{"id":8207,"date":"2026-01-26T08:39:12","date_gmt":"2026-01-26T08:39:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=8207"},"modified":"2026-01-26T08:39:12","modified_gmt":"2026-01-26T08:39:12","slug":"zargin-juyin-mulki-wata-%c6%99ungiya-ta-bukaci-sakin-jamian-soja-da-aka-tsare-saboda-matsalolin-lafiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zargin-juyin-mulki-wata-%c6%99ungiya-ta-bukaci-sakin-jamian-soja-da-aka-tsare-saboda-matsalolin-lafiya\/","title":{"rendered":"Zargin Juyin Mulki: Wata \u0198ungiya Ta Bukaci Sakin Jami\u2019an Soja da Aka Tsare Saboda Matsalolin Lafiya"},"content":{"rendered":"<p>Wata \u0199ungiya mai taken Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki jami\u2019an sojan da ke tsare bisa zargin hannu a wani yunkurin juyin mulki a Oktoban shekarar da ta gabata, har zuwa kammala binciken da ake yi kan lamarin.<\/p>\n<p>Shugaban \u0199ungiyar, Comrade Yusuf Musa Dauda, ne ya bayyana wannan kira yayin taron manema labarai da aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa.<\/p>\n<p>Ya bayyana damuwa kan yadda wasu daga cikin jami\u2019an da aka kama tun watan Oktoba ke tsananin rashin lafiya a yayin tsare su, ba tare da samun ingantaccen kulawar lafiya ba.<\/p>\n<p>Comrade Yusuf Musa Dauda ya kuma nuna rashin jin da\u0257insa kan hana iyalan jami\u2019an damar ganinsu ko tattaunawa da su tun bayan kamunsu, ko a\u0199alla su san halin da suke ciki domin rage musu fargaba.<\/p>\n<p>\u0198ungiyar ta kuma yi Allah-wadai da tsawaita tsare jami\u2019an sojan ba tare da gurfanar da su gaban kotu ko bin ka\u2019idojin doka ba, a wani lokaci da ake ikirarin mulkin dimokira\u0257iyya, inda ta ro\u0199i Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani domin duba lamarin tare da sakin su idan babu tuhuma tabbatacciya a kansu.<\/p>\n<p>A cewarsa:<\/p>\n<p>\u201cHedikwatar Tsaron \u0198asa ta Najeriya, ta hannun tsohon Daraktan Ya\u0257a Labarai na Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, a ranar 4 ga Oktoba, 2025, ta sanar da kama wasu jami\u2019an soja bisa zargin rashin da\u2019a da karya \u0199a\u2019idojin aiki.<\/p>\n<p>\u201cSojoji sun ce bincike ya nuna cewa korafe-korafen jami\u2019an da aka kama na da ala\u0199a da yawan faduwa jarabawar \u0199arin matsayi da kuma jin cewa aikinsu ya tsaya cak.<\/p>\n<p>\u201cBayan wasu makwanni, jita-jita ta bazu cewa an kama su ne bisa zargin shirin juyin mulki, amma sojoji da gwamnati sun gaggauta musanta hakan.<\/p>\n<p>\u201cDuk da cewa muna yin Allah-wadai da duk wani yun\u0199urin kifar da gwamnati ta hanyar da ba ta dimokira\u0257iyya ba, muna kira ga jama\u2019a da kuma ro\u0199on hukumomin da abin ya shafa da su yi adalci wajen duba wannan batu.<\/p>\n<p>\u201cSaboda haka, muna ro\u0199on Gwamnatin Tarayya, Shugaban \u0198asarmu mai jin tausayin al\u2019ummarsa, da sauran hukumomin da abin ya shafa da su ba jami\u2019an kulawar lafiya da ta dace.\u201d<\/p>\n<p>Ya kuma \u0199ara da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da izinin jami\u2019an da ke tsare su rika tuntu\u0253ar iyalansu, domin rage musu damuwa da tabbatar da lafiyarsu da tsaronsu.<\/p>\n<p>COV \/ Aliyu Muraki \/ Lafia<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata \u0199ungiya mai taken Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta saki jami\u2019an sojan da ke tsare bisa zargin hannu a wani yunkurin juyin mulki a Oktoban shekarar da ta gabata, har zuwa kammala binciken da ake yi kan lamarin. Shugaban \u0199ungiyar, Comrade Yusuf Musa Dauda, ne ya bayyana [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":8208,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1918],"class_list":["post-8207","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-juyi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/01\/6fc51d9c-2eeb-40e6-98c7-dfb987963cc4.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8207","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=8207"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8207\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":8209,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/8207\/revisions\/8209"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/8208"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=8207"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=8207"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=8207"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}