{"id":8474,"date":"2026-02-14T11:18:40","date_gmt":"2026-02-14T11:18:40","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8474"},"modified":"2026-02-14T11:18:40","modified_gmt":"2026-02-14T11:18:40","slug":"gwamnatin-jigawa-ta-amince-da-shirin-ciyarwar-watan-ramadan-na-bana","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-ta-amince-da-shirin-ciyarwar-watan-ramadan-na-bana\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa ta Amince da Shirin Ciyarwar Watan Ramadan na Bana"},"content":{"rendered":"<p><strong>Daga Usman Muhammad Zari<\/strong><\/p>\n<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da gudanar da shirin ciyar da jama\u2019a na buda-baki (Iftar) na shekarar 2026, da nufin tallafa wa marasa galihu, tare da tabbatar da cewa al\u2019ummar jihar sun samu abinci mai gina jiki a lokacin watan Ramadan mai alfarma.<\/p>\n<p>Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Nura Ibrahim Kazaure, ne ya bayyana hakan jim ka\u0257an bayan taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a Government House Dutse.<\/p>\n<p>A cewarsa, shirin da aka amince da shi ya tanadi kafa cibiyoyin ciyarwa guda 640 a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Ya ce hakan ya ha\u0257a da kafa cibiyoyi biyu a kowace daga cikin mazabun siyasa 287 da ke cikin \u0199ananan hukumomi 27 na jihar, da kuma cibiyoyi na musamman a manyan makarantu, gidajen gyaran hali, da cibiyoyin jin \u0199ai domin tabbatar da cewa kowa ya amfana da shirin.<\/p>\n<p>Dr Kazaure ya nuna cewa ana sa ran shirin zai rika samar da abinci ga mutane sama da\u00a0 264,600 a kowace rana,<\/p>\n<p>A tsawon watan Ramadan, ana sa ran shirin zai samar da abinci sama da miliyan 23 da dubu 800 wanda za mutane sama da miliyan 7 da dubu 900 za su amfana.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-8477\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260214-WA0000-300x205.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"205\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260214-WA0000-300x205.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260214-WA0000-768x525.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260214-WA0000.jpg 1007w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Kazaure ya ce an tsara shirin ne domin samar da abinci mai gina jiki da inganci ga Musulmai masu azumi da sauran marasa galihu, tare da tallafa wa gidaje masu \u0199aramin \u0199arfi da kuma mutanen da ke fuskantar matsin tattalin arziki.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa shirin zai \u0199arfafa zumunci a tsakanin al\u2019umma, tausayi, da \u0257aukar nauyin juna, tare da \u0199ara tallafa wa shirye-shiryen\u00a0 zamantakewa da rage talauci da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.<\/p>\n<p>Sai dai Dr Kazaure ya bayyana cewa majalisar ta umarci a bi \u0199a\u2019idojin inganci sosai wajen sayo kayan abinci, girkawa da kuma rabawa.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya \u0199ara da cewa za a kafa kwamitocin sa ido a matakin jiha, \u0199ananan hukumomi da kuma unguwanni domin tabbatar da an aiwatar da shirin yadda ya kamata tare da rabon adalci.<\/p>\n<p>Ya bu\u0199aci shugabannin al\u2019umma, cibiyoyin addini, \u0199ungiyoyin matasa da \u0199ungiyoyin fararen hula su bayar da cikakken ha\u0257in kai domin tabbatar da nasarar shirin tare da kiyaye tsari a duk cibiyoyin ciyarwar.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa wannan shirin na jin \u0199ai da ha\u0257a kan jama\u2019a ya kuma shafi ma\u2019aikatan gwamnati na jihar, wa\u0257anda su ne ginshi\u0199in aiwatar da manufofin gwamnati a fannoni daban-daban.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zari Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da gudanar da shirin ciyar da jama\u2019a na buda-baki (Iftar) na shekarar 2026, da nufin tallafa wa marasa galihu, tare da tabbatar da cewa al\u2019ummar jihar sun samu abinci mai gina jiki a lokacin watan Ramadan mai alfarma. Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr Nura Ibrahim [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8478,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[943,59,218],"class_list":["post-8474","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ciyarwa","tag-jigawa","tag-ramadan"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/IMG-20260214-WA0001.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8474","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8474"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8474\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8479,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8474\/revisions\/8479"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8478"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8474"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8474"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8474"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}