{"id":8326,"date":"2026-02-02T09:24:11","date_gmt":"2026-02-02T09:24:11","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8326"},"modified":"2026-02-02T09:24:34","modified_gmt":"2026-02-02T09:24:34","slug":"jaridar-the-sun-ta-karrama-gwamnan-zamfara-da-lambar-yabo-ta-gwamnan-shekarar-2025","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jaridar-the-sun-ta-karrama-gwamnan-zamfara-da-lambar-yabo-ta-gwamnan-shekarar-2025\/","title":{"rendered":"Jaridar THE SUN Ta Karrama Gwamnan Zamfara Da Lambar Yabo Ta \u2018Gwamnan Shekarar 2025\u2019"},"content":{"rendered":"<p>Gwaman Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu wata babbar karramawa bayan da jaridar The Sun ta ba shi lambar yabo ta \u201cGwamnan Shekarar 2025\u201d, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin gagarumar nasara da gwamnatinsa ta samu a fannin shugabanci nagari.<\/p>\n<p>An mi\u0199a lambar yabon ne a wani gagarumin biki na Sun Awards da aka gudanar ranar Asabar, 31 ga Janairu, 2026, a \u0257akin taro na Expo da ke Eko Hotels and Suites a Legas.<\/p>\n<p>Bikin na shekarar-shekara na jaridar The Sun na karrama fitattun mutane ne da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban na rayuwa a Nijeriya.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa wannan karramawa wata shaida ce da ke nuna cewa manufofin Ayyukan Ceto Zamfara, wato \u201cRescue Mission\u201d na gwamnatin Dauda Lawal suna kan turbar da ta dace.<\/p>\n<p>Ya ce, tun bayan rantsar da gwamnan a ranar 29 ga Mayu, 2023, gwamnatin ta mayar da hankali wajen farfa\u0257o da Zamfara duk da \u0199alubalen tattalin arziki da ta gada.<\/p>\n<p>Sanarwar ta jaddada cewa bangaren tsaro ya kasance kan gaba a ajandar gwamnatin, inda aka kashe ma\u0199udan ku\u0257a\u0257e domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al\u2019umma. Haka kuma, an nuna cewa an samu ci gaba mai ma\u2019ana a fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, gina ababen more rayuwa, bun\u0199asa tattalin arziki da kula da jin da\u0257in ma\u2019aikata.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, gwamnatin Zamfara ta kuma yi fice a fannin kiwon lafiya a matakin farko, inda a watan Disambar bara aka ayyana jihar a matsayin wacce ta fi kowacce jiha a Arewa maso Yamma \u0199warewa a Gasar Jagorancin Kiwon Lafiya ta Matakin Farko.<\/p>\n<p>Masu lura da al\u2019amuran siyasa na ganin wannan lambar yabo a matsayin \u0199arin kwarin gwiwa ga gwamnatin Zamfara, tare da \u0199ara jaddada muhimmancin \u0257orewa kan manufofin da ke inganta rayuwar al\u2019umma. A nasu bangaren, magoya bayan gwamnan na kallon karramawar a matsayin tabbacin cewa \u0199o\u0199arin da Gwamna Lawal ke yi na samar da shugabanci nagari yana samun karbuwa har a matakin \u0199asa.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwaman Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya samu wata babbar karramawa bayan da jaridar The Sun ta ba shi lambar yabo ta \u201cGwamnan Shekarar 2025\u201d, sakamakon abin da aka bayyana a matsayin gagarumar nasara da gwamnatinsa ta samu a fannin shugabanci nagari. An mi\u0199a lambar yabon ne a wani gagarumin biki na Sun Awards da aka [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8328,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[363],"class_list":["post-8326","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-sun"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/02\/d4ebf808-3313-4fb5-b4ad-ae2a3453561f.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8326","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8326"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8326\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8327,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8326\/revisions\/8327"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8328"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8326"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8326"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8326"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}