{"id":8220,"date":"2026-01-26T11:52:47","date_gmt":"2026-01-26T11:52:47","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8220"},"modified":"2026-01-26T11:52:47","modified_gmt":"2026-01-26T11:52:47","slug":"hukumar-shige-da-fice-ta-kasa-ta-ceto-mutane-22-da-aka-yi-yunkurin-safararsu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-shige-da-fice-ta-kasa-ta-ceto-mutane-22-da-aka-yi-yunkurin-safararsu\/","title":{"rendered":"Hukumar Shige da Fice ta Kasa ta Ceto Mutane 22 da Aka Yi Yunkurin Safararsu"},"content":{"rendered":"<p><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>Hukumar Shige da Fice ta kasa ta ceto mutane 22 da aka yi yunkurin safararsu,\u00a0 a yankin kan iyakar Zango da ke Jihar Katsina.<\/p>\n<p>Kwamandan Hukumar na Rundunar Iyakokin Jibia, Haruna Zakirai ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Daura.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa an gudanar da aikin ceton ne a sansanin sintirin jami\u2019an hukumar da ke Daura, bayan samun bayanan sirri daga wasu mazauna yankunan da ke kan iyaka, wa\u0257anda yi zargin wadansu\u00a0 mutane yayin da suke \u0199o\u0199arin tsallakawa da wa\u0257anda abin ya shafa zuwa \u0199etare.<\/p>\n<p>Zakirai ya ce jami\u2019ai da ma\u2019aikatan sansanin sintiri na Daura sun gaggauta \u0257aukar mataki, inda suka tare wa\u0257anda mutanen a wani kango a \u0199auyen Maibara da ke \u0198aramar Hukumar Zango ta jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa mutanen da aka ceto sun ha\u0257a da mata 11 da maza 11, masu shekaru tsakanin 17 zuwa 35, wa\u0257anda suka fito daga jihohi daban-daban na \u0199asar nan da suka ha\u0257a da Lagos, Osun, Rivers, Kwara, Katsina, Imo, Ondo, Benue, da Babban Birnin Tarayya Abuja.<\/p>\n<p>\u201c<em>Binciken farko ya nuna cewa ana safarar mutanen ne zuwa \u0199asar Libya, daga nan kuma zuwa Turai, inda aka yaudare su da alkawarin samun ingantacciyar rayuwa.<\/em><\/p>\n<p><em>\u201cWannan dabara ce da \u0199ungiyoyin safarar mutane ke yawan amfani da ita wajen ru\u0257ar mutanen da ba su sani ba. Muna kira ga al\u2019umma da su guji fadawa wannan tarko, domin a koda yaushe Hukumar Shige da Fice tana shirye wajen tarwatsa irin wa\u0257annan \u0199ungiyoyi da kuma ceto mutanen da ake yunkurin safarar su,<\/em>\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Zakirai ya \u0199ara da cewa akwai \u0257an \u0199asar Togo daga cikin mutanen da aka ceto, wanda za a mayar da shi \u0199asarsa bayan kammala bincike. Ya kuma ce a yanzu haka hukumar na neman shugaban \u0199ungiyar masu safarar wanda aka sani da suna \u201cCargo\u201d ruwa a jallo, wanda ya tsere lokacin da ake kokarin kama &#8216;yan \u0199ungiyar ta sa.<\/p>\n<p>Ya jaddada \u0199udirin Hukumar Shige da Fice ta kasa, na ya\u0199i da safarar mutane, \u0199aura ba bisa \u0199a\u2019ida ba, da laifukan ketare iyaka, tare da ro\u0199on al\u2019umma da su rika bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan duk wani da ake zargi da safarar mutane.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Daga Isma\u2019il Adamu\u00a0 Hukumar Shige da Fice ta kasa ta ceto mutane 22 da aka yi yunkurin safararsu,\u00a0 a yankin kan iyakar Zango da ke Jihar Katsina. Kwamandan Hukumar na Rundunar Iyakokin Jibia, Haruna Zakirai ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Daura. Ya bayyana cewa an gudanar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":8221,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1920,145,898],"class_list":["post-8220","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hukumar-shige-da-fice","tag-katsina","tag-safara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/IMG-20260126-WA0014.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8220","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8220"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8220\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8222,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8220\/revisions\/8222"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8221"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8220"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8220"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8220"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}