{"id":8235,"date":"2026-01-26T19:33:37","date_gmt":"2026-01-26T19:33:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8235"},"modified":"2026-01-27T19:30:57","modified_gmt":"2026-01-27T19:30:57","slug":"bayan-sauya-she%c6%99a-gwamna-yusuf-ya-amince-da-kafa-majalisar-dattawan-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/bayan-sauya-she%c6%99a-gwamna-yusuf-ya-amince-da-kafa-majalisar-dattawan-kano\/","title":{"rendered":"Bayan Sauya She\u0199a: Gwamna Yusuf Ya Amince da Kafa Majalisar Dattawan Kano"},"content":{"rendered":"<p>Daga Abdullahi Jalaluddeen<\/p>\n<p>Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam\u2019iyyar NNPP zuwa\u00a0 APC,\u00a0 inda ya jagoranci gagarumar sauya she\u0199a a siyasar Jihar Kano.<\/p>\n<p>Sauya she\u0199ar ta ha\u0257a da mambobi 34 na Majalisar Dokokin Jihar, dukkan shugabannin \u0199ananan hukumomi 44, da kuma daukacin masu ri\u0199e da mu\u0199aman siyasa a gwamnatinsa.<\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani babban biki da aka gudanar a dakin taro na Coronation da ke Gidan Gwamnatn Kano.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a taron, Gwamna Yusuf ya ce matakin sauya she\u0199ar ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da kuma tantance halin da jihar ke ciki a yanzu da burin da take da shi a gaba.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa an \u0257auki matakin ne domin yin aiki tare da Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu, da nufin hanzarta ci gaban Kano tare da kawo ainihin amfanin dimokura\u0257iyya ga al\u2019ummar jihar.<\/p>\n<p>\u201c<em>Bayan shawarwari masu zurfi kan makomar Jihar Kano, ni tare da mambobi 34 na Majalisar Dokoki, dukkan \u0199ananan hukumomi 44 da kuma dukkan masu ri\u0199e da mu\u0199aman siyasa, mun yanke shawarar shiga jam\u2019iyyar APC domin yin aiki da shugabanci mai hangen nesa na Bola Ahmed Tinubu,\u201d in ji gwamnan.<\/em><\/p>\n<p>Gwamna Yusuf ya ce Ajandar sabunta kudurori ta <em>Renewed Hope<\/em> ta Shugaban \u0198asa ta fara haifar da sakamako mai kyau a fa\u0257in \u0199asar, yana mai jaddada cewa Kano ba za ta iya zama a gefe ba a lokacin da ha\u0257in gwiwa da Gwamnatin Tarayya zai bu\u0257e \u0199arin damammaki ga al\u2019ummarta.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa rikice-rikicen siyasa da fa\u0257a ba su taimaka wa kyakkyawan shugabanci, yana mai bayyana shugabanci a matsayin hidima ga jama\u2019a ba gasa ba.<\/p>\n<p>Gwamnan ya tabbatar wa magoya bayansa cewa wannan mataki bai rage \u0199o\u0199ari da gudummawar dukkan wa\u0257anda suka tsaya tare da shi a tafiyarsa ta siyasa ba.<\/p>\n<p>Ya kuma yi kira ga al\u2019ummar Kano da su duba sauya she\u0199ar cikin adalci, yana mai jaddada cewa an \u0257auki matakin ne da kyakkyawar niyya domin samar da \u0199arin dama, musamman ga matasan jihar.<\/p>\n<p>Haka kuma, Gwamna Yusuf ya sanar da amincewa da kafa Majalisar Dattawan Kano. Ya ce majalisar ba za ta kasance ta siyasa ba, kuma za ta zama cibiyar ba da shawara ga gwamnati domin inganta zaman lafiya, ha\u0257in kai da kyakkyawan shugabanci a jihar.<\/p>\n<p>A cewarsa, ha\u0257in kai da Gwamnatin Tarayya zai taimaka wajen samar da yanayin siyasa mai tsafta da ha\u0257in kai, tare da tabbatar da daidaito da kwanciyar hankali na dogon lokaci.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201c<em>Muna bu\u0257e sabon shafi bisa ginshi\u0199in ha\u0257in kai, kwanciyar hankali da shigar kowa. \u0198ofofinmu a bu\u0257e suke ga dukkan al\u2019ummar Kano<\/em>,\u201d in ji gwamnan, yayin da ya yaba wa shugabancin APC bisa goyon baya da halartar bikin sauya she\u0199ar.<\/p>\n<p>Manyan shugabannin APC da dama sun halarci taron, ciki har da tsohon Shugaban APC na \u0198asa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Karamin Ministan Gidaje da Bun\u0199asa Birane, Abdullahi Ata Fagge; Sanata Kawu Sumaila; Shugaban APC na Jihar Kano; da kuma dukkan shugabannin \u0199ananan hukumomi 44, tare da sauran jiga-jigan jam\u2019iyyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Abdullahi Jalaluddeen Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam\u2019iyyar NNPP zuwa\u00a0 APC,\u00a0 inda ya jagoranci gagarumar sauya she\u0199a a siyasar Jihar Kano. Sauya she\u0199ar ta ha\u0257a da mambobi 34 na Majalisar Dokokin Jihar, dukkan shugabannin \u0199ananan hukumomi 44, da kuma daukacin masu ri\u0199e da mu\u0199aman siyasa a gwamnatinsa. Gwamnan ya bayyana [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5723,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[39,538,1714],"class_list":["post-8235","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-kano","tag-majalisar-dattawa","tag-sauya-sheka"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Abba-Kabir-Yusuf.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8235","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8235"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8235\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8237,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8235\/revisions\/8237"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5723"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8235"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8235"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8235"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}