{"id":8438,"date":"2026-02-12T08:24:50","date_gmt":"2026-02-12T08:24:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8438"},"modified":"2026-02-12T08:24:50","modified_gmt":"2026-02-12T08:24:50","slug":"cibiyar-ilimin-yaya-mata-ta-bu%c6%99aci-ci-gaba-da-goyon-bayan-ilimin-yan-mata","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/cibiyar-ilimin-yaya-mata-ta-bu%c6%99aci-ci-gaba-da-goyon-bayan-ilimin-yan-mata\/","title":{"rendered":"Cibiyar Ilimin \u2019Ya\u2019ya Mata Ta Bu\u0199aci Ci Gaba da Goyon Bayan Ilimin \u2019Yan Mata"},"content":{"rendered":"<p>Cibiyar Ilimin \u2019Ya\u2019ya Mata ta yi kira ga iyaye, shugabannin gargajiya da na addini da su ci gaba da bayar da goyon baya wajen inganta ilimin \u2019yan mata masu tasowa.<\/p>\n<p>Mai Kula da Ayyukan Cibiyar, Malama Alawiya Abdullahi, ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na kwana guda, da aka gudanar a dakin taro na cibiyar da ke Sabon Gari GRA a Zariya.<\/p>\n<p>Malama Alawiya Abdullahi ta bayyana cewa shirin ya mayar da hankali ne kan bai wa \u2019yan mata masu shekaru daga goma sha \u0257aya zuwa goma sha shida ilimin karatu da lissafi, musamman wa\u0257anda ba sa zuwa makaranta ko kuma suka daina zuwa.<\/p>\n<p>Ta \u0199ara da cewa taron shi ne karo na hu\u0257u da cibiyar ta shirya domin tantance ci gaban aikin, tattauna \u0199alubale da kuma \u0199arfafa mallakar shirin daga al\u2019umma.<\/p>\n<p>Saboda haka, mai kula da aikin ta yi kira ga sarakunan gargajiya da limamai da su \u0199ara wayar da kan al\u2019umma, tare da \u0199arfafa iyaye su bai wa \u2019ya\u2019yansu mata damar samun ingantaccen ilimi.<\/p>\n<p>Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yaba da shirin, suna bayyana yadda ya samar da alfanu mai yawa ga al\u2019ummominsu, musamman wajen fa\u0257a\u0257a damar ilimi ga \u2019ya\u2019yansu mata.<\/p>\n<p>Maharta taron sun yanke shawarar yin aiki tare domin bun\u0199asa ilimin \u2019yan mata da kuma tabbatar da \u0257orewar shirin a cikin al\u2019ummominsu.<\/p>\n<p>A yayin taron, mahalarta sun bayar da shawarwari tare da shiga tattaunawar rukuni-rukuni da jami\u2019an shirin suka jagoranta.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar mahalarta daga \u0199ananan hukumomin Giwa, Makarfi, Sabon Gari da Zariya.<\/p>\n<p>Ibrahim Suleiman\/Zaria<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Cibiyar Ilimin \u2019Ya\u2019ya Mata ta yi kira ga iyaye, shugabannin gargajiya da na addini da su ci gaba da bayar da goyon baya wajen inganta ilimin \u2019yan mata masu tasowa. Mai Kula da Ayyukan Cibiyar, Malama Alawiya Abdullahi, ta yi wannan kiran ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na kwana guda, da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8439,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[562],"class_list":["post-8438","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-zaria"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/82f06b98-0909-4ff9-ab15-a4bdf68a2848.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8438","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8438"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8438\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8440,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8438\/revisions\/8440"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8439"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8438"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8438"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8438"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}