{"id":8466,"date":"2026-02-13T08:38:50","date_gmt":"2026-02-13T08:38:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8466"},"modified":"2026-02-13T08:38:50","modified_gmt":"2026-02-13T08:38:50","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-raba-kayan-abinci-ga-dubban-iyalai-a-jihar-kebbi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-raba-kayan-abinci-ga-dubban-iyalai-a-jihar-kebbi\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kayan Abinci Ga Dubban Iyalai A Jihar Kebbi"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan abinci da na gina jiki ga dubban marasa galihu da kuma masu larurar nakasa a Jihar Kebbi.<\/p>\n<p>Ministan Kasa a Ma\u2019aikatar Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Alhaji Yusuf Tanko Sununu, wanda ya kaddamar da rabon a Birnin Kebbi, ya ce shirin ya nufin tallafa wa al\u2019ummomin da suka fi rauni wa\u0257anda bala\u2019o\u2019in jin-\u0199ai suka shafa a jihar.<\/p>\n<p>Yusuf Sununu ya bayyana cewa shirin ya ha\u0257a da rabon kayan gina jiki da magunguna ga asibitoci, cibiyoyin kula da yara, da sauran rukunonin da ke bukata. Ya \u0199ara da cewa za a kai irin wannan tallafi zuwa sauran mazabun sanatoci na jihar.<\/p>\n<p>Ya ce shirin ya yi daidai da ajandar \u00a0sabuwar fata ta Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu, wadda ke da nufin rage ra\u0257a\u0257in da bala\u2019o\u2019in jin-\u0199ai ke haifarwa a \u0199asar. Ya bayyana cewa kayan abincin sun ha\u0257a da buhun shinkafa, gero, wake, masara, man girki, da sauran kayan gina jiki.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan wannan tallafi, yana mai cewa shirin zai taimaka matu\u0199a wajen rage wahalhalun al\u2019ummar jihar. Ya kuma tabbatar da jajircewar gwamnatinsa wajen ha\u0257a kai da Gwamnatin Tarayya don rage talauci, yunwa da cututtuka.<\/p>\n<p>Gwamnan ya yi kira ga wa\u0257anda suka amfana da shirin da su yi amfani da tallafin yadda ya dace, tare da tabbatar musu da \u0199arin tallafi nan gaba. Haka kuma ya bu\u0199ace su da su nuna godiya ta hanyar sake za\u0253en Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wa\u2019adi na biyu.<\/p>\n<p>Rahoton Radio Nigeria ya nuna cewa wasu daga cikin wa\u0257anda suka amfana sun yaba da \u0199o\u0199arin gwamnatocin tarayya da jiha, inda suka tabbatar da cewa tallafin ya zo a kan lokaci kuma za su yi amfani da shi yadda ya kamata.<\/p>\n<p>An kaddamar da shirin ne ta hannun gwamnan jihar tare da taimakon \u0198aramin Ministan Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, a gaban manyan jami\u2019an gwamnatocin tarayya da jiha.<\/p>\n<p>COV: Sani Dutsinma<\/p>\n<p>Gwamnatin Tarayya Ta Horar da Masu Shigo da Kaya da Masu Ruwa da Tsaki kan Kasuwanci<\/p>\n<p>Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta \u0199arfafa \u0199a\u2019idojin \u0257a\u2019a a harkar shigo da kaya a matsayin wani muhimmin mataki na \u0199ara ku\u0257a\u0257en shiga da bun\u0199asa tattalin arzi\u0199in \u0199asa.<\/p>\n<p>Babban Sakataren Ma\u2019aikatar Ku\u0257i ta Tarayya, Mista Raymond Omenka, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron wayar da kai na kwana guda ga masu shigo da kaya, hukumomin da ke da alhaki da sauran masu ruwa da tsaki. Taron ya gudana a Kano, mai taken \u201c\u018aa\u2019a a Harkar Shigo da Kaya don Inganta Tara Ku\u0257a\u0257en Shiga.\u201d<\/p>\n<p>Sakataren Dindindin ya bayyana cewa \u0253angaren shigo da kaya muhimmin ginshi\u0199i ne a tattalin arzi\u0199in \u0199asa, inda ya ce yana taka rawar gani wajen samar da kayayyaki da ayyuka, \u0199ir\u0199irar guraben ayyukan yi, da sau\u0199a\u0199a hul\u0257ar kasuwanci da \u0199asashen waje.<\/p>\n<p>Da take wakiltarsa, Mataimakiyar Darakta a Sashen Hul\u0257ar Kasuwanci, Rukayyatu Abdullahi, ta ce damar da ke akwai na \u0199ara ku\u0257a\u0257en shiga ta hanyar bin \u0199a\u2019idojin \u0257a\u2019a a \u0253angaren shigo da kaya babba ce \u0199warai. Ta jaddada cewa aiki da gaskiya da ri\u0199on amana na samar da daidaito da adalci ga dukkan masu shigo da kaya.<\/p>\n<p>A nasa jawabin babban bako, Daraktan Sashen Kasuwanci da Musayar Ku\u0257a\u0257e na Babban Bankin Nijeriya (CBN), Dakta Musa Nakoji, wanda Jamilu Ado ya wakilta, ya ce taron zai bai wa masu ruwa da tsaki damar amfani da \u0199a\u2019idojin \u0257a\u2019a a harkar shigo da kaya a fannoni daban-daban na kasuwanci da rayuwar \u0257an Adam, wanda hakan zai \u0199ara ingancin tattalin arzi\u0199i.<\/p>\n<p>Daga cikin muhimman abubuwan da suka gudana a taron akwai gabatar da takardu daga Hukumar Kwastam ta Nijeriya, Hukumar Kula da Inganci ta Nijeriya (SON), Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta \u0198asa (NAFDAC), da \u0198ungiyar Masu Shigo da Kaya ta Nijeriya.<\/p>\n<p>Fiye da mahalarta 151 ne suka halarci taron.<\/p>\n<p>ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan abinci da na gina jiki ga dubban marasa galihu da kuma masu larurar nakasa a Jihar Kebbi. Ministan Kasa a Ma\u2019aikatar Harkokin Jin-\u0199ai da Rage Talauci, Alhaji Yusuf Tanko Sununu, wanda ya kaddamar da rabon a Birnin Kebbi, ya ce shirin ya nufin tallafa wa al\u2019ummomin da suka fi [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8468,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[139],"class_list":["post-8466","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kebbi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/5bbf1438-8dab-4cf9-94bb-029d0fe2b971.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8466","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8466"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8466\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8469,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8466\/revisions\/8469"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8468"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8466"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8466"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8466"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}