p>Ya kuma yi kira ga sauran \u0199ungiyoyin agaji da na addini da su yi koyi da irin wannan aiki domin taimaka wa masu bu\u0199ata da inganta yanayin cibiyoyin gyaran hali a \u0199asar.<\/p>\n<p>COV\/Aliyu Muraki\/Lafia.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata \u0199ungiyar agaji mai suna Islamic Society of Eggon-land (ISE) ta bai wa fursunoni da ke Cibiyar Gyaran Hali ta Wamba kayan abinci na sahur da bu\u0257a-baki da darajarsu ta kai miliyoyin naira. Yayin da yake mi\u0199a kayan, Babban Sakataren \u0199ungiyar, Alhaji Umar Abdullahi Galle, ya bayyana cewa wannan tallafi wani \u0253angare ne na al\u2019adar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8607,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1961],"class_list":["post-8606","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-wamba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/f070cb6b-0a1f-4c6e-97d9-bb2cd8dbe72b.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8606","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8606"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8606\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8608,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8606\/revisions\/8608"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8607"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8606"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8606"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8606"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}