{"id":8294,"date":"2026-01-31T20:27:44","date_gmt":"2026-01-31T20:27:44","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8294"},"modified":"2026-01-31T20:34:05","modified_gmt":"2026-01-31T20:34:05","slug":"jamiar-tarayya-dutse-za-ta-rantsar-da-sabon-shugabanta-ranar-10-ga-watan-fabrairu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamiar-tarayya-dutse-za-ta-rantsar-da-sabon-shugabanta-ranar-10-ga-watan-fabrairu\/","title":{"rendered":"Jami&#8217;ar Tarayya Dutse Za ta Rantsar da Sabon Shugabanta Ranar 10 ga Watan Fabrairu"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Jami\u2019ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta bayyana cewa za a rantsar da sabon Shugaban Jami\u2019ar (Vice-Chancellor) da aka na\u0257a, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, zai gudana a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 kamar yadda aka tsara.<\/p>\n<p>Lauyan mai kare wadanda ake kara, Barrista Shamsu Ubale Jibrin ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse,\u00a0 babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Hakan na zuwa ne\u00a0 bayan \u0199arar da Farfesa Abdulsalam Balarabe, \u0257aya daga cikin masu neman kujerar Shugaban Jami\u2019ar, ya shigar ta hannun lauyansa, inda yake \u0199alubalantar tsarin za\u0253en tare da ro\u0199on kotu da ta hana Majalisar Gudanarwa da sauran wa\u0257anda ake \u0199ara a shari\u2019ar gudanar da bikin rantsarwar da mi\u0199a mulki ga sabon Shugaban Jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Barrista Jibrin ya ce a gabatarwarsa, ya gabatar da hujjoji masu \u0199arfi tare da takardun shaidar gaskiya a gaban kotu, wa\u0257anda ke nuna cewa an kammala tsarin za\u0253en cikin tsari ba tare da karya daya daga cikin \u0199a\u2019idojin cancanta da aka ayyana a tallar da aka wallafa a jaridun \u0199asa ba.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa lauyan Farfesa Abdulsalam Salam ya kasa gabatar da wata hujja a gaban kotu da za ta nuna cewa ba a bi ka\u2019ida ba wajen na\u0257a sabon\u00a0 Shugaban Jami\u2019ar.<\/p>\n<p>Ya ce daga hujjojin da ya gabatar a gaban kotu, Farfesa Gumel ya cika dukkan sharuddan da ake bu\u0199ata don na\u0257a shi a matsayin Shugaban Jami\u2019a, inda ya samu maki mafi yawa, tare da zama na farko a tantancewar da aka yi wa &#8216;yan takarar, sannan Majalisar Gudanarwa cikin hikimarta ta na\u0257a shi a matsayin\u00a0 Shugaban Jami\u2019ar na hu\u0257u.<\/p>\n<p>Ya ce kotu ba ta amince da ro\u0199on dakatar da rantsarwar ba, sai dai cikin hikimarta ta \u0257age sauraron shari\u2019ar zuwa 23 ga Fabrairu bayan an kammala bikin rantsarwar.<\/p>\n<p>A cewarsa, wannan wata nasara ce ga\u00a0 Majalisar Gudanarwa da Farfesa Gumel.<\/p>\n<p>Barrista Jibrin ya bayyana cewa ya gabatar da hujjoji ingantattu don tabbatar da cewa Farfesa Gumel ya cika sharadin \u0199warewar aiki na shekaru 15 a jami\u2019a a zaman kotu da aka gudanar a ranar Alhamis.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Usman Muhammad Zaria Jami\u2019ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta bayyana cewa za a rantsar da sabon Shugaban Jami\u2019ar (Vice-Chancellor) da aka na\u0257a, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, zai gudana a ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 kamar yadda aka tsara. Lauyan mai kare wadanda ake kara, Barrista Shamsu Ubale Jibrin ne ya sanar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8295,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[986,59,526],"class_list":["post-8294","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-fud","tag-jigawa","tag-sabon-shugaba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/IMG-20260131-WA0032.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8294","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8294"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8294\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8298,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8294\/revisions\/8298"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8295"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8294"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8294"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8294"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}