{"id":8573,"date":"2026-02-19T09:38:39","date_gmt":"2026-02-19T09:38:39","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8573"},"modified":"2026-02-19T09:38:39","modified_gmt":"2026-02-19T09:38:39","slug":"ministan-tsaro-ya-yaba-da-jajircewar-gwamnan-zamfara-a-fannin-tsaro","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/ministan-tsaro-ya-yaba-da-jajircewar-gwamnan-zamfara-a-fannin-tsaro\/","title":{"rendered":"Ministan Tsaro Ya Yaba da Jajircewar Gwamnan Zamfara a Fannin Tsaro"},"content":{"rendered":"<p>Ministan Tsaro na \u0198asa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motoci masu sulke, jiragen sa-ido marasa matu\u0199a (drones) da sauran kayan aiki domin \u0199arfafa wa rundunonin tsaro a jihar.<\/p>\n<p>A wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau ranar Laraba, Gwamna Lawal ya mi\u0199a motoci 25 na zamani masu sulke (Armoured Personnel Carriers) ga jami\u2019an tsaro, domin \u0199ara musu kariya yayin da suke gudanar da aiki a yankunan da ke da ha\u0257arin tsaro a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa baya ga motocin sulken, gwamnatin Zamfara ta sayo jirgin sa ido mai \u0199arfin shawagi na tsawon mita 80, wanda zai iya rufe nisan kilomita 50 tare da yin aiki na tsawon sa\u2019o\u2019i takwas ba tare da tsayawa ba.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen \u0199addamar da kayayyakin, Gwamna Lawal ya ce halartar Ministan Tsaro ta \u0199ara nuna ha\u0257in kai da fahimtar juna tsakanin Gwamnatin Tarayya da ta Zamfara wajen tabbatar da tsaro da doka a jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa tsawon shekaru, Zamfara ta fuskanci matsalar tsaro da ta kawo cikas ga rayuwar al\u2019umma, noma, kasuwanci da zirga-zirga, lamarin da ya shafi tattalin arzikin jama\u2019a.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8575\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/a39ec204-7026-46aa-972d-a2f5f94c2f3d-300x169.jpeg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/a39ec204-7026-46aa-972d-a2f5f94c2f3d-300x169.jpeg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/a39ec204-7026-46aa-972d-a2f5f94c2f3d-768x432.jpeg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/a39ec204-7026-46aa-972d-a2f5f94c2f3d.jpeg 1000w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya ce a kar\u0199ashin shirin \u201cRescue Mission\u201d, gwamnatinsa ta koma daga martani na wucin-gadi zuwa tsarin gyara mai \u0257orewa, inda aka kafa Asusun Tsaro na Jihar Zamfara domin samar da ingantaccen tallafin kayan aiki ga hukumomin tsaro. Haka kuma, an samar da rundunar tsaron al&#8217;umma, wato \u2018Community Protection Guards\u2019 bisa tanadin doka domin inganta tattara bayanan sirri da sama da tsaro.<\/p>\n<p>Gwamnan ya \u0199ara da cewa, gwamnati ta raba motocin Hilux sabbi 150 ga jami\u2019an tsaro da suka ha\u0257a da \u2018yan sanda, DSS da NSCDC, tare da sayo motocin Toyota Buffalo guda 20 \u2013 10 masu sulke da 10 marasa sulke \u2013 da kuma babura sama da 600 domin saurin kai \u0257auki a wuraren da ababen hawa ba sa iya shiga cikin sau\u0199i.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa ha\u0257a sa ido ta sama da ta \u0199asa zai \u0199ara fa\u0257a\u0257a hangen nesa na jami\u2019an tsaro, inganta fahimtar yanayin wuri da kuma \u0199arfafa daidaito tsakanin cibiyoyin umarni da jami\u2019an da ke fagen daga.<\/p>\n<p>A nasa bangaren, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce matakin da gwamnatin Zamfara ta \u0257auka na sayo motocin sulke da sauran kayan aiki ya nuna \u0199wazon jagoranci da jajircewar gwamnan wajen kare rayuka da dukiyoyi.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, duk wani shugaba da ke zuba jari mai tsoka wajen tsaron jama\u2019arsa yana aikewa da sa\u0199o mai \u0199arfi ga masu aikata laifi.<\/p>\n<p>Ya \u0199qra da cewa, kare rayuka da dukiyoyi ya wuce siyasa, yana mai nuna farin cikinsa da yadda gwamnatin Zamfara ta biya dukkan ku\u0257a\u0257en kayan aikin gaba \u0257aya, lamarin da ke \u0199ara tabbatar da \u0199udurin gwamnati na ya\u0199i da rashin tsaro.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Tsaro na \u0198asa, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa sayo motoci masu sulke, jiragen sa-ido marasa matu\u0199a (drones) da sauran kayan aiki domin \u0199arfafa wa rundunonin tsaro a jihar. A wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau ranar Laraba, Gwamna Lawal ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8574,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[115],"class_list":["post-8573","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/ee19c4b5-e8d3-442b-be7d-a9310bece1b9.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8573","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8573"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8573\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8576,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8573\/revisions\/8576"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8574"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8573"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8573"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8573"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}