{"id":8459,"date":"2026-02-13T08:35:42","date_gmt":"2026-02-13T08:35:42","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8459"},"modified":"2026-02-13T08:35:42","modified_gmt":"2026-02-13T08:35:42","slug":"kwamitin-majalisar-dattawa-kan-ku%c9%97i-ya-dakatar-da-nazarin-kasafin-ku%c9%97in-2026","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/kwamitin-majalisar-dattawa-kan-ku%c9%97i-ya-dakatar-da-nazarin-kasafin-ku%c9%97in-2026\/","title":{"rendered":"Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Ku\u0257i Ya Dakatar da Nazarin Kasafin Ku\u0257in 2026"},"content":{"rendered":"<p>Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ku\u0257i ya dakatar da ci gaba da nazarin kasafin ku\u0257in shekarar 2026 na Ofishin Babban Akanta na Tarayya.<\/p>\n<p>A yayin zaman kare kasafin ku\u0257i da aka gudanar a wannan Alhamis, Kwamitin ya tsananta wa Babban Akanta na Tarayya, sakamakon matsalolin da ke hana ofishin gudanar da aikinsa yadda ya kamata.<\/p>\n<p>A jawabin bu\u0257e taro, Shugaban Kwamitin, Sanata Sani Musa, ya nuna bacin ransa tare da sukar Ofishin Babban Akanta kan \u0199arancin sakin ku\u0257a\u0257e ga Ma\u2019aikatun Gwamnati, Hukumomi da ke \u0199ar\u0199ashin doka, da kuma abin da suka kira tsarin biyan ku\u0257i na bai da ke takura \u2019yan kwangila.<\/p>\n<p>Ya nuna cewa halayyar ofishin ga kwamitin ba ta da kyau, kuma dole ne ta canza domin amfanin kowa da kowa.<\/p>\n<p>Ya ce:\u201cBa za mu kar\u0253i kasafinku ba har sai mun gamsu cewa ofishinku a shirye yake ya yi abubuwan da za su sa al\u2019amura su inganta ga \u2019yan Nijeriya, tare da cikakkun tabbaci daga gare ku.\u201d<\/p>\n<p>Da suke bayyana ra\u2019ayoyinsu a zaman, wasu sanatoci sun yi \u0199orafi mai zafi kan dalilin da ya sa Ofishin Babban Akanta ya gaza sakin ku\u0257a\u0257e ga \u2019yan kwangila.<\/p>\n<p>Sanata Muntari Dandutse ya bayyana mamakinsa kan yadda aka ruwaito cewa hukumomin tara ku\u0257a\u0257en shiga sun samar da naira tiriliyan 28, amma duk da haka kashi 85 na \u2019yan kwangila ana bin su bashin ku\u0257i, yayin da yawancin Ma\u2019aikatun Gwamnati ba su samu ko sisin kwabo ba a \u0253angaren kasafin ku\u0257in manyan ayyuka na shekarar 2025.<\/p>\n<p>Haka kuma, Sanata Abdul Ningi ya nuna damuwarsa cewa yawancin ayyukan kwangila da aka tsara aiwatarwa ba a aiwatar da su ba sakamakon \u0199arancin sakin ku\u0257a\u0257e, alhali ana kashe makudan ku\u0257a\u0257e a wasu fannoni daban.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa yawancin Ma\u2019aikatun da suka zo kare kasafinsu, babban \u0199orafinsu shi ne rashin sakin ku\u0257a\u0257e.<\/p>\n<p>Da yake mayar da martani, Babban Akanta na Tarayya, Shamsudeen Ogunjumi, ya ce yawan bayar da kwangila ba tare da tabbacin samuwar ku\u0257i ba da wasu Ma\u2019aikatu ke yi ne ya haddasa wannan matsala. A cewarsa, hakan ne ya sa aka bayar da umarnin hana Ma\u2019aikatu bayar da kwangila idan babu ku\u0257in da za a aiwatar da su.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa duk da \u0199alubalen da aka fuskanta a tsarin biyan ku\u0257i na bai \u0257aya, wa\u0257annan matsalolin ba a hango su ba tun da farko, amma ana aiki tukuru domin gyara su don samun sau\u0199in aiki.<\/p>\n<p>Ya ce:\u201cEh, a matsayina na Babban Akanta na Tarayya, ana sa ran ofishina ya rika sakin ku\u0257a\u0257e ga hukumomin da suka dace a kan lokaci. Amma hakan zai yiwu ne kawai idan ku\u0257in yana nan, domin dole ne in samu ku\u0257in kafin in iya raba shi.\u201d<\/p>\n<p>Ya kuma danganta matsalar da yadda tsarin Ways and Means da ake amfani da shi a baya wajen samun ku\u0257a\u0257en tallafi ya daina aiki, domin kare lafiyar tattalin arzi\u0199in \u0199asa.<\/p>\n<p>COV: Bashir Mayere<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ku\u0257i ya dakatar da ci gaba da nazarin kasafin ku\u0257in shekarar 2026 na Ofishin Babban Akanta na Tarayya. A yayin zaman kare kasafin ku\u0257i da aka gudanar a wannan Alhamis, Kwamitin ya tsananta wa Babban Akanta na Tarayya, sakamakon matsalolin da ke hana ofishin gudanar da aikinsa yadda ya kamata. A [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8461,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1943],"class_list":["post-8459","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-mayerre"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/0fcb1162-d4b0-4673-b6a2-1aab60bb1e13.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8459","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8459"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8459\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8462,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8459\/revisions\/8462"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8461"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8459"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8459"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8459"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}