{"id":824,"date":"2024-04-01T20:34:19","date_gmt":"2024-04-01T20:34:19","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=824"},"modified":"2024-04-01T20:34:19","modified_gmt":"2024-04-01T20:34:19","slug":"gwamnan-kebbi-ya-bi-sahun-takwarorinsa-na-bada-tallafi-ga-alhazai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnan-kebbi-ya-bi-sahun-takwarorinsa-na-bada-tallafi-ga-alhazai\/","title":{"rendered":"Gwamnan Kebbi Ya Bi Sahun Takwarorinsa Na Bada Tallafi Ga Alhazai"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da tallafin Naira miliyan daya ga kowane mahajjacin jihar su dubu uku da dari uku da arba&#8217;in da hudu domin sauke farali a aikin Hajjin shekarar 2024.<\/p>\n<p>Kwamishinan yada labarai da al\u2019adu na jihar, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, biyo bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a ranar Litinin.<\/p>\n<p>Ya ce, hakan ya biyo bayan karin kudin aikin Hajjin 2024 ne da Naira miliyan daya da dubu dari tara da Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta yi.<\/p>\n<p>A cewar sa, za a biya Naira miliyan daya ga kowane maniyyaci da ya kammala biyan kudin aikin Hajjin sa a baya.<\/p>\n<p>Dangane da batun fasa shaguna da sace-sacen hatsi da wasu baragurbi suka yi a babban birnin jihar, Kwamishinan ya ce, gwamnatin jihar ta yi Allahwadai game da hakan.<\/p>\n<p>Alhaji Yakubu BK ya ce gwamnatin jihar ta yi tir da irin wadannan munanan dabi\u2019u domin ba halayyar mutanen jihar ba ne.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, an kafa kwamiti mai mutum 13 a karkashin jagorancin kwamishinan aikin gona don binciki lamarin.<\/p>\n<p>Kwamitin, zai bankado musabbabin wannan\u00a0 aika-aikar, tare da tantance mutanen da ke da hannu tare da ba da shawarar hanyoyin hana sake aukuwar hakan.<\/p>\n<p>Shima da yake magana akan lamarin, kwamishinan noma da albarkatun kasa, Alhaji Shehu Muazu, ya shaidawa manema labarai cewa, kayan agajin da aka wawashe na gidauniyar Dangote ce ba na gwamnatin jihar ba.<\/p>\n<p>Abdullahi Tukur<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da tallafin Naira miliyan daya ga kowane mahajjacin jihar su dubu uku da dari uku da arba&#8217;in da hudu domin sauke farali a aikin Hajjin shekarar 2024. Kwamishinan yada labarai da al\u2019adu na jihar, Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":825,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[139,271],"class_list":["post-824","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kebbi","tag-tallafin-aikin-hajji"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/04\/24JQb54o_400x400.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/824","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=824"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/824\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":826,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/824\/revisions\/826"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/825"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=824"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=824"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=824"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}