{"id":8529,"date":"2026-02-16T09:59:39","date_gmt":"2026-02-16T09:59:39","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8529"},"modified":"2026-02-16T09:59:39","modified_gmt":"2026-02-16T09:59:39","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-fara-aikin-sake-gina-gadar-namnai-a-taraba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-fara-aikin-sake-gina-gadar-namnai-a-taraba\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Sake Gina Gadar Namnai A Taraba"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Raya Yankin Arewa maso ta fara aikin sake gina gadar Namnai da ta rushe a Jihar Taraba.<\/p>\n<p>Wannan babbar hanya mai yawan zirga-zirga, wadda ke ha\u0257a jihar da yankunan kudancin Nijeriya, na cikin \u0198aramar Hukumar Gassol a jihar.<\/p>\n<p>Abin tunawa ne cewa ambaliyar ruwa ta shekarar 2024 ce ta wanke gadar, lamarin da ya katse muhimmin hanyar sufuri tare da jefa masu amfani da hanya cikin wahala. Haka kuma, a sakamakon rushewar gadar a shekarun baya, an rasa rayuka da dama bayan aukuwar ha\u0257urran jiragen ruwa (\u0199ananan kwale-kwale).<\/p>\n<p>A halin da ake ciki, wata babbar tawaga daga NEDC, wadda ta ziyarci Jihar Taraba a \u0199arshen mako domin \u0199addamar da ayyukan da ta aiwatar a fa\u0257in jihar, ta kai ziyara wurin gadar domin duba yadda aikin ke tafiya.<\/p>\n<p>Tawagar ta samu jagorancin Ministan \u0198ananan Harkokin Raya Yankuna, wanda kuma \u0257an asalin jihar ne, Hon. Uba Maigari Ahmadu. A cikin tawagar akwai Shugaban Kwamitin Gudanarwa na NEDC, Manjo Janar Paul Tarfa; Darakta Janar\/ Shugaban Zartarwa na Hukumar, Mohammed Goni Alkali; \u2019yan Majalisar Dokoki ta \u0198asa; Daraktocin Zartarwa; mambobin Kwamitin Gudanarwa; da manyan jami\u2019an gudanarwa na hukumar.<\/p>\n<p>Da yake magana da \u2019yan jarida, Ministan ya ce ziyarar duba aikin na da nufin tantance ci gaba, ganin cewa tuni aka tura \u2019yan kwangila domin kammala aikin cikin gaggawa, don rage wa masu amfani da hanyar wahalhalu.<\/p>\n<p>Hon. Uba Maigari Ahmadu ya bayyana cewa sake gina gadar da sauran ayyuka masu yawa da NEDC ta aiwatar a fa\u0257in Jihar Taraba sun yi daidai da Manufar \u201cRenewed Hope\u201d ta Shugaban \u0198asa, Bola Ahmed Tinubu.<\/p>\n<p>Ministan ya nuna farin ciki da fara aikin gadar a \u0199arshe, tare da jaddada \u0199udurin Shugaba Tinubu na samar da romon dimokura\u0257iyya ga yankin da \u0199asar nan baki \u0257aya.<\/p>\n<p>A nasa \u0253angaren, Darakta Janar na NEDC, Mohammed Goni Alkali, ya bayyana tsoma-bakin a matsayin abin da ya zama dole domin rage wahalhalun da rushewar gadar ta haifar da kuma farfa\u0257o da harkokin tattalin arziki a yankin.<\/p>\n<p>Ya sake tabbatar da jajircewar hukumar wajen hanzarta aiwatar da ayyukan raya kasa a yankin Arewa maso Gabas.<\/p>\n<p>Wasu \u2019yan Nijeriya da ke yawan bin wannan hanya, a zantawarsu da wakilinmu, sun bayyana farin cikinsu da fara aikin ginin gadar, tare da yaba wa NEDC bisa cika aikinta.<\/p>\n<p>Sani Sulaiman<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya, ta hannun Hukumar Raya Yankin Arewa maso ta fara aikin sake gina gadar Namnai da ta rushe a Jihar Taraba. Wannan babbar hanya mai yawan zirga-zirga, wadda ke ha\u0257a jihar da yankunan kudancin Nijeriya, na cikin \u0198aramar Hukumar Gassol a jihar. Abin tunawa ne cewa ambaliyar ruwa ta shekarar 2024 ce ta wanke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8530,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1954],"class_list":["post-8529","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gadar-taraba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/93d2af8f-3a3e-4e5e-b6ec-0ae83ad1b9b9.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8529","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8529"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8529\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8531,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8529\/revisions\/8531"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8530"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8529"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8529"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8529"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}