{"id":8213,"date":"2026-01-26T08:42:12","date_gmt":"2026-01-26T08:42:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8213"},"modified":"2026-01-26T08:42:12","modified_gmt":"2026-01-26T08:42:12","slug":"rundunar-yan-sanda-ta-kebbi-ta-kama-dan-damfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/rundunar-yan-sanda-ta-kebbi-ta-kama-dan-damfara\/","title":{"rendered":"Rundunar \u2018Yan Sanda ta Kebbi Ta Kama Dan Damfara"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Hamza Abdullahi Sama, mazaunin unguwar KCC a Birnin Kebbi, bisa zargin damfarar sama da mutum 175 da ke neman aikin yi, a \u0199ar\u0199ashin hujjar samar musu da ayyukan shirin ciyar da \u0257alibai a makarantu da gwamnatin jiha ta amince da su.<\/p>\n<p>Jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na rundunar, SP Bashir Usman, ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Birnin Kebbi, babban birnin jihar.<\/p>\n<p>SP Bashir ya ce binciken da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya yi karya ta hanyar bayyana kansa a matsayin wanda Gwamnatin Jihar Kebbi ta bashi damar shirya daukar ma\u2019aikata a makarantun firamare da sakandare.<\/p>\n<p>Ya ce bisa wannan \u0199aryar wakilci, wa\u0257anda abin ya shafa\u2014ciki har da Shafa\u2019atu, Yusuf Yahaya, Hussaini Sani, Ubaida Abubakar, da sauransu sun yarda suka biya Naira dubu talatin kowanne, a matsayin kudaden kafin alkalami na wasu abubuwa kafin basu aikin.<\/p>\n<p>SP Bashir ya \u0199ara da cewa \u0199arin bincike ya tabbatar da cewa wanda ake zargin ya damfari jimillar Naira miliyan 5 da dubu 200 daga hannun wa\u0257anda abin ya shafa, ta hanyar yaudara da gangan, domin babu irin wa\u0257annan guraben aiki, kuma ba a ba shi izini daga kowace hukuma ta gwamnati ba don \u0257aukar ma\u2019aikata ko sarrafa ayyuka a madadinta.<\/p>\n<p>A halin yanzu, wanda ake zargin na tsare a hannun \u2018yan sanda, kuma bincike na ci gaba da gudana da nufin gurfanar da shi gaban kotu bayan kammala bincike. Rundunar ta kuma ja hankalin al\u2019umma da su kasance masu fa\u0257ake da taka-tsantsan daga mutanen da ke cin moriyar halin \u0199unci na masu neman aiki ta hanyar shirya aikin yi na bogi.<\/p>\n<p>SANI DUTSINMA<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2018Yan Sanda ta Jihar Kebbi ta kama wani mutum mai suna Hamza Abdullahi Sama, mazaunin unguwar KCC a Birnin Kebbi, bisa zargin damfarar sama da mutum 175 da ke neman aikin yi, a \u0199ar\u0199ashin hujjar samar musu da ayyukan shirin ciyar da \u0257alibai a makarantu da gwamnatin jiha ta amince da su. Jami\u2019in hul\u0257a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8214,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,8],"tags":[1054],"class_list":["post-8213","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tsaro","tag-damfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/48092ff4-f63a-4cd5-80fe-32e9f3647daf.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8213","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8213"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8213\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8215,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8213\/revisions\/8215"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8214"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8213"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8213"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8213"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}