{"id":8567,"date":"2026-02-19T09:28:03","date_gmt":"2026-02-19T09:28:03","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8567"},"modified":"2026-02-19T09:28:03","modified_gmt":"2026-02-19T09:28:03","slug":"zamfara-na-neman-karin-hadin-gwiwa-domin-magance-matsalar-yara-marasa-zuwa-makaranta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zamfara-na-neman-karin-hadin-gwiwa-domin-magance-matsalar-yara-marasa-zuwa-makaranta\/","title":{"rendered":"Zamfara Na Neman Karin Hadin Gwiwa Domin Magance Matsalar Yara Marasa Zuwa Makaranta"},"content":{"rendered":"<p data-start=\"119\" data-end=\"133\">Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa da abokan hulda na ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.<\/p>\n<p data-start=\"325\" data-end=\"619\">Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da hadaddiyar tawaga daga shirin ciyarwa ga dalibai a Shirin Abinci na Malaisar dinkin Duniya da cibiyar nazarin harkokin abinci ta duniya.<\/p>\n<p data-start=\"621\" data-end=\"967\">A cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai a Ofishin SSG, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, SSG ya bayyana ilimi a matsayin babbar fifiko ga gwamnatin Gwamna <span class=\"whitespace-normal\"><b>Dauda Lawal<\/b><\/span>, yana mai cewa gwamnati ta dauki kwararan matakai domin gyara sakacin da aka yi wa bangaren ilimi tsawon shekaru.<\/p>\n<p data-start=\"969\" data-end=\"1150\">Nakwada ya bayyana cewa bayan ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi da gwamnatin yanzu ta yi, an gyara tare da samar da kayan koyarwa da na koyo a kusan makarantu 600 a fadin jihar.<\/p>\n<p data-start=\"1152\" data-end=\"1421\">Ya sake jaddada kudurin gwamnati na kara yawan shigar yara makaranta, da tabbatar da dorewarsu a makaranta har su kammala karatu, yana mai nuni da cewa shirin ciyar da dalibai a makaranta na daya daga cikin muhimman hanyoyin karfafa musu gwiwa su ci gaba da zama a aji.<\/p>\n<p data-start=\"1423\" data-end=\"1582\">Ya ce, \u201cYa kasance babban kalubale a rike yara a makaranta ba tare da samar musu da abinci ba. Wannan bangare ne da muke bukatar karin hadin gwiwa da tallafi.\u201d<\/p>\n<p data-start=\"1584\" data-end=\"1814\">Ya kara da cewa, \u201cMun kuduri aniyar tabbatar da cewa babu wani yaro da za a bari a baya a tsarin ilimi. Da matakan da muka dauka a yanzu, muna da yakinin cewa za a samu raguwar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Zamfara.\u201d<\/p>\n<p data-start=\"1816\" data-end=\"2139\">Bisa kididdigar da Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Zamfara (ZSUBEB) da UNICEF suka bayar, jihar ta samu kimanin yara 455,947 da ba sa zuwa makaranta a shekarar 2025, wanda ke nuna raguwar kaso 48.4 cikin dari idan aka kwatanta da adadin 883,953 da hukumar ilimi bai daya ta kasa \u00a0ta fitar a shekarar 2022.<\/p>\n<p data-start=\"2141\" data-end=\"2292\">Sanarwar ta bayyana cewa wannan ci gaba ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen da aka ci gaba da aiwatarwa a bangaren ilimi karkashin gwamnatin Lawal.<\/p>\n<p data-start=\"2294\" data-end=\"2699\">SSG ya tuna cewa a watan Yulin 2025, Gwamna Lawal ya kaddamar da shirin ciyar da dalibai a makaranta tare da hadin gwiwar Cibiyar Bun\u0199asa Tattalin Arziki ta Kasa da Kasa da kuma FINPACT Development Foundation, inda aka fara da dalibai kimanin 4,300 a makarantu na gwaji a fadin jihar. An tsara shirin ne domin kara yawan shigar yara makaranta, rage ficewarsu, da kuma rage yawan yaran da ke yawo a tituna.<\/p>\n<p data-start=\"2701\" data-end=\"3087\" data-is-last-node=\"\" data-is-only-node=\"\">A nata bangaren, Mataimakiyar Shugabar Shirye-shirye ta WFP a Nijeriya, Darline Raphael, ta yaba wa Gwamna Lawal bisa bai wa ilimi muhimmanci, musamman ilimin \u2018ya\u2019ya mata. Ta bayyana kwarin gwiwarta cewa da irin wannan jajircewa ta siyasa da gwamnatin jihar ta nuna, nan gaba kadan Zamfara za ta zama abin koyi a fannin aiwatar da shirye-shiryen ciyar da dalibai a makaranta a Nijeriya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi kira da a kara karfafa hadin gwiwa da abokan hulda na ci gaba da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Abubakar Mohammad Nakwada, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da hadaddiyar tawaga daga shirin ciyarwa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8568,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1958],"class_list":["post-8567","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-basic"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/eb78730e-d03a-4aed-ab76-b782a186aac6.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8567","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8567"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8567\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8569,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8567\/revisions\/8569"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8568"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8567"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8567"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8567"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}